5

598 18 0
                                    

*DUBU  JIKAR MAI CARBI*

LABARI DA RUBUTAWA

         AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITERS'S ASSO...

Labarin mallakin Duniyar Hausa Novels ne, za a ci gaba da sauraren ci gaban shi  bayan sakin wasu shafikan.

https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels

Ku dannan👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼 subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.

            5

  Da sauri Baba Munkaila ya juyo yana muzurai don har lokacin banda huci babu abin da yake yi. Tun kafin ya ƙaraso Dubu ta riƙe hannun Yaya babba tana bata haƙuri, don duk cikin gidan babu wanda Dubu take tsoro kamarsa. Zuciyar Hajiya Nafisa fes don ko ba komai ta san zao gyarawa Dubu zama, yana ƙarasowa ya ce, "Inno ga ni." Yaya babba ta kalli Dubu da ta yi wuri-wuri sai zare ido take yi saboda gari banza ma Baba Munkaila ba ya raga mata ina ga yau da yake cike da haushin kashe masa zabbinsa.

Yaya babba ta ɗauke kanta daga wurin Dubu tana cewa, "Munkaila don Allah ka raba ni da yarinyar nan Dubu, ni take son yi wa ɗiban albarka. Wai don Allah meye haɗina da ita da ba za ka tafi da ita sashenka ba..." Tun bata gama magana ba Baba Munkaila ya zuba mata ranƙwashi a ka. Ai kuwa ta daka uban tsalle ta faɗa uwar ɗaki. Ganin haka ya sa Yaya babba ta sallame shi amma sam ba haka Hajiya Nafisa ta so ba.

Cikin Dare.

   Tun dare bai gama tsalawa ba ƴan bijilanti suka yi wa gidan Marigayi mai carbi dirar mikiya, hannuwansu ɗauke da gorori sai fitilun da suke haskawa masu ɗan karen haske. Ban da haske-haske babu abin da suke yi, da sun ji motso ko na dabbobin gidan ne za ka ga sun haske sun nufi wurin da gudu. A wannan ranar ma Dubu da wuri ta yi kwanciyarta don ta samu damar gabatar da aikinta idan ta farka ciki dare. Sai dai wannan karon tsoro ne mamaye a zuciyarta saboda irin gororin da ta gani a hannuwa su Duna da Kuraye. Tana son suma ta nuna musu iyakarsu amma tana shakkar ta inda za ta ɓullowa lamarin saboda sun zagaye ko'ina ga fitilun da suke haske-hasek da su.

Dabara ce ta faɗo mata don har sai da ta murmusa a fili saboda mugunta. Ta shi ta yi a hankali cikin sanɗa ta ɗauko butar Yaya babba sai da ta zo daidai kan Barira wacce take kwance da Ƴarta ta tsiyayawa yarinyar a jikinta , idan ka ga yanda ta yi sharkaf sai ka rantse da Allah fitsari ta yi. Ɗaga rigarta ta yi ta zaro guntun likkafanin da ta ɓoye sai ta ɗaura a ƙafar Baraka ƴar wurin barira. A hankali ta fara jan ƙafar yarinyar har sai da ta kaita ƙofar ɗaki, ta koma ta riƙa jan ƴaƴan mutane tana kaisu bakin ƙofa sai da ta gama sai kawai ta haɗa ƙafafuwa su ɗai-ɗai ta riƙa ɗaurewa da likkafani. Sai da ta kai kusan yara biyar bakin ƙofa sannan ta janyo tsintsitar kwakwa ta tsinka ta riƙa bi tana kartawa iyayen da yaran, da sauri ta bi gefe ta wurin da yaran suke kwance a bakin ƙofa ita ma ta yi luff ta tura ƙafarta ciki tasu. A hargitse mutanen ɗakin suka tashi carko-carko suka fara wawurar fitila, Barira na haska fitilarta a ka hango yaran suna firƙai-firƙai suna koke-koke. Kowacce da sauri ta je ta rarumi Ɗanta ai suna ganin Likkafani a ƙafar ƴaƴan kowa ya fara shan jinin jikinss.

Maraƙisiyya ta dubi Barira ta ce, "Don Allah Barira me idona yake gane mini kamar likkafani." Barira dama bakinta ƙunshe yake da magana don dai tana tsoron furtawa a samu matsala, ai kuwa tana jin haka ta yi farat ta ce, "Lashakka fihi wallahi likkafani ne don Allah ku taimaka mana fatalwar nan za ta ja mana yara." Jin wannan maganar ta Barira da sauran hayaniyar mutanen ɗakin ya sa Ƴan bijilantin suka tattaru a ƙofar ɗakin Yaya babba suna tambayar ba'asi. Dubu na ganin haka ta zari buta tana matse-matsen ƙarya wai fitsari take ji, da sauri Yaya Babba ta yi farat ta ce, "Dubu ki raba ni da wannan ƙaddararran fitsarin da za ki yi yanzu, so kike ki fita fatalwar nan ta yi gaba da ke?" Dubu ya sake zabura tana buga ƙafa ta ce, "Wallahi fitsarin ya matse ni."

DUBU JIKAR MAI CARBIWhere stories live. Discover now