Chapter Four

22 5 0
                                    

     Da yamma bayan sallar la'asar Noor ce zaune kan sallayar da tayi sallah bata kai ga tashi ba don tun da ta idar da sallar take zaune ta tsunduma kogin tunani. Hakika duk wanda ya kalli Noor a wannan lokaci ba ƙaramin tausaya mata zai yi ba domin gaba daya ta fita daga hayyacin ta. Ga wata uwar rama da tayi sai kace wacce ta shekara tana jinya. Dama ba wani auki ne da ita ba sai ya zama ta sake figewa.
Kofar dakin da take ake ta knocking hade da sallama amma sam bata san ma ana yi ba dan hankalin ta sam baya jikinta. Da Hibba ta gaji da knocking ta shigo. Idon ta ne ya sauka akan kawar ta wacce ta jinginar da kanta a jikin gado tayi nisa cikin tunani ga wani siraran hawaye na bin kwarmin idon ta. Cikin sassarfa Hibba ta ƙarasa ciki tare da durƙusawa a gaban ta amma still bata san da wanzuwar ta a wurin ba.

"Noorieee."
Hibban ta faɗa tana girgiza ta.
Firgit ta dawo hayyacin ta ganin Hibba yasa tayi saurin rungumeta tana me fashewa da matsanancin kuka mai taba zuciya. Ganin irin kukan da take yasa Hibba fahimtar lallai ba kalau ba akwai damuwa. Nan da nan itama ta fara hawaye dan ba karamin shakuwa bace tsakanin aminan guda biyu. Sai da Noor tayi mai isar ta kamin Hibba ta rarrashe ta sannan ta tambaye ta meke faruwa.
Nan take ta sanar mata inda jikin Hibba yayi sanyi sannan tausayin kawar ta ya cika mata zuciya.

"Hibba bana kaunar auren nan wallahi ban so ko kadan. Hibba ban san wani laifi na aikata ba ake son hukuntani ta wannan hanyar."

"Noor kiyi hakuri inshaallah babu abun da zai faru tunda Ammiey tace zata wa dad magana idan ya dawo."
Hibba ta bata amsa reassuringly.

"Bana tunanin dad zai amince da maganar Ammiey. Kuma shima wanda zasu aura mun din baya so baki ga rashin mutuncin da yazo har gida yamun ba ne dazu."

Ta ƙarasa tana bata labarin duk abinda ya wakana tsakanin ta da Junaid din.
Sosai tashin hankali ya bayyana a fuskar Hibban. Wannan wace irin kaddara ce take neman sauka a kan kawar ta?
Cikin lallami ta rinka bata baki tana kwantar mata da hankali har ta samu taci abincin da Ammiey ta dafa.
Sai can bayan magrib Hibba ta koma gida tausayi da kuma tunanin halin da kawar ta take ciki fal ranta.

*****
Karfe 9:07 na dare agogon dake manne jikin bangon dakin ya nuna. Dad ne zaune cikin kujera mai cin mutane biyu sanye cikin ash colour jallabiya da kuma siririn farin glass a idon sa yana duba magazine ɗin hannun shi, lokaci zuwa lokaci kuma yana daga ido yana kallon labaran da aka fara na BBC.
Da sallama Ammiey ta shigo tayi wa kanta mazauni gefen maigidan nata.

"Barka da dare Alhaji."

"Yawwa uwargida a gidana."

Ya amsa yana sakar mata lallausar murmushi. Duk da shekaru sun ja amma har yau son da yake mata bai ragu ba koda da kwayar zarra ne. Itama murmushin ta mayar masa tana gyara zama domin so take su fuskanci juna.

"Kamar kina da magana koh? Ina sauraron ki I'm all ears." Ya fada still with that smile a fuskar shi.

"Dama Alhaji akan Noor ne. Sai nake ganin kamar bamu bi hanya mai kyau ba. Bawai ina nufin wani abu bane a'a. Amma duba da yanda yarinyar bata son abun sai nake tunanin me zai hana a fasa gudun jefa rayuwar ta a matsala."
Lokaci daya fara'ar dake fuskar dad ta dauke da yaji maganar da Ammiey tazo masa dashi. Cikin kakkausar murya yake fadin:
"Juwairiya kina ganin kamar bana son 'ya ta ne? Look, bari kiji. Kamar yadda kike son ta haka nima nake sonta. Maybe more than you do. So please bana son sake jin irin wannan zancen. Or do you want me to lose that contract I am about to sign?"

Cikin karyewar zuciya Ammiey ta fara magana "Amma Alhaji bai dace kayiwa 'yar ka auren dole ba akan wani selfish reason naka. Wato idan na fahimce ka kudi sun fiye maka welfare din family dinka." By now hawaye ne ke fita daga idanun ta.
Ba tare da ya damu ba yace "Yes. I value money over everything. Maybe it's because baki san amount of billions da zan samu bane shiyasa." Yana gama fada ya mike ya fita leaving her there.
Sosai Ammiey ta shiga damuwa gashi ta rasa yadda zatayi ta shawo kan maigidan ta wanda sam ba haka yake ba a da. Bata san meya faru ba lokaci daya alkiblar sa ta canza. Amma koma menene zata dage da rokon Allah don babu abun da yafi karfin sa.

NOORUL JANNAWhere stories live. Discover now