*NADAMA*
*BONUS PAGE*
Garaɓasar samun littafin nadama akan naira ɗari biyu kacal .
Page 11&12
"Umma zan amince da duk abinda kike sona dashi ",Umma ta shafa kanta tare da sanya mata albarka.
Asalinsu Umma ƴan garin Maiduguri ne ,gudun hijira na faɗace -faɗacen da akeyi ne ya dawo dasu garin jos unguwar Dogon agogo , Tun bayan auransu da Alhaji Usman iyayen Umma wato Zainab suka rasu , Alhj Usman yana sana'ar jan doguwar mota yana kai kaya gari-gari , tun yanada mota ɗaya har Allah ya azurtashi da motoci har goma manya , da kuma wacce ya siya ƙarama ta hawa ,
Kwanci tashi yayi arziƙi na ban mamaki yaje makkah yakai mahaifiyarsa Amina makkah lokacin mahaifinsa ya rasu , akwai wani ɗan uwansa ana ce masa Abdullƙadir shima Alhji Usman ya kaishi makkah , daga nan yakai Hajya Amina makka , bayan ta dawo da wata bakwai Allah yayi mata rasuwa ,ƴaƴansu biyu da Ruqaiyya da Jamila, lokacin Ruqaiyya tayi aure da shekara ɗaya tana ɗauke da ciki wata takwas ,sunyi kuka da mutuwar mahaifinsu ,tun bayan rasuwar Alhj Usman Umma ta kama sana'ar kayan kitchen suna samun alkairi sosai ,
Kullu nafsun za'ikatul maut aranar wata Juma'a da safe da misalin ƙarfe goma dai-dai aka bugowa Umma waya jikin mahaifiyar Alhj Usman ya tashi , a hanzarce Umma ta fice da gudu mayafi kawai ta ɗauka kasancewarsu babu nisa , dana tafiya tana haɗawa da gudu kafin takai ƙofar gida ta hango mutane ana cike kowa yayi cirko -cirko , Umma na gani ta fashe da kuka kafin tace "shikenan suntafi babu manya " tana shiga ta samu anata salati masu kuka nayi ana hanasu ,Umma ta zauna a kan dakalin gidan tare da rafka tagumi tana tuno abubuwan da mahaifiyar mijin nata take yi mata na alkairi .
Batamayi kuka ba sai da taga an wuce d gawar a makara ta miƙe tana sumbatu ,dole aka riƙeta ,Ruqaiyya dake da tsohon ciki ta kalli Umma ta share nata hawayen abda tunowar da tayi Umma marainiya ce batada uwa batada uba ,kuma itakaɗai iyayenta suka haifa sai ƴan uwan iyayenta wasu ma ba lallai ta sansu ba .
Bayan anyi sadakar uku ya rage sai umma da Abdulƙadir wato ƙanin mijinta da ƴar uwar uwar mijin da Jamila ,sai da akayi sadakar bakwai sannan suka koma gida , Abdulƙadir yaci gaba da kula da dukiyar Alhj Usman cikin aminci ,duk ƙarshen wata yana sanya musu ribar da akace ya raba gida uku ya bawa Umma biyu ya ɗauki ɗaya .
Lokacin da cikin Ruƙaiyya ya cika wata tara da kwana goma ,a safiya Litinin naƙuda ta kamata , kasancewar ta kira Umma ,Umma ta tura mata Jamila wato Ummi ,
Daga baya itama ta tafi , Umma na sallama ta samu ƴan uwan mijin Ruqaiyya har sun ƙarɓi aihuwa kasancewar a gida ta aihu ta haifi yarinyarta mace kyakkyawa , sai da Umma tayi ƴar ƙaramar ƙwallah duk da aihuwar fari ce amma wani sa' in sukanyi wasa da dariya.
Cikin ikon Allah ranar suna yarinya taci suna Salma , taga gata da kayayyaki ta fannin Umma da dangin mijin sbda suna son Ruqaiyya sosai , har Umma ta tambayi wankan gida suka hana sabda zasu bata kulawa kamar inda Ummanta zata bata ,Umma tasan halinsu na kirki ta barmusu Ruqaiyya ,kwanci tashi asarar mai rai har sukayi ar'bain da kwana goma ,a ranar taje gidan Umma da goyon zuƙeƙiyar yainyarta wato Salma suna kiranta da Afnan , tanayin sallama Umma ta fito daga ɗaki ita da Ummi wato Jamila , suna mamakin kyau da ƙiba ga wani haske da Ruqaiyya tayi , suna shiga ɗaki Ummi tace "abamu sirrin Anty Ruqaiyya " Ruqaiyya na dariya ta kunto Afnan ta direta a cinyar Umma tare da zama kan ɗaya daga cikin kujerun , kasancewar ɗakin yana ɗauke da kujeru huɗu da mai zaman mutum biyu da kuma mai zaman mutum ɗaya guda biyu , Umma na kan mai zaman mutum biyu Ruqaiyya ta zauna a mai zaman mutum ɗaya , Ummi ma tana kan mai zaman mutum ɗaya .
Bayan sun gaisa aka shiga hira Ruqaiyya na faɗin irin alkairan da iyayen mijinta suka dinga mata Umma na godiya , ƙarfe 11:20 suka ɗora girkin shinkafa da miya wacce taji kifi da latas da cocumba da tumatur da albasa , bayan sun kammala aka zubowa Umma Ummi ta zubo musu itada Ruqaiyya , suka ajiye na dare a foodflaks babba .
Suna kammala ci akacigaba da hira har akayi azahar sukayi sallah , Abdulƙadir ya shigo ,kasancewar yau ya sauka a gari , ya shigo gidan Umma da sallama ,Umma ta fito tana faɗaɗa fara'arta kafin tace "muryarka bata ɓuya ,Abdulƙadir yayi dariya kafin yace" Umma kenan ashe kin kusa fita ?" cikin wani irin yanayi Umma tace "gobe ne " Abdulƙadir yace "Allah yayi masa rahama "ya ƙarasa cikin ɗakin hannunsa riƙe da bako har guda biyu ya ajiyesu a ɗakin Umma , Ruqaiyya da Ummi na ganinsa suka hau murna kowacce na ƙoƙarin gaishesu , bayan ya amsa da cewa "mai jego ya baby "Ruqaiyta tayi murmishi batace komai ba , Ummi ta ɗauko masa yarinya ta miƙa masa ,ya karɓa tare da kwararo mata adu'oi ya tofa mata , Ruqaiyya ta zubo masa abinci ta kawo masa ruwa , bayan yaci yayi hamdala ,ya buɗe bakin bako bag ya miƙowa Ruqaiyya ,kana ya kira Umma ya bata nata , Ruqaiyya ta buɗe nata ta fara ɗago atamfofi har kala huɗu masu tsadar gaske ga manshafawa da sabulai da rigar yarinya kala biyu ,har ƙasa ta durƙusa taje gabansa tana yi masa godiya.
Umma dake fito da nata kayan ta fashe da kuka tana cewa "Abdulƙadir ubangiji ya baka mata ta gari ya kareka daga dukkan sharri "Abdullƙadir da kansa ke sunkuya yana amsawa da Amin yace "Umma kome nayi miki ai ban faɗi ba ,duk daga cikin dukiyar yaya Usman ne kuma ke kika nunarmin da yin alkairi "
Umma kam bakinta ya rufe ,
Ya miƙe yana duba lokaci ƙarfe 3:12 pm har ya fita ya dawo da baya yana cewa "ah "ai na mance Ummi ga tsarabarki " Ummi taje da sauri taga kwalin wata Tecno mai maɓallai harda layi yayi mata rijista a ciki da memory , tsalle ta doka tana murna sosai ,kafin tayi masa godiya yayi musu sallama ya fice.
Umma tace "bansan dame zan sakawa Abdull ba .
Sai da Ruqaiyya tayi kwana biyar sannan ta koma gidan iyayen mijin suka mayar da ita gida.
Lokacin da Ummi ta gama secondry bataci gaba da makaranta ba ,kasancewar samari da suketa kai komo a kanta ga kuma Alhj Muntari dake kawo nashi harin dan har an turo da magabata ,
Cikin hukuncin ubangiji aka yanke dukiyar aure dangin mahaifinta bayan sun kawo kuɗin da sati biyar aka sanya rana wata ɗaya.
Kasancewar Umma nada tsuminta a ɓoye na tarin kayan kitchen dama tana siyarwa ,yasa yanzu take siyan abubuwan buƙata kamarsu zanin gado labulaye da sauransu ,
Kwanci tashi asarar mai rai biki ya rage saura sati uku , Umma babu zama koda wane lokaci tana busy ga wata mai gyaran jiki dake zuwa ana gyarawa Ummi kullum da tsumata da magunguna , a lokacin da bikin ya rage sati biyu wata ranar Lahadi ,Alhj Mintari yazo cikin shigarshi na manyan kaya ,wani lallausan yadi mai ruwan ƙasa ne a jikinsa sai sheƙi yake bugu da ƙari kuma mai tsadar gaske , jingina yayi a jikin motarsa daga bisani ya sanya hannyensa a cikin aljihu yana kallon ƙofar gidansu Ummi , Ummi dake zaune tana taya Umma tsintar shinkafa ,kasancewar babu inda Umman taje yau taji wayarta na ring , sunan my lovely ne ke yawo a fuskar wayar ta miƙe da gudu tayi ɗaki , tana shiga ta amsa tare da sallama , bayan ya amsa sallamar yace "gani a ƙofar gidanku " Ummi tace "okay ganinan fitowa " ta zura zumbulelen hijabinta ta fice ,kasancewar yanzu sun saba tunda yazo ba na ɗayaba kuma ba na biyu ba bayayin kwana uku bai zoba ,tana fita ta tarar dashi a jingine a jikin mota yayi nisa a tunani " ɗan tafi tayi masa a gefen fuskarsa kafin tace "bawan Allah tunanin me kake ?" Alhj Muntari yayi murmishi lokacin da idonsu ya sarƙe ana juna kafin yace , "ke nake tunani "wanda a zahiri ba hakan bane mahaifinsa kawai yake tunani .
Ummi tayi murmishi kana tace "yau naga fuskarka wani iri Allah dai yasa lafiya " Alhj yai murmishi ,sbda tuno maganar mahaifinsa yake ,da yace "ko bayan babu raina idan kayi aure karka wulaƙanta mahaifiyarka , murmishi Muntari yayi ya buɗe mata mota ta shiga ya shiga shima ya fara driving ,yau ta gansa ba kamar inda suka saba ba suyita tsokanar junansu dan haka tayi shiru ,har suka iso wani ahalan wa sahalan na cikin garin Jos wato inda ake siyarda wayoyi , parking taga yayi ya fita tare da shiga shagon waya ,sai gashi ya fito da leda a hannunsa bayan gani da tayi ya miƙa ATM ɗinsa , yana dawowa ya buɗe gefenta ya ɗora mata a hannunta ya rufe ya zagaya mazauninsa na driver ya zauna ya rufe tare da jansu suka nufo hanyar gida,
Buɗe ledar tayi taga kwalin waya ta duba sunan Spark2 ce ƴar madai-daiciya , ta haɗe hannayenta biyu tayi masa godiya , Alhj Muntari yayi murmishi kafin yace "karki damu tawan ".
Kwanci tashi asarar mai rai yau ta kama Laraba ,Alhj Muntari ya turo mata da 70k ta acct ɗin Umma sbda tayi hidimar biki , yau akeyin Hausa day ,akayi faten tsaki aka rarraba su goruba taura magarya , ansha rawa ,ƙasancewar ba wasu yawaitar ƙawayene da ita ba yawanci ƴan uwane suka zo mata .
Washe Alhamis akayi fulani day ,sukayi rawar fulani da shiga irin tasu , aka raba fura da nono
Ranar Juma'a kuma akayi wa'azi a cikin gidan nasu inda akayi wa'azin akan biyayya da haƙuri da kawaici da kumabiyayya.
Ranar Asabar basuyi komai ba anata shiriya amarya kasancewar ranar ne ɗaurin aure ,
Ummi na can gidan Ruqaiyya anata shiryata ,wow hangota nayi tana sanye da leshi ruwan coffee an yane mata kai da milk color ɗin gwaggwaro tayi kyau sosai ,an yafa mata ɗan ƙaramin mayafi a kafaɗa.
Ƙarfe 2:10 dai-dai dubban mutane suka sheda ɗaurin auran Jamila (Ummi) Musa da Muntari (Usman ) lakadan ba ajalan ba ,
Ɗaurin auran daya sami halartar manyan abokan marigayi mahaifin Muntari da abokan Muntari da abokan mahaifin Ummi da abokan Abdulƙadir , masha Allah sunsha Adu'oi daga mutane da yawa .....!Domin samun cigaban labarin ki tunuɓi 08141799224.
MOM ISLAM
YOU ARE READING
NADAMA
RomanceBurina bai wuce ace gani a gidan mijina ba ,iyayena sun kasa gane farincikina da baƙin cikina.