JINKIRIN AURE!!!

511 11 0
                                    

*_JINKIRIN AURE_*
*_(Ƙalubale ga ƴammata)_*

*By*

*Oum Hairan*

*Dedicated to*
Dr. Mass @gadas son so for ever.

*Free P 5-6*

_Normal 300 VIP 600 PC 1k acct details 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank. Shaidar payment ta wannan number 09013718241_


Murmushi takeyi wanda da ka gansa kasan na ciwo ne irin wadannan ƙananun sharrikan suna damunta amma yanzu sun rage yi mata zugi a zuciya ta saduda tunda ita dai ta tabbatar da bata taɓa aikata abinda mutane suke kallonta dashi ba, ta sani Allah zai wanketa tsaf idan lokacin wankewar yayi.
Da wannan suka isa sukayi parking bata iya cewa komai ba suka fito kowacce ta wucce office ɗinta da wuri tayi ƴan aikace-aikacenta ta sallami petiant ɗinta yawanci duk waɗanda zasu ƙara karɓar magani ne da kuma ganin yanayin jiki dake azumi ta ɗauka yau ɗin sai uku ta fito daga nata office ɗin ita dama Dr. Zahira ta jima da tashi a aiki suka kuma ficewa, lalle sukaje da kitso Zahira aka yima kitso Madinah ba ma'abociyar kitso bace tafi ganewa ta gyara sumarta ta daure dake Allah yayi mata baiwar sumar.


Biyar suka ɗauki hanya wannan karon Zahira ke jan motar suka shiga unguwannin cikin gari ƙofar nasarawa sukaje wani gida Zahira ce ta kira wata number bugu biyu aka ɗaga suka gaisa ta sanar dashi suna ƙofar gidan yayi musu izinin shiga Madinah na mita tana cewa ta gaji da yawon zuwa gurin ƴan tsubbu da Zahira ke sata ita ta barta taji da damuwarta basai ta ƙara mata wata ba.
Da wannan suka shiga cikin gidan a aljihun zauren suka ishe babban mutumin malami ne babba da tarin littafai a gabansa yana duba wani littafi a hannunsa ya dago ya amsa sallamarsu tare da nuna musu gurin zama suka zauna da gaisawa Zahira ta fara yi masa bayani tace “Mal wannan ita ce Dr. Madinah wacce jiya na fara baka labari wato Mal wani abune me bam mamaki da ɗaure kai yake faruwa nikam abin yana bani mamaki matuƙa, Mal babu muni babu matsalar tarbiyya babu jahilci babu gigita ta talauci amma rayuwar taƙi tayi haske kullum cikin damuwa take hatta Ni kaina abin ya fara sani a damuwa, Mal mijin aure ya gagara ga Dr. Madinah gashi shekaru har sun fara nauyi kullum abu sai ƙara nisa yakeyi Ni raina ya fara faɗamin anya babu sa hannu ko na mutum ko na shaiɗanu?"


Zubawa Dr. Idanu yayi kanta na ƙasa tana wasa da yatsunta can ya numfasa yace “Allah ya shiga lamarin Madinah" shiru ta tsawaita can ya dago yace “Babu matsalar jinnu cikin lamarin nan kuma babu sa hannun kowa Madinah kawai lokacine baiyi ba amma insha Allahu zamu duƙufa tayaki addu'a Allah ya jinkirta zama ya kawo abokin rayuwa na kwarai yanzu abinda nakeso daku ga wata addu'a da zan baki yau daren Laraba ƙarfe biyu ki tashi kiyi alwala kiyi sallah raka'a huɗu kowacce ki karanta mata fatiha ƙafa ɗaya da kulhuwallahu 40 kowacce raka'a har ki idar kiyi istigfari adadin 100 kiyi salatin annabi ƙafa ɗari shima kina me tawassali ga Annabi Muhammad (S.A.W) bayan kin gama ki faɗi bukatar ki ta zaɓin miji na kwarai abin alfaharin kowacce mace sai ki rufe da istigfari 100 salati 100 saiki tashi ki koma ki kwanta kiyi haka na tsayin kwanaki bakwai bijahi Rasulullah sai Allah ya waiwayi lamarinki domin kin haɗa shi da wanda bazai iya juya baya ga bukatar wanda yaje masa dashi ba wato Muhammadur Rasulullah, Madinah idan kinyi haka duk abinda alƙibla ta nuna to dole ki karɓe shi koda kuwa ɗan uwan naki Khamalu ne idan kuma akasinshi ne to dama fatan da mukeyi kenan, aje a dage Allah zai duba buƙata"


Gdy tayi masa sosai suka ajiye masa sadakar Naira dubu goma suka tafi hakanan taji malamin ya kwanta mata domin a kalaminsa akwai tawali'u sosai cikin lamarinsa, suna tafe ne tafiya irin ta kurame can Madinah tace “Dole zan bar ƙasar nan cikin yan kwanaki Dr. Saurin cin birki tayi tace “What happen Dr. Madinah da zakice zakibar ƙasa bayan kinsan yanayin da muke ciki yanzun?"  Numfashi ta sauke tace.
“Shine dalilin da zaisa nabar ƙasar Dr. Zahira yau ina zaune a office Baba Sunusi ya kirani zagin da yayimin akan nace banada ra'ayin aure da Khamal ko karen gidansa baitaɓa waba har yana kirana ƴar matsiyata taka hayen arziki......" Kukane yaci ƙarfinta ta rushe da kuka tace “Wai meye laifina ne da Alƙasim ya haifeni da Adiyyah? Dubanta Zahira tayi tace.
“Na dade da fahimtar family ɗinku kuna rayuwa a cikinsu ne kawai amma basa kaunarku Dr. Don Allah yau dai ki bani labarinki ko a takaice ne wala Allah ta yiwu inada rawar takawa Dr tun muna school of nursing na fahimci halin da kuke ciki amma abin baiyi tsamari irin yanzu ba don Allah Please Dr. Ba'a ɓoyewa abokin kuka mutuwa"


JINKIRIN AUREWhere stories live. Discover now