*DUBU JIKAR MAI CARBI*
©AMEERA ADAM
FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV
FREE PAGE 11
Aseem kusan sandarewa ya yi da jin kalaman Dubu, don ya fahimci inda maganar tata ta dosa dukda bata faɗa yanda ake furtawa ba. Babban abin da ya fi ba shi mamaki yana yi mata kallon ƙaramar yarinya sakarai marar wayo, ashe shi take yi wa kallon haka? Tun da har ta san ta kira saurayi ta ce masa My Love, ba tare da kunya ko jin nauyi ba. Jin ya yi shiru ya sa Dubu ta saci kallon Yaya babba ta sake cewa:
"Me lob wallahi ina ta kewarka kuma na yi musun ɗinka." Yaya babba na jin haka ta saki murmushin farinciki, don bata ɗauka Dubu za ta iya nutsuwa lokaci ɗaya ta yi waya da saurayi a haka ba.
Aseem bai gama tunani ba Dubu ta sake jefa shi cikin kogin mamaki, da jin kalaman da idan za a sa mata wuƙa bata san takamaimai abin da suke nufi ba. Dubu ba ta damu da jin shirun da ya yi ba ta ci gaba da jawabi.
"Me lob dama kiran da na yi maka don mu gaisa ne, na san kaima ka yi kewata; kuma ban ji ka ce komai ba..." Tun bata ƙarasa ba ya buga mata tsawar da ta katse ragowar kalamanta da cewar: "Ke! Kina hauka ne?" A tsora ce Dubu ta zame wayar daga kunne, ganin haka ya sa Yaya babba ta kalleta tana faɗin, "Dubu lafiyarki kike razana kamar wacce aka ɗanawa wuta?" Wayar Dubu ta miƙa mata tana faɗin, "Riƙe ki ji abin da yake faɗa Inno." Da sauri Yaya babba ta karɓi wayar ta sa a kunne tana faɗin, "Sojaaa." Aseem na jin haka ƙit ya kashe wayar yana huci. Maganganun Dubu sun jima suna yi masa yawo a rai, yana mamakin har yaushe ta ga makwancinsa da za ta kira shi a waya tana ce masa My love.
Yaya babba ta yi zuru tana nazari sannan ta ce, "Dubu me kika yi wa Soja da zafi haka da zai hau yi miki barazana?" Dubu ta kwaɓe fuska ta ce, "Inno kina ji dai a gabanki na yi wayar." Wayar ta sake miƙawa Dubu ta ce, "Maza lalubo mini lambar Garba, alƙur'an idan shi yake zuge shi a kanki zan ji dalili. Saboda Allah me ya sa Garba ya cika hassada? Dama tun rannan na lura da hassadar da yake yi wa Soja akan aurenki. A'a ba halina ya gada ba bare kuma mahaifinsa, Allah ya sani wannan ɗabi'ar ƴan wuta ce idan kuma Garba ya ɗore a haka na shiga falsafar tashin hankali a ce jinina na da ɗabi'ar ƴan wuta ina na kama." Dubu ta gama dube-dubenta ta miƙawa Yaya Babba wayar ta ce, "Kin san dai ba iya nemo lambarsa na yi ba Inno kawai ki kira Baba Munkaila, ki sa ya kira shi" Suna cikin haka Salisu ya shiga shi da abokinsa Musbahu, da sauri Yaya babba ta miƙa masa waya ta ce, "Maza kira mini Garba." Da ido ya tsare Dubu da kallon tuhuma, don ya san ita take juya Yaya babba kamar waina, ya ce, "Me za ki ce masa Inno."
"Me ye ma ba zan ce masa ba Ɗan nan? Ka kira mini shi idan ba za ka kira ba, wuce ka kira mini ubanka ko Munkaila in sa su kira shi." Gudun magana irin na Yaya babba ya sa ya karɓa ya kira mata Baba Abubakar, sai dai an yi rashin sa'a wayar a kashe take.
Musbahu abokin Salisu cikin ladabi ya gaishe da Yaya babba ta washe baki ta ce, "Lafiya ƙalau Musbahu ya Uwale?" Ya amsa mata cikin girmamawa, Yaya babba ta ɗora da cewa:
"Ina ma Soja ya samu abokan ƙwarai irin ka Musbahu, don Allah da bai more ba? Don Allah waye ba ya san farantawa, ka duba yarinyar nan Dubu daga kiran Soja zai fara sauke mata falsafar rashin mutumci, ana zaune ƙalau don Allah wannan halin mutumci ne?" Musbahu ya yi murmushi ya ce, "Gaskiya bai kyauta ba Inno, amma ki yi haƙuri."
"Don Allah rabani da haƙurin nan Musbahu! Kai Salisu ba ina ji rannan Zulfa na ce masa tana kewarka ba. Musbahau don Allah ka ji wata lalata irin ta ƴaƴan zamani. Lokacin da aka ɗaura auren uwar Zulfa, ni kaina da nake uwar miji sai da ta kwana a ɗakina, kwananta biyu tana gudun miji za ta yi na uku na ce, a'a ta rabani da wannan falsafar kar Munkaila ya ɗau gaba da ni ana zaune ƙalau. Munkaila kunya Kulu kunya yooo gadon wa tayo a cikinsu na rashin kunya? Don Allah gane mini hanya Musbahu." Salisu ya karɓe zancen da cewa, "To ke tsohuwa ina ruwanki da sa ido ne?"
YOU ARE READING
DUBU JIKAR MAI CARBI
FantasyDa sauri Yaya babba ta matsa baya tana zaro ido ta ce, "Dubu me nake gani kamar aski akanki." Dubu ta rushe da kuka ta ce, "Inno wallahi aski ya mini kuma wallahi ɗan iska ne." Cak Yaya Babba ta tana ƙarewa Dubu kallo sannan ta ce, "Dubu je ki can m...