Chapter One

131 5 1
                                    

Yau ma kamar kullum suna tsaye a kofar dakin daukar darasi, wato classroom a turance, bayan fitar malamin biology, wanda kuma ya kasance shi ne darasin su na ƙarshe a kowace ranar talata. A ƙalla sun dauki kusan mintuna bakwai suna tattaunawa game da darasin da suka gudanar kafin suka miƙa zuwa bakin gate din makarantar.
Makaranta ce babba wanda ya amsa sunan sa sannan kuma sai 'ya'yan wane da wane ne ke samun damar karatu a wurin. Isar su keda wuya suka samu motar gidajensu sun zo ɗaukar su.
"Noor sai gobe kuma in Allah ya kaimu. Kuma Please kada ki manta da alƙawarin da kika mun yau. Sannan please poem din ya tsaru sosai duk da dai nasan cewa ke din ba baya ba wajen rubutun poems."
Wacce aka kira da Noor tayi murmushin da ya ƙawata kyakkyawar fuskar ta sannan tace
"Ke kam Hibba bakya gajiya da surutu na rantse. Ji yadda kike ta zuba kamar 'ya'yan kurna."
"Noor yanzu ni ce mai surutu? Wai har kura ta ce da kare maye." Hibba ta faɗa tana nufar motar gidansu.
"Ki gaida mun da Ammiey da darling sweetheart ɗina." Ta ƙarasa faɗa tana bude motar.
Murmushi Noor tayi tana mamakin irin shakuwar dake tsakanin ƙaramin kaninta kuma autan gidansu da Hibba. Dan ko bata faɗa ba tasan Muhammad Jawad take nufi.
"Barka da rana yaya Auwalu." Ta gaisar da matashin drivern nasu dai-dai lokacin da ta zauna a mazaunin ta.
"Yawwa Noor ya makarantar?" Ya tambaye ta da sakin fuska. Shi dai yarinyar tana matukar burge shi kasancewar ta mai girmama na gaba da ita. Shiyasa duk 'yan aikin gidan suke sonta sosai. Kasancewar Auwalu driver ya dan yi makaranta shima sai ya zamana duk lokacin da yaje daukar ta sai suyi ta hirar makaranta har su iso gidan. Yauma kuma hakan ce ta kasance.
Isar su gidan babu bata lokaci ta sauka daga motar tana masa godiya kamar yadda ta saba sannan ta shiga cikin gidan inda ta iske Ammiey wato mahaifiyar ta tana ta faman girke girke.
"Barka da gida Ammiey na." Ta faɗa tana zama a daya daga kujerun dan madaidaicin dining table din dake kitchen din.
"Barka dai Noorie ya makarantar?" Ta tambaya ba tare da ta kalli diyar tata ba, wanda kuma sam ba haka ta saba ba.
"Lafiya klau Ammiey. Mom ina Jay ban ganshi ba."
"Sun fita Masallaci da mahaifin ku." Ta bata amsa a takaice.
"Ok." Shine kawai abun da Noor ta faɗa tana ficewa daga kitchen din ganin mahaifiyar ta kamar bata son doguwar magana.
Tana shiga dakinta uniform ta fara cirewa sannan ta shiga tayo wanka tare da dauro alwala. Kammala sallar ta keda wuya sai ga Jawad ya shigo da gudu ya faɗa jikinta.
Murmushi tayi ta hau tambayar sa ya makarantar su yana bata amsa. Zama sukayi daga ita har shi din suna hirarsu gwanin ban sha'awa. Sai kusan karfe biyu da rabi Ammiey ta aika aka kira su don cin abinci.

*****

"Amma baka ganin bamu kyauta wa Noor ba idan muka mata haka." Ammiey ta faɗa tana kallon mai gidan ta.
"Juwairiya! Kada muyi haka dake. Ba mun gama magana ba tun rannan? Ki tuna fa, Janna ba karamar yarinya bace, ta fara girma. Kuma sanin kanki ne yin hakan kadai shi zai sa muyi nasara wurin samun wannan contract din da muka dade muna nema."
"Haba maigida! Mai yasa kake son saka rayuwar 'yarka a matsala saboda kasuwancin ka yayi karfi? Kar ka manta fa, watanni biyu da suka gabata Noor ta cika shekaru goma sha-bakwai a duniya, taya kake tunanin aurar da ita ga wanda bai san taba kuma itama bata san shi ba? Taya hakan zai kasance?" Ta faɗa daidai lokacin da wani siririn hawaye yake fita daga idon ta.
"Ki fahimce ni matata, sanin kanki ne bazan taba cutar da 'yata ba. Ni nasan wanene JUNAID kuma nasan ba zai taba cutar da ita ba. Sannan mahaifin shi Alhaji Arabi aboki na ne kuma abokin kasuwanci na (business partner). Saboda haka ina so ki kwantar da hankalin ki, insha'Allah babu abinda zai faru sai alkhairi." Ya faɗa trying his best to make her understand.
"Amma baka tunanin mu fara jin ra'ayin ta game da hakan?"
"Mai yasa kike yi kamar baki san halin 'yar ki ba? Tana da biyayya. Na tabbatar zata amince da duk abinda muka yanke a kanta."
"Shikenan Allah ya shige mana gaba." Shine abinda tace, ba wai dan ta yarda da abunda maigidan nata ya faɗa ba. Ita a ganin ta ya kamata su nemi shawarar 'yar su kafin zartar da irin wannan babban al'amari akan ta. Amma ba komai. Zata cigaba da mata addu'a dan tasan shine kadai abunda 'yar tasu tafi bukata.
Kitchen ta wuce don tabbatar da komai yana tafiya daidai yanda ya kamata kasancewar a yau ne Junaid da mahaifinsa zasu kawo musu ziyara.
Zuwa karfe shida komai ya kammala har an jera abinci bisa teburin cin abinci (dining table) bakin kawai suke jira su iso.

Ammiey ce zaune ita da 'ya'yan ta bayan sallar isha suna hirarsu kamar yadda suka saba, sai dai yau hirar yawanci akan bin iyaye take yinshi wanda za'a iya kira kai tsaye da hannun ka mai sanda.
Ƙarar kararrawar kofa (door bell) suka ji wanda ko ba'a faɗa ba sun san mahaifin su ne ya dawo. Noor ce ta mike kai tsaye ta isa kofar tare da bude kofar. "Barka da dawowa da..." Maganar ce ta makale a makoshin ta daidai lokacin da idanun ta suka sauka a cikin nasa idanun...

Fateedau📌

NOORUL JANNAWhere stories live. Discover now