*🪂NADAMA🪂*
Zainab Habib(Mom Islam)
Elegant online writers
Follow me on wattpad
https://www.wattpad.com/user/Momislam2021?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
Tabbas naji ƙorafinku akan kuɗin littafin yayi yawa ,inason ku sani bawai iya shi kaɗai zan dinga posting ba amma daga yau da gobe na bada bonus dominku ki turo 200 ki karanta hankali kwance ta wannan account ɗin 3175689751 Zainab Habibu first bank shedar biya ta wannan number 08141799224 idan kum kati ne ,zaki ɗauki hoton katin ki turomin in sambaɗaki a grp ƴan Niger kuyimin magana ta numberta.
____________________🆓P5
A ɓangaren Anisa kuwa tanason dady na tafiya gobe ta kaiwa Salim ziyara.
Da misalin ƙarfe 5:pm Humaira ta shigo ɗakin Anisa , samunta tayi tana bacci ,ta zauna a gefen gado kafin ta fara kiran sunanta Anty Anisa, Anty Anisa ,firgit Anisa ta tashi daga baccin datasamu ya ɗauketa daƙyar cikin fara tace ",Humaira bansan lokacin da zaki girma ba ,har sau nawa zance kidena tashina idan na bacci ko kin mance ne ? Humaira tace "am sorry anty dama dady ne yace "wai ki fito muje gidan hajiya " Anisa tace "ke ni babu inda zani ki tafi ki bani guri " Humaira tace "Anty Anisa kinga tulin kayan da dady ya nuna mana a waya kuwa ?wallahi yace "daganan zamu taho dasu duk suna gidan hajiya " Anisa tayi tsaki mtsw kafin tace "ki zaɓo hardani cikina na ciwo ".
Humaira kam dole ta koma ta sanarwa su dady ,mamy tace "amma kaima ka mance Anisa ne batason zuwa anguwa ko kaɗan "dady yace "ku ƙyaleta tunda kun shirya muje " mamy ta tafi ɗakin Anisa ta sameta a kwance tayi ruf da ciki ,ta girgiza kai kafin tace "Anisa "
Anisa ta juyo tayi kamar irin ciwon cikinta ya tashi tana nishi tace "mamy cikina ni bazan iya zuwa ba " cikin tausayawa mamy tace "Allah ya baki lafiya , sai mun dawo " Anisa tace "tom ".
5:20 Mamy da dady da Humaira suka fita a motarsa , kai tsaye suka wuce gidan hajiya tudun wada , sunyi tafiya mai nisa kafin suka iso gidan ,dady yayi parking a ƙofar gida kasancewar mota bazata shiga gidan ba .
Suka shiga dukkansu da sallama a bakinsu , Hajiya dake cikin ɗaki tana shara ta fito tana amsa sallamar tana faɗaɗa fara'arta , cikin zolaya Humaira tace "walhi hajiya bakya gajiya da aiki jibi gida kamar an lashe tsabar ƙalƙala " hajya ta kamo hannun Humaira tana cewa "ah Jamila ku shiga man ,su dady suka shiga ,Humaira ta taya Hajiya haɗa musu lemu ta kawo musu gabansu bayan ta janyo musu tebur.
Shugowa Hajiya tayi hannunta riƙe da kular abinci ta ajiye musu ta koma ta ɗauko plet da cokali ta ajiye a gabansu kafin ta zauna tana cewa to ina yuninku " Dady ya sauko ƙasa ya gaishe ta hakama mamy ta sauƙo ta gaisheta daga nan suka ɓarke da hira .
A ɓangaren Anisa kuwa , su mamy na tafiya ko anguwar basu bari ba ta miƙe da sauri ta shiga wanka ,tana fitowa ta shafe jikinta da mai mai ƙamshi kana ta kawo zafafan turaruka masu ƙamshi wanda dady ke siya mata duk ƙarshen wata , ta feshe jikinta dasu kasancewarta gwana gurin tsara kwalliya yasa tayi kyau sosai , ta buɗe drowa ta ɗauko riga da wando ,rigar fara wandon baƙi ta kawo after dress tasa baƙa a sama , tayi rolling kanta da farin ɗankwali , tayi kyau matuƙa ta kuma feshe jikinta da turare ,ta ɗauki wayarta da hand bag ɗinta ta fice tare da buɗe get bata jira driver ba sbda batason kowa yasan ta fita , a ƙofar gidansu ta danna number Salim ,cikin sa'a ya ɗaga kafin yace ",baby jikinne ?" Anisa tace "albishirinka " Salima yace "goro fari tass "Anisa tace "gani nan zuwa yanzu su dady sun fice ,amma ina gaisheka zan dawo kar su samu na fita "cikin rawar jiki Salim yace "aiko nagode barin fara rawa ,ta kashe wayar .
Da sauri yahau gyara ɗakinsa tare da tanadar abubuwan da yasan yanada buƙata ,kai tsaye yaje wani chemist ɗin abokinsa ya karɓo wani magani wanda tuni sunyi maganarsa ,ya dawo ya buɗe 5alive yasa a ciki ya girgiza , cikin ƙanƙanin lokaci ya gama gyara komai harda wanka yayi ya sauya kaya ya zauna zaman jiranta .
Kiran da yaji ne yasashi ɗagawa yace "kina dai-dai ina ?" Anisa tace "ai gani a ƙofar gidanka " Salim ya tashi zaune dan ji yake kamar a mafarki ,ya sanya takalmansa ya fice yaje tarbota .
Suna isowa ya nuna mata kujera mai zaman mutum biyu ,bayan ta zauna ya cika mata gabanta da kayan ciye-ciye kafin yace ...!08141799224
Mom Islam
YOU ARE READING
NADAMA
RomanceBurina bai wuce ace gani a gidan mijina ba ,iyayena sun kasa gane farincikina da baƙin cikina.