4

601 17 0
                                    

*DUBU  JIKAR MAI CARBI*

LABARI DA RUBUTAWA

         AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITERS'S ASSO...

Labarin mallakin Duniyar Hausa Novels ne, za a ci gaba da sauraren ci gaban shi  bayan sakin wasu shafikan.

https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels

Ku dannan👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼 subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.

            4

  Wannan karon gabaɗaya turus suka yi da jin abin fa aka faɗa, kallon-kallo aka fara yi a tsakanin juna kowa da abin da yake nazari a zuciyarsa. Suna cikin haka suka sake jin an ce, "Bismillahir rahmanirrahim bari mu fara ɗauka daga kan ta bakin ƙofa." Ai Dubu bata rufe baki ba sai ji ta yi alamar guje-guje, Yahanasun Auwalu tun bayan sallar asuba da ta shiga ɗakin Inna Furai ba ta sake fitowa ba kuma ta ci alwashin ko da fitsari za ta ji sai dai ta matse abin ta, idan ta kama ma sai ta saki abin ta a wurin. To ashe tsugunne bata ƙare mata ba tun da ha fatalwar za ta iya kawo musu farmakin dare har cikin ɗakuna, tun da ta ji an ce za a fara ɗauka daga na bakin ƙofa.

Nabila ƴar wurin Hajiya Nafisa, budurwa ce don ta yi sha tara a shekaru. Turo baki ta yi tana cewa, "Maganar gaskiya Mommy ni fa na gaji da wannan abubuwan kullin abu ɗaya wacce irin fatalwa ana zaune ƙalau bayan kowa ya san babu wata fatalwa a musulunci." Cike da ƙosawa Hajiya Nafisa ta ce, "Nabila ya za mu yi kin san dai ba mu da ta cewa tun da zuwan nan na dole ne ya kama mu haka Allah ya ƙaddara mana." Yaya Babba da ke gefe fuskarta ban da gumi da maiƙo babu abin da take yi, ta dubi Hajiya Nafisa da kallon sheƙeƙe ta ce, "Ke Nafi! Zuman ku a gidan na shi ne ƙaddara. Wallahi za ki ga ƙaddara kuwa ganin idonki. Wannan gidan da kike gani kin zo kenan zuwa sojan badaskare." Tana gama faɗa ta yi ƙwafa a zafafe.  Dudu daga wurin da take ta jiyo hayaniya na tashi kaɗan-kaɗan ta sake shaƙe murya ta ce, "Ƴan sama jannati basa lamintar kuskure don haka za mu fara bi ta kan dabbobin gidan kafin mu fara taɓa mutanen ciki, ina tawagar Fatale ku fara dirowaaaa." A hankali ta lallaɓa da sauri ta buɗe ɗakin zabbin Baba Munkaila. Hannunta riƙe da muciya ta fara buga ƙyauren langa-langar da ke jikin ƙofar.  Nan da nan zabi suka fito a tsorace suka fara tsalle da kuka "Ƙurƙet! Ƙurƙet!"  Da yake da hasken wutar lantarki tuni zabbi suka fara bazama suna kuka, Dubu ta sa muciya ta riƙa make kawunansu ɗaya bayan ɗaya. Da ta bugawa zabo ɗaya sai ka ji ya yi ƙara ya faɗi ƙasa. Wannan kukan Zabbin ba ƙaramin ɗaga hankulan mutanen da ke cikin ɗakunan ya yi ba. Shiru suka yi suka zurawa sarautar Allah ido. Kowa da abin da yake ayyanawa zuciyarsa. Sai dai a wannan ƙadamin Lantan ta ci alwashin matuƙar tana da rabon ganin wayewar gari, babu wanda zai hanata tafiya don tun da ta zo duniya bata taɓa ganin masifa da tashin hankali irin wannan ba.

Zabbin nan gabaɗaya haka suka warwatsu suka shiga sauran sashen da ke cikin gidan. Muhsana ita ce ƴar autar Lantan, ta taho daga can sashen Baba Sule ba ta san abin da yake faruwa ba ta hangi Zabbin Baba Munkaila suna guje-guje wanda ya tabbatar mata da alama akwai abin da yake faruwa. Gabanta ne ya faɗi sakamakon ganin gawarwakin Zabbi kusan bakwai a ƙasa jini duk ya ɓata wurin. Sai dai har lokacin bata ga wanda yake aikata wannan abin ba, ɗaya zuciyarta ce take raya mata ko dai da gaske Fatalwar da ake faɗa ce ta fara aikinta, yayin da ta ƙara riƙe hannu Ɗanta Salihu don dama yaron ne ya fito da ita zai yi kashi. Ta bayan ɗakin Marigayi mai carbi ta je wucewa ba ta yi aune ba sai ji ta yi an fisgi hannun Salihu, aikuwa kusan tare suka ƙwalla ƙara daga ita har Salihun da ake ja, jan Salihu ta riƙa yi tana yi tana ihun neman agaji amma ba a daina jansa ba. Dubu na ganin Muhsana ta kusa fin ƙarfinta ta raɗa mata muciyar a baya tana cewa, "Ki taho mu yi rayuwar barzahu da ke. Ko ki bani Ɗanki Salihu na tafi da shi, ko kuma na ɗauke ku gabaɗaga." Muhsana bata gama jin ƙarashen maganar ba ta saki hannun Salihu ta yi cikin gida da gudu tana tafe tana sosa wurin da Dubu ta maka mata muciya. Shi kansa Salihu da ba a yi masa komai ba ya gama tsorata, dama jikinsa babu riga babu wando haka ya zuba a guje da tiƙeƙen cikinsa a daidai lokacin aka ɗauke wuta Salihu ya rasa wurin da zai bi haka ya riƙa gware da bango yana mage sauran zabbin da suma ta kansu suke yi.

DUBU JIKAR MAI CARBIWhere stories live. Discover now