*DUBU JIKAR MAI CARBI*
LABARI DA RUBUTAWA
AMEERA ADAM
FIRST CLASS WRITERS'S ASSO...
Labarin mallakin Duniyar Hausa Novels ne, za a ci gaba da sauraren ci gaban shi bayan sakin wasu shafikan.
https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels
Ku dannan👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼 subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.
6
Duk wannan abin da ya faru sam Dubu bata lura ba, masifa na cin ta bata san da ta sheƙa wa Aseem garin masara a jiki ba, sai ma uban tsalle da ta buga ta cukumi wuyan Nabila tana kai duka tana cewa: "Wallahi ba za ki daki banza, kwarankwasa dubu sai na koya miki hankali, hegiya tsigi-tsila da ƙafa kamar ta tsinken tsintsiya" Ganin ɗankwalin da ke kanta na niyyar kawo mata cikas ya sa ta fisge shi wurga shi ta baya sai kuwa ya sauka a kan fuskar Aseem, ban da tsami da bashi babu abin da yake tashi a cikinsa. Sai ga kitson kanta ya fito duk ya tuje hatta da tsagar kitson ta haɗe sai furu-furun amosani a saman kan.
Warin ɗankwalin ne ya doki fuskar Aseem har ya shaƙa da ƙofofin hancinsa ya sa shi farkowa daga suman tsayen da ya yi na wucin gadi. Aseem tun da ya zo duniya ba a taɓa yi masa abin da ya fusata shi lokaci ɗaya kamar abin da Dubu ta yi masa, dom shi abin daga haushi ma sai ya koma ba shi mamaki. Bakinciki da ganin yadda mutane suka zura masa ido ne ya ɓata masa rai har ya gagara sanin abin da zai aiwatar don ya wanke masa zuciya. Amma tabbas sai ya koya mata hankali don ya lura har lokacin Yaya babba ba ta ɗora ta a hanyar arziƙi ba.
Duk yanda Dubu ta so nunawa Nabila ƙarshen iyawarta abin ya ci tura don a girme Nabila ta girme ta da kusan shekara huɗu. Gudun kar a kunyatata cikin jama'a ya sa Dubu ta tattara ƙarfinta ta fara wani fisge-fisge kamar mai aljanu tana kai duka ta ko'ina, ai kuwa ta ɗaga ƙafa bisa taautsayi ta harbawa Aseem da ke saƙa da warwara akan irin abin da ya dace ya yi mata. A hassale ya ƙarasa wurinta cikin zafin nama ya fisgi hannunta. Cikin tsiwa da rashin sanin wa ya riƙe ta Dubu ta ce, "Wallahi duk wanda ya riƙe ni sai na yi masa jini da majina dalla ku sake ni wallahi ba za ta daki banza ba." Ai kuwa ya sauke mata mari a fuska, kafin wancen marin ya gama ratsa fuskarta ya sake kifa mata wani marin har sa da ta ga wasu irin taurari na gilma mata. A gigice Dubu ta buga tsalle cikin fitar hayyaci ta ce, "Innalillahi wayyo Baba Munkaila zai kashe ni wayyo! Inno fuskata."
Sauke hannun Aseem ya yi daidai da fitowar Yaya Babba za ta zagaya banɗaki. Da sauri ta saki butar hannunta ta fashe da kuka ta ƙarasa wurinsu, tana shirin riƙe hannun Dubu; Aseem ya sake fisgar Dubu ya nufi hanyar fita da ita. Duk irin kiran da Yaya Babba take yi masa ko waiwayenta bai yi ba bare ta saka ran zai tanka mata.
Duk yanda zuciyar Dubu take a bushe wannan karon sai da hanjin cikin ya kaɗa, tsoro ya mamaye ta musamman ta lura da irin ɓarin makauniyar da ta yi masa da garin masara. Suna zuwa soron ƙarshe ta yi ta maza ta fara ƙoƙarin fisge hannunta tana faɗin:
"Wai ina za ka kaini? Ka sakar mini hannu malam." Idanunsa sun kaɗa jawur saboda ɓacin rai don haka tambayar Dubu ba ƙaramin baƙanta masa rai ta ƙara yi ba. Bai tanka mata ba ya sake fusgarta da ƙarfin tsiya ya buɗe mota ya wurga ta sannan ya buɗe mazaunin direba ya zauna.
Ganin ya tuƙa mota da ya fice da gudun tsiya ya ƙara hargitsa hanjin ciki Dubu, don wannan karon har ta fara bubbuga gilashin motar tana ihu. Can gefen titi ya gangar ya faka motar sai dai uffan bai ce ba. Sai da ya share minti biyar a haka yana jin kukan da Dubu take yi da ɗan ƙarfinta, ya zaro ƴar ƙaramar bindiga ya juya yana ce mata.
"Idan baki rufe mini baki ba zan harbe ki na wurgar da banza a wurin nan." Wata ajiyar zuciya da Dubu ta sauke idan ka ji za ka yi tsammanin numfashinta na ƙarshe ne zai fita. Bata san lokacin da ta haɗiye kukanta ba, ban da raba idanu babu abin da take yi, haɗe da jin wata irin da-na-sanin zuwanta duniya. Saboda ta san da ba'a haifo ta ba babu wata ƙaddara da za ta haɗo ta shi har ya nemi kashe ta da bindiga murus ya wurgar a gefen hanya. Don tun da take bata taɓa ganin bindiga ido da ido ba sai dai ko idan tana daga moto ta hangota a hannun Sojoji ko ƴan sanda. Amma yau har ita ake yi wa iƙirarin harbewa da ita da rana tsaka. Tana son tambayarsa inda zai kaita amma tsoro ya hanata, tana cikin tunani ta ji ya sake fisgar motar da wani irin matsanancin gudu, ai kuwa ta ƙwalla uwar ƙara tare ta ƙanƙame jikin kujera.
YOU ARE READING
DUBU JIKAR MAI CARBI
FantasyDa sauri Yaya babba ta matsa baya tana zaro ido ta ce, "Dubu me nake gani kamar aski akanki." Dubu ta rushe da kuka ta ce, "Inno wallahi aski ya mini kuma wallahi ɗan iska ne." Cak Yaya Babba ta tana ƙarewa Dubu kallo sannan ta ce, "Dubu je ki can m...