Chapter Two

33 6 0
                                    

Sam bata yi zaton dad tare da baƙin nashi zai dawo ba hakan yasa ta tsaya tana mai mamakin ganin baƙon fuska a kofar tasu.

"Noor lafiya kuwa kike ta tsaye? Ko dai babu kowa ne?" Muryar Ammiey ta katse mata tunanin da take yi. Cikin sunkuyar da kai ta koma ciki ba tare da ta sake magana ba.
"Assalamu alaikum."
Muryar sa ta doki dodon kunnen ta.
"Wa'laikum Salam Junaid." Ammiey ta amsa masa daidai lokacin da su dad suke shigowa dauke da tasu sallamar a kan lebban su. Amsa musu sukayi inda yaran suka gaishe su sannan suka bar sitting room din kasancewar haka ɗabi'ar gidan take yara basa zama a wuri in da baki.
Sun dan taɓa hira kadan inda daga baya Ammiey ta gabatar musu da abinci sannan kowa yaci yayi nak don Ammiey ba baya ba wajen sarrafa abinci.
Ita dai Noor gaba daya ta kasa sakewa dan tun da ta daura idanu a kansa taji gabanta yayi mummunar faduwa, ga kuma mutuwar da jikinta yayi wanda ya jawo har dad saida ya tambaye ta ko akwai abinda ke damunta. Ita dai tace masa babu komai amma deep down she feels uncomfortable in this stranger's presence. Amma abinda ya daure mata kai bai wuce rashin maganar sa ba dan tun bayan gaisawar da yayi da Ammiey bai sake cewa komai ba, sai ma danna wayarsa da yake ta faman yi. Lokaci zuwa lokaci kuma yana sakin murmushi wanda hakan ke nuni da yana jin dadin koma menene yake yi da wayar tasa.
Basu wani jima sosai ba a gidan suka yi musu sallama suka koma masauƙin su don dama dad ne da abokin sa suka shirya haɗuwar don 'ya'yan nasu suga juna.

Bayan tafiyar tasu ne dad ya umarce Ammiey da duk bata da wani cikakken natsuwa da ta je ta kira Noor yana da magana da ita. Jiki a sanyaye Ammiey ta isa dakin inda ta iske ta tana faman rubutu inda sai tayi nazari kafin take rubutun. A hankali ta iso bakin gadon tare da zama gefen Noor din.
"Rubutu ake yi ne?" Ta tambaya cikin kulawa.
"Eh Ammiey. Poem ne Hibba tace na rubuta mata shine nake so na kammala kafin nayi bacci." Ta faɗa tana murmushi.
"Toh shikenan amma ki tashi maza kije mahaifin ku na neman ki yanzu. Ki sameshi a dakin shi."
"Ok Ammiey. Jay yayi bacci ne?"
"Eh yayi bacci tun dazu." Ammiey ta amsa tana ficewa daga dakin dan duk sai take jin jarumtar da ta aro yana neman kaucewa.

Cikin hanzari ta amsa kiran dad ɗin dan ba kasafai yake kiranta haka ba sai idan akwai wani muhimmin abu. Ba tare da kawo komai a zuciyar ta ba tayi sallama kamar yadda ta saba sannan ta jira ya bata izinin shiga. Ko data shiga ta sameshi ne a zaune alamar ita yake jira. Cikin nutsuwa ta sake gaisheshi. Duk da Noor ta kasance cikin jerin mutane masu surutu amma hakan sam bai bari nutsuwa ta kaurace mata ba.
Amsawa yayi tare da ɗan nazarin ta na wani lokaci. Tabbas sai yanzu ne yake gaskata maganar Ammiey na cewa Noor tayi karama a aurar da ita. Amma babu yanda ya iya dan yana bukatar sealing wannan deal din matuƙa. Kuma hakan ba karamin bunƙasa kasuwancin sa zai yi ba.
Gyaran murya yayi sannan ya fara magana kamar haka:

"Janna! Kinsan cewa mu iyayen kine sannan bazamu taba yin wani abu da zai cutar dake ba. Sanin da na miki na kasancewa yarinya mai biyayya yasa na amince da kudirin abokina Alhaji Arabi na nemawa ɗan sa auren ki. Saboda haka ina so ki mana biyayya kamar yadda kike mana a da. Kada ki watsa mana kasa a ido dan yardar da nayi dake ne yasa na amince ba tare da neman shawarar ki ba."

Tun da ya fara magana gabanta yayi wani mummunan yankewa ya fadi. Salati kawai take yi a zuciyarta tanajin wani abu na tasowa tun daga cikin ta zuwa makoshin ta. Hawaye take kokarin dannewa don karsu zubo amma ina, sai da suka betraying dinta suka zubo. Kasa daga ido tayi ta kalli mahaifin nata duk yadda zuciyarta take ingiza ta ta kalle shin dan gani take wannan ba dad dinta da ta sani mai kaunar ta bane. Taya rana tsaka zai taso mata da magana mai girma irin wannan? Aure fa? Ita a shekarun ta da basu haura goma sha bakwai ba ta ina zata fara? Gaskiya da sake. Bazata iya ba Allah ma ya gani.
Da kyar ta tattaro sauran nutsuwar da bai gama rugujewa ba ta fara masa magiya.
"Dad please kar ka mun haka. Wallahi ban shirya aure yanzu ba. Dan Allah kayi hakuri kaimun rai. Abba idan wani laifin na maka ka yafe mun amma kada ka aurar dani yanzu kuma ga wanda ban sani ba."
Ta ƙarasa tana fashewa da matsanancin kuka mai karyar da zuciya. Cigaba tayi da rokonsa tana kuka cikin ran ta tana mai fatan ya janye maganar da ya faɗa.
Ilai kuwa kukan ta ya taba zuciyarsa amma daya hasaso yawan maƙuden kudaden da zai samu sai ya samu kansa da tunanin tabbas idan ya rasa waɗannan kuɗaɗen ba karamin asara zai yi ba. Haka ya rufe ido ya cigaba da mata nasiha daga karshe ma kawai umarni ya bata. "Idan kinsan ni na haife ki to kada ki bijire min ki aikata abin da na umarce ki." Abun da ya faɗa kenan ya barta a wurin ita kadai. Rushewa tayi da sabon kuka ta rasa me yake mata dadi a duniyar. Jitayi an dafa ta ta baya. Ko bata juyoba tasan mahaifiyar ta ce. Rungumeta tayi tareda sakin kuka mai taba zuciya. Ita kanta Ammiey kukan take dan sam ta kasa gane kan mijin nata dan da sam ba haka yake ba.
Da lallashi da nasiha ta samu ta kai ta dakinta ta kwantar tare da ballo mata Panadol ta bata dan tuni zazzafan zazzaɓi ya kama ta. Ita dai Noor ta kwanta ne kawai bawai dan zata iya bacci ba. Haka ta kwana tana kuka inda maimakon zazzaɓin nata ya sauka sai ma kara hawa da yayi.

*****

Kallon mahaifin nasa yake kamar wanda bai taba arba dashi ba a rayuwarsa. Meyasa Abba zai masa haka? Mai yasa zai bijiro mishi da abun da ya tabbata bazai iya dauka ba? Auren karamar yarinya wacce ko girma bata gama ba? Bayan haka ma yacewa Maryama mene? Mahaifin sa ya zaba masa matar aure kenan bayan duk alkawarin da ya ɗaukar mata? Kai ina! wannan abu sam ba mai yiwuwa bane.
"Son ina so ka yarda ka auri yarinyar please don ni dinnan shaida ne akan tarbiyyar ta. Kuma besides tana da hankali sosai. Ai ka ganta da muka je gidan su." Abba ya katse masa tunani.
Kasancewar sa mai tsananin biyayya ga Abban kasancewar shi kadai ya rage masa, mahaifiyar sa ta dade da rasuwa tunkan ya mallaki hankalin kansa. Shiyasa yake matukar girmama mahaifin nasa don ya maye masa gurbin da mahaifiyar ce yakamata ta cike.
Ba tare da ya nuna rashin amincewarsa da maganar ba ya mike ya wuce dakinsa kai tsaye. Zama yayi a bakin gado ya rasa me zaiyi yaji dadi. Wannan babban al'amari da yake shirin tunkaro sa a gefe ga kuma Maryama da ta addabe shi da kira tun yana wurin Abba.
Tunani dai babu irin wanda bai saka ba inda daga karshe ya hakura ya kwanta tare da kashe wayar sa ya ajiye dan bazai iya magana da Maryama ba a wannan daren.
Koda ya kwanta bacci sam yaki zuwa masa inda ya cigaba da sakawa da warware wa har daga ƙarshe ya samo mafita inda yake fatan hakan ya kawo karshen duk wata kura da take shirin tasowa.

*

Please vote and comment. It means a lot. Thanks😘

NOORUL JANNAWhere stories live. Discover now