JINKIRIN AURE!!!

776 15 6
                                    

17-18

_Kiji tsoron Allah karki karanta baki biya ki biya ta wannan asusun 300 VIP 600 PC 1k domin jin yanda wannan littafi zai kaya sis abari ya hucce shike kawo rabon wani in baki fara ba ki fara yau JINKIRIN AURE ƙalubale ne dake ciwa al'umma tuwo a ƙwarya_
_Nrml 300 PC 1k acct details 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank ko 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko kati MTN ta wannan number 09013718241, Yan Niger zaku turo katin Airtel na 500cf shaidar payment direct Link👇🏼_

https://wa.me/message/LFSVQWEXOXAHF1



Bansan tsayin lokacin dana ɗauka zaune a gurin nan ba Saida naji an buɗe office ɗina an shigo shima ba shigowar naji ba ƙarar dukan table ne ya dawo dani hayyaci na dago idanuna da suka kaɗa sukayi jawur tare da cije leɓe na ganin me shigowar yana nufoni yasani saurin miƙewa na nunashi da yatsa sai naga ya tsaya shima jikinsa na rawa da murya me nuna alamun tashin hankalinsa yacemin "Ya akayi kikayi mana video jiya har kika fitar dashi......."
Bansan inada fushi ba sai ranar Allah ɗaya bansan lokacin dana ɗauke Hamma Hussain da wani nagartaccen mari da ya sanyashi dafe kunci ba, cikin kuka nace masa "Azzalumi mayaudari dama shirinka kenan akan rayuwata shiyasa kaketa bibiyata ashe jiran damar da zaka canzamin lissafin rayuwa kakeyi Hussain ni ka tallatawa surata a duniya saboda cin mutumci da tozarci akan abinda bantaɓa nema ba bantaɓa aikatawa ba Hamma meye nayi maka daka zaɓi fitar da bad video na....."
Rufemin baki yayi da hannunsa jikinsa har yanzun rawa yake yi na tureshi nace "Karkace min komai ɗon girman Allah kaje kawai Allah ya bimin haƙƙina ya sakamin wannan tozarcin daka shirya yimin"
Ina faɗin haka na zari jakata da key na nayi waje ya biyoni yana kwalamin kira banko bi takansa ba bare na saurareshi nayi ma motata key na fice da mugun gudu na nufi get ɗin maigadin ya buɗe min cike da mamakin yanda nakejan motar a fusace.


Gida na nufa dama dai ikon Allah ke kare bawa amma kariyar ranar ta musamman ce, inayin parking na kifa kaina a sitiyarin na rushe da wani kuka me dukan zuciyar makusanci banji sanda aka buɗe ƙofar ba saiji nayi ansa hannu an ɗago fuskata yasa hannu ya sharemin hawayen yana girgizamin kai yace "Ɓingel ya akayi haka?" Da sauri na ɗago ina ja baya ina kaɗa masa kai yayi saurin damƙar hannu na yace "Please Lovely sis baa ɓoyewa abokin kuka mutuwa kuma ko kowa yaƙi fahimtarki nikam zan fahimceki garin yaya haka ta faru videonki nata yawo tsakanin wayoyin dangi harma suna iƙirarin fitar dashi duniya muddin baki yarda da ƙudurinsu ba?"
Sai yanzu na samu damar furuci na buɗe bakina Harshena na sarƙewa na zayyane masa komai yaja gwauron numfashi yace "Allah shine kawai zai fitar dake Hussain yayi kuskure kuma ya ha'ince ke Madinah koda ace da yardarki hakan ta faru bai kamata yayi Miki video har yayi sakacin da videon zai tantsama duniya ba, yanzu dai karki shiga gdannan saboda Ammi nakan tsini wlh duk wani bayani daya kamata nayi mata nayi mata taƙi fahimta muje na kaiki gdansu Ja'afar ki zauna tare da Mamansu duk yanda zanyi sanyi na haɗo Miki komanki kiyi tafiyarki Faransa ki barmu da Ammi zamuji da ita"
Ɗagowa nayi ina ƙoƙarin dakatar da kukana nace "Bazan iya tafiya bansan matsaya ta a gun Ammi ba Hamma Mus'ab....." A fusace yace dole saikin tafi domin kuwa hakan shine kawai zaisa komai ya batare da rai ya ɓaci ba"


Naso gardamewa kafiyar Yaya Mus'ab yasa na amince ya kaini gidansu abokinsa dake Inna Saude tasanni bamu samu matsala ba ta rinƙa bani kulawa har zuwa dare wajen Goma Yaya Mus'ab ya kawomin trolly na kayana dana haɗa da sauran tarkace na na killace washegari raina babu daɗi haka Dr. Kaltingo ya kirani yazo ya ɗaukeni shida Yaya Mus'ab suka kaini Airport Saida suka jira tashinmu ina kuka ina ɗagawa ɗan uwana hannu karon farko da zanyi tafiya me nisa a rayuwata bantaɓa zuwa ko Niger ba iyakar yawona a cikin gidane Nigeria sai gashin zan sauka a birnin Rum da sunan karatu tabbas wannan wani Babban ƙalubale ne daya farmaki rayuwata dole nasan irin naɗin da zanyi don ɗaukar cece-kucen sociaty ɗina.
Ƙasar France ƙasace me ban sha'awa da burge idanu gani na fara fuskantar hakan ne tun daga Airport ashe abin na gaske ne ko anan ɗin ma motar WHO ce tazo ta daukemu ukune Ni kaɗai ce mace kuma bahaushiya a cikinsu ɗayan Ucche yazo daga Ogun Dayan kuma yazo daga Benue, aka kaimu masauki kowa aka damƙa masa key na dakinsa a hotel ɗin da aka saukemu.


You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 19, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

JINKIRIN AUREWhere stories live. Discover now