Chapter Twelve

41 4 1
                                    

Bayan fitar Junaid daga gidan bai zarce ko'ina ba sai gidan su amininsa wato Saif. Sun dade suna hira amma yawancin hirar tasu Saif ne ke zolayar sa kan ya baro amarya ita kadai a gida maimakon ya zauna yasha honeymoon.
"Kai fa wani lokacin banza ne Saif. Kana abu kamar baka sanni ba? Mai zanyi da wannan yarinyar bayan inada wacce nake so? This girl you're talking about is just a teenager. Amfanin me zatayi banda aikin gida?" Ya faɗa ranshi na neman ɓaci.
"Haba Junaid. Ban sanka da haka ba wallahi. Kar ka manta kamar yadda kake ɗa haka itama 'yar wasu ce. Kuma matar ka. Sannan tana da hakki a kanka." Saif was trying to make him understand.
"Spare me wannan nonesense talks din. Ba wa'azi nazo kayi mun ba. Nazo ne kawai cause I was bored at home amma kana neman bata mun rai. Me ruwan ka da rayuwar da na zaba wa kaina? Koma me zanyi ka zuba ido kawai kayi kallo. Wannan yarinyar ba zabi na bace saboda haka she can go to hell!" By now he was boiling with anger. Tun asali dama Junaid badai zuciya ba. Amma kuma yana da saukin kai sosai ga wanda ya fahimce shi.
"Junaid wallah bazan tsaya kallon ka kana aikata ba daidai ba nayi shiru. Sai dai kayi duk abinda zakayi. And don't forget, she's your wife so you got to treat her as..."
"Enough! Enough Saif. Kar ka sake cewa matata ce ita. She's not my wife ita din 'yar aiki ta ce." Da karfi yayi maganan fuskarsa tayi jaa alamun ɓacin rai ya bayyana sosai dan har rawa jikinsa yake.
Shi fa da gaske yake bazai taba kallon ta a matsayin mata ba. Haba wannan ai rainin wayo ne ma ace wannan karamar yarinyar ce matar sa. Shi fa bashi da burin da ya wuce ya auri age mate dinsa just like his Princess. Amma gaba daya mahaifinsa ya ruguza masa wannan tsarin ta hanayar auro masa wannan mayyar. Sai dai duk zai nuna musu shima ya isa da kansa and zai iya yankewa kansa hukunci da kansa. Yasan idan ya sake ta mahaifinsa zaiyi fushi dashi saboda haka azaba zai mata wanda ita da kanta sai ta nemi a raba auren.
Tashi yayi bayan ya zabgawa Saif wata uwar harara sannan ya saki tsaki ya wuce dan ba karya Saif ya bata masa rai. Da yasan abinda zai zo ya tarar kenan da bazai zo bama.

Daga nan direct gida yaje inda ya tarar da mahaifinsa zaune yana duba jaridar daily trust. Kusa dashi ya zauna bayan sun gama exchanging pleasantries sannan ya tambaye shi ya amaryar sa. Sosai yayi kokari wajen danne fushinsa da yaji yana neman sake tasowa sakamakon tambayar da Abba yayi masa. Murmushin dole ya manna wa fuskar shi sannan ya amsa masa. Sun dan taɓa hira kadan duk da dai yawanci kan business ne kafin suka tashi kowa ya dauro alwala suka wuce masjid don gabatar da sallar magrib. Basu dawo ba har saida akayi Isha. Junaid bai shiga cikin gidan ba yayiwa mahaifinsa sai da safe daga waje declining his father's request na ya shiga suyi dinner tare. Yafi so yaje ya samu abincin da housemaid zata dafa yaci dan yasan mai dadi zatayi. Just today yaji bazai iya cin abincin John ba duk da tun asali John ne ke musu girki a gidan Abba.
Mota ya shiga sannan ya wuce Allen Avenue amma zuciyarsa cike take da bakin cikin maganganun Saif. Wallahi Saif ya raina Ni ba kadan ba. Zanyi maganinshi ne.  Ya faɗa a zuciyarsa. Dialing number Princess yayi amma bai shiga ba. Take zuciyarsa ta sake hasala ya figi motar kamar itace mai laifin. Parking yayi roughly sannan ya wuce cikin gidan. Bai zarce ko'ina ba sai bathroom yayi wanka ya shirya cikin kayan baccinsa masu kyau sannan ya dawo downstairs dan yaci abinci. Ganin babu alamar abinci a dining din parlor yasashi wucewa kitchen sai dai nan ma babu sai dai ragowar Lasagna din dazu. Me yarinyar nan take nufi dani? Nine zanci wannan jagwalgwalon? Ya faɗa referring to sauran abincin ranan. Bai bata lokaci ba ya wuce direct zuwa dakinta ya tura ya shiga baiko yi sallama ba. Shigarsa kuwa yayi daidai fitowar ta daga bathroom da ɗan guntun towel dinta da bai ko kai gwiwa ba. Gabanta ne ya fadi ganinshi a dakinta yasa tsoro ya kama ta har towel din na neman faduwa. Da sauri ta riƙoshi da kyau sannan ta dauki babban hijabin ta ta daura a kai. Duk abinda take yana tsaye ko gezau baiyi ba bare ma tayi tunanin zai fita sai ma kara gyara tsayuwarsa da yayi.
"Baki san aikin ki bane kokuma uban me kika tsaya yi without making dinner?"

Kamar daga sama taji saukar maganar a kunnenta.
"Thought you will not need it shiyasa ban dafa ba."

"You what? Yau na sake tabbatarwa ke ba karamar dakikiya bace. How dare you? Kina housemaid kice baki making dinner ba? Infact you're... Oh my God!" Ya ƙarasa sounding frustrated. She's just adding to his anger.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 12 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

NOORUL JANNAWhere stories live. Discover now