9

431 17 0
                                    

*DUBU JIKAR MAI CARBI*

            ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

FREE PAGE 9
    https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels

Ku dannan👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼 subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.

     Sallamar Baba Munkaila ne ya dawo da Dubu cikin hayyacinta, ba shiri ta shiga nutsuwarta ta fara kumbure-kumbure don ta san babu makawa zai samu labarin abin da ya faru tsakaninta da Hansatu. A daidai kan Dubu ya tsaya fuska babu walwala ya ce, "Ke!" Kamar bata ji shi ba ta yi biris, sai da ya sake buga mata tsawa sannan ta amsa. Cikin faɗa ya ci gaba da cewa, "Dubu ki kiyaye ni fa, kullin iskancinki da iya shegenki ƙara gaba yake ko? Ƴar ƙanƙanuwarki da ke har kin isa tarar matar aure ki ce za ki yi dambe da ita. Wallahi a hir ɗinki idan kika shiga hannuna na lahira sai ya fiki jin daɗi." Dubu dama kamar me jira yana dire zancensa ta fashe da kuka tana faɗin, "Dama na san komai ni za a ɗorawa alhalin ita ce bata da gaskiya." Rankwashi ya sakar mata a tsakiyar ka aikuwa ba ƙaramin shigarta ya yi ba, a zabure ta yi gefe ai kuwa Yaya babba dama ta fara cika ta dubi Baba Munkaila cikin faɗa ta ce, "Munkaila nakasa marainiyar Allah za ka yi? Ka duba irin ƙusar da ka sakar mata a tsakiyar ka sai ka huda mata kai, ka cuceni ka cuci Ado. Ko da ya kasance likita ba sai an sayi magunguna da alluran da za a yi mata aiki ba. Gaskiya bana so ka fita rayuwar yarinyar nan shi ya sa ga tana kamar ruwan aski kullin bata kumari." Baba Munkaila bai tankawa Yaya Babba ya dubi Dubu ya ce, "Tashi ki ɗau hijabinki ki wuce makaranta. " Tun bai rufe baki ba Dubu ta suri kayanta ta fita waje tana kurma uban ihu.

Inna Furai ta ja tsaki ta dubi Baba Munkaila ta ce, "Munkaila wai me ya sa ko yaushe burinka ka zazzagewa yarinyar nan albarkar da ke kanta? Yanzu da ka kaɗa ta waje idan ta shiga gari wa ya shiga uku idan ba mu ba." Yaya babba ta cafe zancen da cewa, "Wallahi idan na rasa Dubu hukuma ce za ta raba ni da Munkaila dama na daɗe ina zargin ba ƙaunarta kake ba." Baba Munkaila ya yi murmushi sannan ya ce, "Inno yanzu so kuke a zurawa Dubu ido ta taso babu nutsuwa da rashin ilimi? Kuna ganin Fatima yarinyar nan kowa sha'awarta yake, saboda ilimin addininta. Mu kuwa wa yake sha'awar Dubu? Ku shaida ne a rana sai a kawo muku ƙara ta yi sau goma. Amma Inna furai ai bai kamata mu zura mata ido haka har girmanta ba."

Yaya babba ta yi shiru tana nazari sannan ta ce, "Munkaila ka yi tunani, kuma wallahi ina jin hannu aka sawa Dubu dole na sake nema mata maganin baki don wallahi baki ba ɗan'uwa ba ne." Baba Munkaila na ganin ya yi wa Tsofaffin iyayen nasa dabara ya tashi ya fice daga gidan.

Dubu na fita ta goge hawayenta ta maƙale jakarta ta ɗauki hanyar islamiyya, sai dai tana saƙa da warwarar abin da za ta yi wa Hansatu don ta fanshewa abin da ta yi mata. Kamar daga sama tana shan kwanar hanyar da za ta sadata da makarantarsu sai ga Ɗan'iya ya fito da tallar wake da shinkafa a kansa, hannunsa na riƙe da bokitin ragadada. Yana ganinta ya yi baya da sauri a tsorace don ya san mai ƙwatarsa a hannun Dubu sai Allah, don haka bai yi wata-wata ba tun Dubu bata tanka masa ba ya fara cewa, "Dubu don Allah ki yi haƙuri wallahi ba zan ƙara ba." Kamar wani abu bai haɗasu ba, haka Dubu ta basar da Ɗan'iya ta ce, "Da aka yi me?"

Ɗan'iya ya washe baki ya ce, "Faɗanki da Innarmu mana." Dubu ta zurawa bokitin ragadadar hannunsa ido, take ta ji yawunta ya tsinke, ta kai hannu za ta taɓa ya janye da sauri. Dubu ta riƙe ƙugu tana jinjina kai sannan ta ce, "Ɗan'iya wallahi ko ka bani bokitin nan ko kuma in haɗa gabaɗaya da Shinkafa da waken da shi bokitin ragadadar in kifar da su don wallahi wannan rigimar mun fara ta kenan ni da ku."

DUBU JIKAR MAI CARBIWhere stories live. Discover now