*DUBU JIKAR MAI CARBI*
LABARI DA RUBUTAWA
AMEERA ADAM
3
Ƙananan yaran da aka bari a ƙofar ɗakuna ban da kiran sunayen iyayensu babu abin da suke yi, ƴan madaidaitan cikinsu waɗanda suka fara sanin ciwon kansu ne suka samawa kansu mafita suka nemi maɓoya. Sauran marasa wayo sai ihu suke suna buga ƙofar ɗakin da iyayensu suka shiga. Yaya Idi saboda firgita bai san lokacin da ya wuce can ƙarshen gadon Inna Furai ba, mutumin da ko falon Inna Furai baya iya ƙwaƙwaron tsayuwa, a cewarsa yana Yayan miji haka sam bai kamace shi ba. Rabon shi da shiga ɗakin Inna Furai tun wata doguwar rashin lafiya da ta yi sama da shekara goma, lokacin da ya je dubata amma a wannan ranar shi ne har tsakiyar gadonta. Ban da ɗigar da gumi babu abin da gemunsa yake yi saboda tashin hankali. Lantan can ƙarƙashin gado ta shige ban da ƴan idanuwanta babu abin da kake iya hangowa, ta ƙwale kai a jikin ƙarfe gado ya fi sau biyar duk don ganin ta ɓoye kanta ba tare da an hangota ba bare tawagar fatale su kawo mata farmaki.
Inna Furai zaman ƴan bori ta yi zanin jikinta ya jiƙe sharkaf da fitsari don gani take wannan zuwan da Fatalwar nan ta yi zuwanta ne, don a ganinta saɓawa umarnin fatalwar da tayi na sake shayar da ƴaƴanta ne ya sa, fatalwar nan ta yi dirar mikiya domin ƴan sama jannati su tafi da ita. Badariya tuni ta ƙwaƙume Yaya Idi da ke gefenta, duk yanda Badariyya ta kai ga jin ƙyanƙyamin gemun namiji sai ga gumin gemun Yaya Idi na ɗiga a sai tin fuskarta. Gabaɗaya mutanen cikin ɗakin ba ƙaramin tsorata suka yi ba. Ita ma Dubu tuni ta bi yarima don kar wani ya yi saurin gano shirinta saboda ko kaɗan bata son ta samu matsala, ta tabbata muddin ta ci gaba da razana su babu wanda zai ƙara koda nan da kwana biyu ne.
Bayan wasu ƴan mintuna Yaya Idi ya ɗago sai a lokacin ya lura da wacce take gefensa a maƙale da shi suna haɗa ido ya watsa mata harara, da sauri ya matsa gefe yana cewa, "Subhanallah! Astagafirullahi wa'atubu'ialhi ke matsa gefe matsa-matsa" A razane ita ma ta ja baya tana yamutsa fuska alamar ƙyanƙyami, don ita kanta bata san lokacin da ta ƙwaƙume Yaya Idi ba don ta san kowane ne shi. Ya kalli Dubu da ke can bakin ƙofa da yake ita ce ƙarshen shiga sannan ya ce, "Ke Dubu wai da gaske kike kin ga Fatalwar Mamman?" Dubu ta yi wani fakare sai kawai ji suka yi ta rushe da wani irin kuka har tana wani furjin yawu kamar wata ƙaramar yarinya." Yaya Idi ya yi zuru yana kallonta a zuciyarsa yana fatan kada Allah ya sa ta tabbatar da abin da ta faɗa da farko. A ƙagauce Yaya Idi ya sake cewa kamar zai yi kuka, "Ke Dubu wannan kukan ba ke kaɗai za ki yi shi ba ki sanar da mu musan halin da mu kanmu muke ciki."
Dubu ta tsagaita da kukan sannan ta fara cewa, "Na ga fatalawar Baffa ido da ido don har cewa suka yi za su fara ɗaukan Innarmu da Innar su Sabi'u. Kuma wai sun ci alwashin duk wanda ya haure shekara Arba'in a gidan nan sai sun naɗe masa ƙafafuwa kamar alkaki."
Tashin hankali wanda ba a samasa rana. Inna Furai na jin ance za a tafi da ita da Yaya Babba hantar cikinta ta sake kaɗawa gumi ta ko'ina sai keto mata yake yi. Don har kusan suman zaune ta yi saboda waɗansu irin taurari ta rinƙa gani suna yi mata gizo a tsakar idonta. Tun daga abin da Dubu ta faɗa babu wani abu da Inna Furai ta sake fahimta a ƙwaƙwalwarta, don sama-sama ta rinƙa jin wani yuuuuuu a zatonta wannan abin da ta fara ji ƴan sama jannatin ne suka fara kawo mata farmaki. Cikin fitar hayyaci Inna Furai ta fara cewa, "Ikon Allah Ikon gaske! Kai Auwalu kana ina ne? Ke Larai don Allah a cikinku wani ya ɗauke ni ko a kafaɗe ya fice da ni tun fatalwa bata tafi da ni. Auwaluna! Auwaluna na ci burin ganin Ɗanka amma da ƙyar idan zan samu wannan damar ka kawo mini Yahanasu idan ya so mu tafi da ita ko da Fatlwar sun tafi da mu na yi mata raino a cen barzahun idan ta haihu." Dubu juyawa ta yi ta rinƙa ɓaɓɓaka dariya ƙasa-ƙasa saboda ta lura tuni Inna Furai ta riga da ta fita hayyacinta, don fitsari ma ta yi ya kai sau uku daga shigarsu ɗakin.
YOU ARE READING
DUBU JIKAR MAI CARBI
FantasyDa sauri Yaya babba ta matsa baya tana zaro ido ta ce, "Dubu me nake gani kamar aski akanki." Dubu ta rushe da kuka ta ce, "Inno wallahi aski ya mini kuma wallahi ɗan iska ne." Cak Yaya Babba ta tana ƙarewa Dubu kallo sannan ta ce, "Dubu je ki can m...