Chapter Three

20 7 0
                                    

Cikin bacci taji ana shafa mata fuska wanda hakan yayi sanadin bude kumburarrun idanun ta. Ammiey ce ta gani zaune a gefen gadon da murmushi a fuskar ta wanda kallo daya zaka masa ka tabbatar bai kai har zuciyarta ba, sannan idanun ta ma sunyi ja alamun tana cikin damuwa.
"Good morning Ammiey na."
"Morning my daughter. Ki tashi maza kiyi shirin makaranta kada ki makara." Ammiey ta umarce ta.
Ba dan taso ba ta mike daga kwancen da take tayi hanyar banɗaki. Jiki a sanyaye Ammiey tabi ta da ido har ta shige. Mikewa tayi itama ta bar dakin don zuwa ta kammala sauran aikace aikacen ta.

Koda Noor ta fito daga wanka uniform kawai ta saka ta dau School bag dinta ta fito. Direct hanyar fita tayi tana cewa Ammiey sai ta dawo.
"Noor baki yi breakfast ba zaki tafi? Dawo maza ki zauna kici abinci." Ammiey ta umarce ta.
"Bana jin yunwa Ammiey. Anjima zanci wani abu a school. But for now I don't have the appetite." Ta faɗa tana kokarin maida kwallar dake son zubowa.
Ammiey bata ce komai ba ta dauko wani karamin warmer daga kitchen ta deba mata komai a ciki ta mika mata. Ba musu tasa hannu ta karba sannan tayi mata sallama ta wuce.

Sam bata taɓa kawowa a ranta ba wai wata rana rayuwar ta zata canza izuwa haka ba. Ko jiya da suka rabu da Hibba tana cikin farin ciki and she was living her normal life. Da wani zai ce mata hakan zai faru da ita san baza ta yarda ba amma sai gashi cikin lokaci kankani komai yana neman canzawa.
Sam gaba daya yau Hibba ta kasa gane kan kawar ta a makarantar dan sam ta kasa maida hankali ta saurari darasin da ake yi. Yin duniya kuma ta tambaye ta amma ta ki faɗa mata damuwar ta. A haka dai ta lallaba har aka tashi ta wuce gida, dan ko hirar da suka saba yi basu yishi ba yau. Ita dai Hibba ido ta zuba mata amma a ranta ta kudiri zuwa gidansu Noor din don gano meyake faruwa.

Isarta gida ta samu Ammiey ta fita hakan yasa ta wuce zuwa dakin ta inda tayi Sallah sannan ta fito dan neman abinda zata ci don ko da ta je school bata ci komai ba. Kitchen ta nufa ta daura noodles sannn ta yayyanka vegetables da yawa ta sa a ciki kasancewar ta da son veges. Bata dau wani lokaci mai tsayi ba ta kammala sannan ta juye shi a plate ta fito dashi yana tururi sai kanshi yake.

***

Ganin bashi da aiki mai yawa ya sanya Junaid mikewa ya nufi hanyar fita daga kayataccen office dinsa. A hanyar sa ta fita ne ya hadu da Catherine wacce ta kasance secretary dinsa ce ita.
"Boss, you have a meeting with Mr Ibrahim in 50 minutes time." Ta faɗa tana tsare sa da idanuwa. Allah ya sani tana tsananin son Boss din nata amma taga shi harkar mata baya gaban shi. Amma duk da haka zata daura damara dan ganin cewa ta sameshi.
"Schedule it for another time." Iyakar abin da ya faɗa kenan a takaice ya wuce ya barta tsaye. Bayansa tabi da kallo tana hasaso ranar da zata mallakesa a matsayin nata.

Junaid sam bai ma san me take ba. Yana fita motarsa ya shige ba tare da neman inda drivern sa yake ba ya bar Company ɗin. Sosai yake zuba gudu akan titi don a yanzu so yake kawai ya isa inda zashi ya aiwatar da abin da yayi niyya. Few minutes ne ya kaishi destination dinshi sakamakon rough driving da yayi. Cikin kasaita da isa ya fito daga motar ya nufi gate din, a zuciyar shi yana me fatan iyayen ta basa nan.
Direct cikin gidan ya wuce kasancewar maigadin ya gane shi shiyasa ba wani bata lokaci ya wuce.

Cikin nutsuwa take naɗo noodles din da fork tana yinshi a hankali kasancewar hankalin ta sam baya jikinta. Ɗagowa tayi ta kai cokalin bakinta wanda hakan yayi daidai da fara kwankwasa kofar sitting room din. A hankali Noor ta mike sannan ta nufi kofar cikin tafiyar ta mai kyau da daukar hankalin mai kallon ta wanda wasu suke ganin kamar da gangan take irin wannan tafiyar. Abun da basu sani ba shine ita bata ma san cewa haka tafiyar tata take ba.

Tana isa bakin kofar ta bude a hankali dan tun da Dad ya mata maganar nan ya zama jikinta yayi sanyi komai tana yinshi ne cikin dauriya.
Kallo daya tayi masa ta fahimci shine baƙon da suka zo tare da mahaifinsa kuma wanda Dad yake shirin aura mata.
Tabbas yaji karar bude kofa amma jin kan shi ya hanashi juyowa. Sai daya bata lokaci kafin ya juyo yayi mata kallon tsaf wanda yafi kama da na kaskanci sannan ya daidaita tsayuwar sa tare da soka hannayen shi duka biyu cikin aljihun wandon shi. Hakan da yayi kuma ba karamin kyau yayi masa ba kasancewar sa daya daga cikin jerin maza da ko wane irin dressing sukayi yana musu kyau.

"Good afternoon."

Iyakar abin da ta faɗa kenan ta sunkuyar da kanta kasa don baza ta juri kallon shiba sakamakon kwarjinin da ya mata.

"What is good about the afternoon? Look I'm not here for exchanging pleasantries. Nazo ne na baki shawara guda daya."

Dago ido tayi ya kalle shi ganin yadda ya haɗe rai fuska sam babu walwala yasa cikin faduwar gaba ya mai da kanta kasa.

"Our parents are planning on getting us married and ni kuma bana son auren cause I have wacce nake so kuma take so na. She's a grown-up unlike you karamar yarinya dake amma har kinsan aure ko? To bari kuji. I have a great respect for my father shiyasa bazan iya masa musu akan auren ba. I want you to meet your parents, ki faɗa musu cewa baki sona kar su miki aure dani. Idan kin kika yadda ƙaddara ta kawo ki gidana matsayin mata wallahi sai kin gwammaci ba'a haife ki ba banza kawai mai kama da mayu."

Ya karasa faɗa cikin tsawa, sannan ya juya cike da ɓacin rai ya bar wurin dan ba kadan kanshi yake sara mishi ba sakamakon dogon maganar da yayi. Zai iya cewa tunda ya mallaki hankalin kanshi baiyi magana mai tsawon wannan ba.

Hakika Noor bata taɓa shiga tashin hankali irin na yau ba. Ga wani mahaukacin rawar da jikin ta yake yi. Haka ta ja jiki ta koma ciki da kyar ta samu ta zauna a kujera tana maida numfashi ga hawayen baƙin ciki dake sintirin fita daga idanun ta. Sam ta ma manta cewa abinci zata ci dan gaba daya yunwar ma ta kau.
Lokaci daya tarin tsoro da kuma fargaba ya taru ya mata yawa wanda tasirin sa yasa taji numfashin ta na kokarin daukewa. Tabbas ta san bata kaunar auren da dad yace zai mata amma kalaman Junaid sun kara ingiza zuciyarta wurin kin auren. Ita yanzu ya zatayi da Dad ya fasa mata wannan qaddararren auren? Gashi kuma from all indications dad is serious dan he has never been this serious a rayuwarsa.
Wani raunataccen kuka ne ya kwace mata a lokaci guda ta shiga rerashi dan tasan babu abin da zai rage mata wannan radadin da take ji a zuciyarta.
Hakika duk wanda ya kalli Noor a wannan yanayi dole ne ya tausaya mata dan a lokaci daya ta fita daga hayyacin ta dan har wata rama sai da tayi.
A tsakanin wannan lokacin ne kuma Ammiey ta dawo daga taron da aka gudanar a Company din maigidan ta. Wani irin bugawa kirjinta yayi lokacin da tayi tozali da 'yarta tana faman kuka cikin fitar hayyaci. Tashin hankali da kiɗima ne suka bayyana akan kamilallar fuskanta sannan cikin sassarfa ta ƙarasa wurin 'yar tare da rungumo ta gaba daya zuwa jikin ta.

"Noorie meya faru me ya same ki?"
Ta tambaya tana girgiza ta.
Jin muryar mahaifiyar ta ya kara haddasa karfin kukan. Ƙanƙame Ammiey tayi sannan cikin kuka take faɗin
"Ammiey na dan Allah ki cewa dad bana son auren nan idan ma wani abun nayi mashi yake son hukunta Ni kada ya hukunta ni ta wannan hanyar." Ta ƙarasa faɗa kukan nacin karfin ta.
Allah sarki mahaifiya nan da nan kwalla ya kawo idon ta tayi saurin ɗauke shi dan kar 'yar ta ta fahimci halin da take ciki. Daurewa tayi ta fara faɗin
"Ya isa haka Noorie dena kukan kar ki kawa kanki wani ciwon. Insha Allahu yana dawowa zan  masa magana ki kwantar da hankalin ki." Cikin tausasawa take maganar.
Idon ta ne ya sauka a kan plate din abincin da kallo daya tayi ta fahimci loma daya kawai Noor din tayi. 
"Maza tashi kici abincin ki gashi kin barshi yana ta sanyi."
"Na koshi Ammiey I have no appetite."
Haka Ammiey ta cigaba da kwantar mata da hankali har ta dan sake zuciyarta.

*

Sorry it took me long to update. I was super busy with other things.

Fateedau

NOORUL JANNAWhere stories live. Discover now