*_JINKIRIN AURE_*
*_Ƙalubale ga ƴammata_**By*
*Oum Hairan*
*Dedicated to*
Dr. Mass @gadas son so for ever.*Free P 3-4*
_Normal 300 VIP 600 PC 1k acct details 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank._
Tashi tayi ta nufi ɗakinta ta cire kayanta ta nufi bayi ta watsa ruwa tayi alwala tayi sallar magrib ta zauna tana karatun Kur'ani tana sharar hawaye, a wannan yanayi taji an buɗe ƙofar dakin nata an shigo an nemi guri an zauna bata ɗago ba Saida takai aya sannan ta rufe Kur'anin ta shafa addu'arta ta juyo tare dayin kasa da muryarta cikin girmamawa tace “Yaya Mus'ab kaine a daren nan ga gari yanata cida alamun ruwa zai sauka"
Fasali yaja yana cire hularsa yace “To ya zanyi Madinah kece kinƙi barinmu mu huta Baffa Sunusi ne yaje ya dameni da maganar aurenki da Khamal kuma yacemin lallai kafin azumin bana sukeson ayi komi a gama shiyasa nazo naji meye kike ganin zai yuwu?"Tunda ya fara maganar take kallonsa tana girgiza kai batare da ta katseshi ba har ya gama sannan tace “Yanzu Yaya Mus'ab wannan shirmen maganar har takai ka hana kanka kwanciya cikin iyalinka ka fito da wannan tsohon daren?"
Murmushi yayi yace “Kullum ke raayinki bambam yakesha da mutane Ni abinda yasa naga dacewar nazo mu tattauna naga ba duka abinda rai keso take samu ba musamman a wannan bigiran Madinah kinsani ni bana cikin mutanen da zasu kawo Miki mafita domin cutarwa a gareki, nayi ɗawainiya da rayuwarki tun yarinta kawo lokacin da kika zama mutum kike iya yiwa kanki abubuwa da suka shafi rayuwarki.
Inason ki tsaya ki ɗauko hankalinki ki tattarashi waje guda ki duba yanda rayuwar take tafiya kiyi hƙr ki karɓi wannan zaɓin kiyi addu'a wata ƙila shine alkhairin daya hana wani zuwa ke kuma kikaƙi karbarsa tun kina ƙarama"Idanunta ta ɗago daya ciko da kwalla tace “Shikenan ashe dama idan Allah ya jarabci bawa da wata ƙaddara saiya manta da faɗin ma'aiki (S.A.W) da yake horonmu da mu zaɓawa ƴaƴanmu iyaye na kwarai, Yaya Mus'ab wanne ɓangare zan nuna idan na karɓi Khamal a matsayin miji nace shine alfahari na? Please Yaya Mus'ab na rokeka a matsayinka na gatan daka tsayawa rayuwata kayiwa girman Allah ka shigemin gaba wajen bijirewa auren Khamal baiyimin ba bayan haka Nima banyi masa ba Yaya Mus'ab abinda Khamal yake faɗa min kullum shine shifa duk da lalacewarsa yanaji a ransa taimakona zaiyi idan ya aureni saboda naje na zubar da darajata irin mazan da nakeso na tsaya ruwan idanu nayi musu tsufa bazasu iya aurena ba Yaya Mus'ab kullum haka yake faɗamin Ni ban kalleshi da aibinsa ba sai shine yake cusguna min da naƙasun da bani nayiwa kaina ba...."
Ɗaganta hannu Yaya Mus'ab yayi yace “Shikenan ya isa Madinah Allah yayi zaɓi na alkhairi yanzu ya batun komawarki karatun? Dr Shafi'u abokina yace akwai wata jami'a a Rasha da suke bada horo na musamman akan duk wata matsala data shafi ƙwaƙwalwa to ke kuma naga kinada interested akan wannan ɓangare shiyasa nace zanyi Miki magana ko zakije ki ƙara samun gogewa"
Ƴar ƙaramar dariya tayi tace “Shiyasa nake sonka Yayana duk abinda da zai kawowa rayuwata haske shine burinka Yaya Mus'ab Allah yaja kwana ya ƙara arziki, ka bincika min shi abinda tafiyar zataci da inason na biya kudin aikin hajji amma tunda hakane bari na tura gaba tunda dai Ammi tayi Ni daga baya naje nayi, Yaya nifa Research kawai akan abinda ya shafi brain yana mugun sani nishaɗi"
Dariya Mus'ab yayi yace “Autar Ammi kenan waye zaiƙi farin cikin Ammi ai dole mu ƙarfafa Miki gwiwa munyi waya ma da Khamis shima ya bada goyon baya Salees ne dai da Aminu suke ƙorafin wai mune mukeja ake zaginmu ana cewa mun ɗaure Miki gindi kina yawo da sunan karatu ni wani lokacin gwiwata har sanyi takeyi"Kwantar da kanta tayi jikin bedside tace “kuyi hƙr No condition is permanent Ya Mus'ab wata rana sai labari Allah shaida ne bana aikata abinda mutane suke zargina dashi Yaya duk wata mace da wannan ƙaddarar ta faɗa mata dama sociaty dinmu kallon ƴar iska gantalalliya watsattsa sukeyi mata hatta da Allah ya hukunta zai aureta bayajin a ransa budurwa zai aura, nifa da wannan surutun da nakeja muku wlh ko za'a bani sadakin bazawara indai nagartar mijin takai gara na karɓa indai yayi albarka Shikenan"
Murmushi yayi ya miƙe cike da tausayin ƙanwar tasa yace “Insha Allahu komai zai wucce ki kwanta goma ta wucce gashi gobe talata" fatan alkhairi tayi masa ya fice tare da ja mata ƙofar ta miƙe tayi mata key ta shiga bayi ta dauro alwata ta kwanta daidai lokacin da aka kece da wani ruwa me ƙarfi ta kunna MP tana sauraron ƙira'a tare da tsunduma duniyar tunanin rayuwar baya.
Kamar yanda ta saba yauma ganin zata raba dare bacci yakasa ɗaukarta tana hasaso lkcn da zata kwanta kusa da mijinta ta tayi matashin kai da ƙirjinsa ta shafa sumarsa taja gemunsa, wannan rana ji takeyi dama zata iya kissimo irin nishaɗin da zata kasance dama tazo mata nan kusa dama zata buɗe idanu taga ba ita ce Madinan da abu ɗaya ya zamewa tsaiko cikin rayuwarta ba.To wai meyene abinda ya zame mata katanga da samun abokin rayuwa ne? Tambayar da kullum takewa kanta da makusantanta kenan amma ta kasa samun amsa saidai ace mata tayi hƙr lokaci ne idan ta hƙr ta cire komai a ranta kuma sune waɗanda zasu fara cewa da ita “Madinah wai yaushe zakiyi aure ne?" Wannan tambaya tana dagula lissafin ta da ace mutanen duniya zasusan ƙuncin da take shiga a dalilin wannan tambaya da sun daina yi mata ita.
Zuwa yanzu abubuwa sun fara yi mata nauyi sha'awar kasancewa da namiji abokin ɗebe kewa tana yawan bijiro mata takan raba tsayin dare bata iya bacci ba saboda ciwon mara idan abin ya ta'azzara har fita takeyi daga hayyacinta sai likita ya tsaya a kanta sannan take dawowa daidai.
Sai bayan sallar asuba sannan ta koma ta kwanta bacci me nauyi ya dauketa dake yau ba itane da dutyn safe ba tanada isasshen lokacin bacci ba ita ta farka ba sai 12:21pm ta farka shima tashinta akayi ta buɗe idanunta kan Ƙawar tata kuma abokiyar aikinta Dr. Zahira murmushi sukayiwa juna Zahira tace “Tunda nayita kiran wayar ki najita a kashe nasan kinanan kina sana'ar saiki tashi mu fita inaso zaki rakani unguwa"Miƙa tayi tare da salati ta diro a katifar Zahira tabita da kallo tana cewa “Kaga manyan mata masu manyan kaya matan me rabo wato Dr. Komanki abin sone ga kowanne lafiyayyen namiji wlh Ni kaina da nake mace halittarki na birgeni an baje fasaha wajen ƙeraki ke gani kin zamewa mazaje ƙwalele ya Allah karka kasheni sai naga wannan me rabo da zai huta da jikin nan"
“Amin ta amsa dashi tana shigewa bathroom ta sakarwa kanta ruwa ta sulla wankanta ta ɗauro towel ta fito ta tsaya jikin mirror tana shafa ta bata kusan rabin awa wajen shafa mai fesa turare gyara gira sannan ta koma ta ɗauki wata baƙar atamfa tasa abinka da kyakkyawar nandanan ta ƙara wani kyau na musamman ta ɗauki mayafi Milk kalar zanen jikin atamfar da takalminta da jakarta duk kalar mayafin ne ta dauki system nata da wayoyinta suka fice.
A tsakar gida suka ishe Ammi tana gyaran ƙumba ta dubesu tace “Ai dake kece kinga ta fito Zahira ni tun asuba rabona da Munau tanacan tana sana'ar bacci kamar kasa" dariya tayi har Saida dimpli ɗinta ya lotsa tace “Ayyah Ammi wlh banyi bacci da wuri ba jiya don Ni a yanda na kwanta ma sai biyu zan fita a gdannan to wannan uwar ƙwarzabar tazo ta tasheni wai zataje unguwa kuma saina rakata"Tsugunnawa tayi tace “Ammi na tuba wlh na horu a taimakeni da key ɗin motar Allah bazan kuma bige kowa ba" harararta tayi zatayi magana tace “Wlh Ammi tsautsayi ne bazan kuma ba da abin hawan kafi kwarjini kinsan yanayin aikin mu....."
Cilla mata mukullin tayi tana cewa “Yar ƙaniya jeki nikam Allah nunamin ranar aurenku na daina ganinku kuna shigemin gaba" addu'a ce Ammi tayi amma Saida ta sanyaya mata jiki, har suka isa kango jikin gidan nasu dake dama tun jiya tace da maigadin ya wanke mata motar shiga kawai sukayi ta sallameshi suka fice suka dauki hanyar asibitin da suke aiki.
Dr. Zahira ce ta kawar da shirun da cewa “Na fahimci kinsa damuwa kwana biyu a ranki Dr. Meye yasa Ni da nake bazawara bana damuwa kamar yanda kike damun kanki?" Dr. Madinah akwai arhar hawaye nandanan suka shiga zarya a idanunta ta buɗe ƙaramin bakinta tace “Saboda ke kin taɓa yi kinada yaranki ko yanzu kika mutu kinada masu ɗaga hannu suce Allah ya jiƙan Umman mu Dr. Ni banyi ba banida kowa sai Ammi, kwana biyun nan ta matsa da maganar aurena sai nakejin dama zan iya aurar kaina kodan na faranta zuciyar mahaifiyata"
Cikin tausayawa Dr. Zahira tace “Dole zata damu Dr. Ko kinsan yanzu a unguwar nan taku shafinki aka buɗe jiya Husain ƙanina yazo yake cemin wai ke meye ya hanaki aure ne? Na dubeshi da mamaki shine yake cemin yaji a majalissar Bala me Youghut anata zaginki wai karuwanci kikeyi har wani dillali yana cewa shi yama taɓa kaiki gurin wani mai gidansa....."
YOU ARE READING
JINKIRIN AURE
RomanceRayuwar wata budurwa kyakkyawa kuma yar boko wacce ta samu shahadar zama Consultant a ɓangaren kwakwalwa amma kash! abu ɗaya ya zame mata tarnaƙi ga rayuwarta, ba komai bane abinnan face mijin aure daya gagareta samu.