3

38 4 0
                                    

*🪂NADAMA🪂*

Zainab Habib(Mom Islam)

Elegant online writers

Follow me on wattpad

https://www.wattpad.com/user/Momislam2021?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Tabbas naji ƙorafinku akan kuɗin littafin yayi yawa ,inason ku sani bawai iya shi kaɗai zan dinga posting ba amma daga yau da gobe na bada bonus dominku ki turo 200 ki karanta hankali kwance ta wannan account ɗin 3175689751 Zainab Habibu first bank shedar biya ta wannan number 08141799224 idan kum kati ne ,zaki ɗauki hoton katin ki turomin in sambaɗaki a grp ƴan Niger kuyimin magana ta numberta.

Bismillahir rahmanir rahim.

_____________🆓P 3

Mamy wai saiki dinga bin abinda anty Anisa takeso bayan ita ba komai ke burgeta ba" Humaira ta faɗa tanfan zuwa makaranta dole Humaira ta tafi ita kaɗai ,
Ƙarfe ɗaya da rabi (1:30pm) mamy ta shiga ɗakin Anisa ta samu tayi wanka tana sanye da riga da wando wanda yayi mata kyau ,mamy tace "yaufa dadynku na hanya idan cikin ya lafa miki kizo mu shiga kitchen "cikin farinciki Anisa tace "naji sauƙi mamy muje " Mamy tayi mumishi suka wuce ,
Bayan sun gama haɗa masa shinkafa da miyar kifi wacce taji kayan ƙamshi suka gyara grin , Anisa na palo tana zaune taji mamy dake bedroom ɗinta tana waya tana cewa "wanne ne na sha da madara kuma wane ne zan dinga shafawa a fuska ,kai amma turaren nan yanada keyau har kyauta Abban Anee yayi min "Mamy ta tuntsire da dariya .
Anisa dake jinta taja tsaki mtsw kafin ta miƙe tabar gurin ,tana zuwa ɗakinta ta kifa kanta a bed tare da sakin kuka ,da sauri ta share hawayen tare da awowa palon cikin ƙwarin guwiwa kai tsaye ta wuce bedroom ɗin mamy , tana shiga ta sameta ta gama waya tana shirin jona chaji ta zauna gefenta kafin tace " mamy ina son aure !" a razane mamy ta kalleta kafin tace "Anee abin har ya girma haka ki kalli ƙwayar idona kice aure kikeso ?"Anisa ta sunkuyar da kai ,Mamy ta numfasa kafin tace "burunmu shine ki kammala karatunki ki kama aiki wanda zaki dogara dashi kina samun albashi mai tsoka ,daga wannan lokacin duk wanda kika kawo walahi inhar mun yaba da halinsa zamu aura miki shi " Anisa ta miƙe fuuu tabar mamy ba surutunta , sallamar dady da taji a palo ne ya sata fitowa da sauri tana cewa "Abban Anee surprise ne kuma yau ?"dady yayi murmishi ya riƙe hannun mamy suka wuce bedroom ɗinta , zama yayi a kan ɗaya daga cikin kujerun dake gurin ,mamy ta kawo masa ruwan sanyi tana masa sannu , cikin sauke ajiyar zuciya yace "yawaa ya naji gidan shiru ko suna makaranta ne ?"

Mamy ta ɗan taɓe baki kafin tace "Anisa dai yanzu tabar nan ,Humaira kuma tana makaranta "
Dady yayi murmushi kafin yace ",har yanzu ƙin makarantar tata yana nan kenan ?" mamy ta miƙe tana cewa "wanka zaka farayi ko abinci zakaci ?" dady yace "baki bani amsata ba "mamy tace "zan baka wanne zaka farayi ?dady yace "barinyi wanka sannan ".

Yana tafiya toilet mamy ta wuce kitchen dan haɗa masa abinci ,bayan ta kammala ta kawo ta ajiye kan table ta zauna tana jinjina maganar Anisa .
Bayan dady ya fito daga wanka ya shirya cikin shadda mai ruwan ƙasa ,ya zauna yana duba lokaci a wayarsa , ganin ƙarfe biyu har da mintuna ya sashi miƙewa yana cewa "mamy barinyj sallah ,
Daga nan ya wuce masallacin gidan da baya rabo da jama'a ,yana idar da sallahr bayan yayi adu'oinsa ya dawo gida ya zauna cin abinci ,
Ihun da suka jiyo ne yaja hankalinsu ,dady na cewa "kamar Anisa ?"mamy ta fice da gudu cikin tashin hankali ,tana zuwa ta sami anisa kwance tana riƙe da mararta hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarta ,a razane mamy ta ƙwalawa dady kira a halin yanzu ko numfashi batayi , dady ya shigo cikin saura yana tambayar wai meke damun Anisar ne ?" mamy kam baki ya kulle ta fara yi masa nuni da hannu alamar ya kama mata ita suje mota ,
Bayan ya kamata an sata a mota ,dady yayi driving ɗinsu zuwa asibitin Dr Zakari , suna isa aka wuce da ita emergency roon aka fara bata taimakon gaggawa , dady da mamy dake tsaye a harabar asibitin kowa ƙirjinsa na dukan 3 ,kiran da dr yayi musu ne yasa su katse tunaninsu suka nufi office da sauri .
Suna shiga dr ya miƙawa dady hannu kafin yace...!

Yanzu wasan ya fara

Ki biya 200 ki karanta  wannan garaɓasar daga gobe insha Allah zai koma kuɗinsa.
08141799224
Mom Islam

NADAMAWhere stories live. Discover now