*_JINKIRIN AURE_*
*_(Ƙalubale ga ƴammata)_**By*
*Oum Hairan*
*Dedicated to*
Dr. Mass @gadas son so for ever.*Free P 9-10*
_Normal 300 VIP 600 PC 1k acct details 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank. Shaidar payment ta wannan Link ɗin👇🏼._
https://wa.me/message/LFSVQWEXOXAHF1Tsalle nayi na faɗa jikin Hamma Hussain ina dariya ya ɗagani muka fita duk da shekaruna sun fara nauyi ina da kusan 15 years Amma har yanzu ban girma da ɗauka gurin Hamma Hussain ba baya gajiya da hidima dani baya gajiya da wahaltamin baya gajiya da jiɓantar al'amura na.
Muna rayuwa da taimakon Ubangiji dayake kawo mana ɗauki cikin nasara Yaya Mus'ab ya samu aikin campany ya fara shikuma Yaya Salees yaci gaba da buga-bugarsa shine acaɓa shine kwandastan mota ita kuma Ammi takanyi funkaso da safe da rana kuma tayi lemon ginger da kunun aya haka Allah ya rinƙa tallafarmu munaci gaba da rayuwa cikin ƙaramin yanayi Ni da yayye ba biyu muna karatunmu wani lokacin kudin school fees ɗinma sai anyi kamar anayi kafin asamu a biya.
Zahira a mafi yawan lokuta ma Hamma Hussain shine yake biyamin kuɗin makarantar, shekarata sha bakwai na gama secondary A wannan lokaci idan kika kalleni zakice nayi shekaru ashirin da biyu saboda cikar zati na da halitta ta.Tabbas na amince Zahira ni babbar yarinya ce matar manya a hankali mukayi wata shaƙuwa da ta rinƙa rikiɗa tana zama soyayya amma a ɓangaren Hamma Hussain nikam bantaɓa jin so na soyayya tsakanina da Hamma ba saidai kawai nasan duk cikin ƴan uwana inajin Hamma Hussain a raina fiye da kowa.
Lokaci da zamuyi candy Hamma Hussain ya kashemin kudi bana wasa ba domin a lokacin ya gama karatunsa dake zuwa wannan gaɓa Allah ya ɗaga mahaifinsa da Baffa Sunusi sun shiga harkar siyasa gadan-gadan wannan tasa baisha wahalar samun aiki ba, kuma baya ƙyashin kashemin ko nawa ne ga Yaya Mus'ab shima komai ya samo Deenah komai ya shigo hannunsa nawa ne wannan tasa na zama ƴar gata abu guda ɗaya yanzu daya kutso cikin rayuwa shine masifar son karatun likitanci kamar yanda naci buri itakuma Ammi tunda na taso taga yanda nake girma kamar kazar gidan gona bata da burin daya wucce taga ta auradda Ni.Muna zaman jiran jarabawa Kusanci na da Hamma Hussain yana ƙara ƙarfi duk dangi kowa yana kallon mu matsayin masoya Mal Buba shine ya shiga cikin maganar dakansa yasa aka kira Baffa Nuhu akan maganata da Hussein tashin farko abinda Baffa Nuhu yace ya girgiza Ammi na sanda taji wai Baffa Nuhu ne yace shi indai shine ya haifi Husain to bai amince masa aure na ba harma da ƙarin cewa shi ai baima yarda muɗin halattatun ƴaƴa bane don har Ethiopia yaje ba'a nuna masa limamin daya ɗaura mawa Baffanmu da Ammi aure ba.
Tun daga wannan lokaci aka jingine maganar auren to dama dake ba wani damuna maganar tayi ba haka naci gaba da harkokina ranar da jarabawarmu ta fito Hamma Hussain ne yaje ya dubo min yazo da murnarsa jarabawa tayi kyau na samu duk abinda ake buƙata ranar Ya Mus'ab har goyani yayi saboda murna ya tsugunna gabana yace “Uktee me kikeso yanzu bayan fitowar jarabawarki?" A dan ɗarare saboda Ammi bata bani da sauƙi idan nace mata karatu nakeso nace masa.
“Hamma Mus'ab don Allah kar ku watsawa muradina ƙasa kune kukace shine burin Baffanmu akaina koda baya raye zaku iya cika masa burinsa, inason nayi karatu burina shine na zama likitar ƙwaƙwalwa please Ya Mus'ab....."
Ɗaukeni naji anyi da marin da Saida bakina ya fashe Ammi tace “Karatun ubanki zakiyi Munau Ni kwadantaki zanyi inci da zansaki a gaba in kalla Mus'ab na faɗa maka ka daina biyewa shirmen yarinyar nan....."Cikin sanyin jiki Yaya Mus'ab ya ɗago yace “Ba haka bane Ammi yawanci tunanin yaro shine nasararsa Kinga yanzu kece da kanki kikace mubar maganar auren Hussain da Madinah to me zamuyi da ita Ammi babu amfani zaman Madinah a gida gara ta tafi makarantar wala Allah karatun shine alkhairin rayuwarta kuma ai karatu baya hana aure tana karatun ta idan Allah ya kawo mijin sai tayi aurenta"
Barin gurin Ammi tayi Yaya Mus'ab yabita nikuma na nufi ɗakina nasa tisue na goge bakina ina tunanin idan Ammi taƙi amincewa da muradina ya zanyi Allah ya sani ina matuƙar son karatu bazan iya hƙr da karatun ba, na kusan raba dare ina juyi ranar ko islamiyyarmu ta dare banje ba har na saduda na haƙura da lamarin karatun amma kullum raina a kunci yake banida sakewa damuwa ta aure ni gashi Hamma Hussain ya daina zuwa zuwa gdanmu Baba Suwaiba da Baffa Nuhu sunce idan bai hƙr daniba zasu cireshi cikin jerin yaransu.
A zahiri ya nuna musu ya haƙura saidai a bayan fage yanata yimin hidima adashi Yaya Mus'ab ya ɗauka a gurin aikinsu yaje ya yankarmin Form na Jamb bansan anayi ba sai saura sati ɗaya za'ayi jarabawar na samu labari murna a gurina kamar anyimin Hajj da Umrah lokacin jarabawa yayi muka zana cikin kokwanto ko mu dace ko mu faɗi tunda mun riga mun san halin ƙasar mu, bayan kammalawa muka dawo sati kaɗan Jamb ta fito komai na cikin nasara na samu abinda kowanne dalubi yake nema, nan aka shiga fafutukar yanda za'ayi a biyamin kuɗin jarabawa a Jami'ar Adamawa aka samamin admission Yaya Mus'ab yasai da machine ɗinsa da system dinsa ya gamamin komai dakansa yakaini makaranta ya kamamin hostel muka fara rayuwar karatu da ɗalubai yan'uwana anan muka haɗu dake in baki manta ba.Tun a wancan lokacin kyawu na yake firgitani kinsan meye yasa kyawuna yake firgitani? Tunda na taso na mallaki hankalin kaina bayan Hamma Hussain babu wani namiji daya taɓa kallona ya furtamin kalmar nan me tsada a gurina kuma me arha a gurin ƴammatan da suka amsa sunan su mata musamman kyawawa kamata.
Zahira kinsani tun a wancan lokacin Ni dake zamu fito daga makaranta za'a ganmu tare a tsaya ace ana sonki saidai Ni bantaɓa samun wannan gatan ba muna wannan rayuwar kikayi aure kika auri Daddyn Noor har muka gama makaranta mukayi duk abinda ya dace muka dawo garinmu kikaci gaba da rayuwa a gidan mijinki nikuma naci gaba da rayuwata tare da mahaifiyata da ƴan uwana.A wannan ƙadamin ne kuma idanun jama'a yayo kaina musamman da naje karatu na dawo su Baffa Sunusi sune suka fara buɗe fagen da cewa Ammi ta mayar dani karuwa taki barni bayi aure saboda tana morar kyauna tana samun abin lasawa.
Wannan maganganu sune suka rinƙa tunzura zuciyar Ammi takan cemin Munau ki hƙr da makarantar nan tunda kin samu abinda kika samu kiyi aure ko dangin mahaifinki sa daina zagina da ganin laifina" a duk lokacin da tayimin wannan bayanin nakanyi dariya nace “Ammi kenan duk fa wanda ya zageki haƙƙi ya rage Miki tunda kinsan baki aikata abinda suke zarginki dashi ba kuma ma Ammi shi aure ai mutum biyu akeyinsa Ni kinganni fah wlh tunda na taso babu wanda ya taɓa cewa yana sona shima Hamma Hussain da kuke gani wlh bakina da nasa baitaɓa kallona yacemin Deenah inasonki ba kawai abu daya dana sani zanyi aure idan lokacinsa yayi, kiyi hƙr Ammi banason zaman banza shiyasa kikaji muna zancen juyawata karatu tunda mijin auren baizo ba"
Jinjina kai Ammi tayi tace “Shikenan Munau Allah ya taimaka ya kawo miji na gari" amsawa nayi da Amin na tashi na ɗauki handbag ɗina dana aje na shige ɗakina na cire kayana na fito na shiga bayi na watsa ruwa na sanya kayan bacci naci abinci na kwanta Zuciyata cunkushe da tunanin ta inda zan fara neman abokin rayuwa raita tana faɗamin to nayiwa Hamma Hussain magana mana aikuwa na daga waya na kirashi ya dagamin babu wani jinkiri kamar yanda na saba nace “Hamma!" Numfashi ya sauke yace “Na'am Ɓingel" yanayin yanda naji muryarsa yasa gabana faɗuwa sai nayi shiru da furta ƙudurina har Saida naji yace “Deenah meye yake faruwa ne yau na yini zirga-zirga akan sharafin karatunki harma an gama komai zaki fara karatu a Skyline university dake nan Kano makarantar tanada kwararrun malamai shiyasa na zaɓa Miki ita kuma shi kinsan wannan ɓangaren da kika ɗauka bangare ne me wahala harkar ƙwaƙwalwa har tafi ta zuciya wahala shiyasa naga gara ayi abin da gaske, to alhmdllh dake Ɓingel ɗin tawa akwai kwazo result ɗinki ya tsallake harma ya zarce kin sami gurbin karatu a cikinta saidai matsalar kuɗi amma karki damu zanji da komai tunda mun gama magana da Yaya Mus'ab komai zai yiwu da yardar Allah"Numfashi na sauke cikin raunin murya nace “Hamma Ni na hƙr da karatun Ammi aure takeso taga nayi saboda maganganun da aketayi akaina, Hamma kawai muyi aure idan da rabon nayi karatun nayi a gaba...." Wannan magana dana faɗa masa ba ƙaramin jefashi a tashin hankali nayi ba ashe abinda yake addabar zuciyarsa kenan shiyasa farkon kirana naji kamar bashida lfy.
Numfashi ya sauke cikin son kwantar min da hankali yace “Kullum shine burina Deenah karki damu lokacin ya kusa insha Allahu gobe kafin na tafi aiki zanzo gidan muyi magana da Ammi"
Haka mukayi sallama ko babu komi na ɗan samu nutsuwa inaji a raina nakai kukana inda za'a sharemin hawaye, kamar yanda ya alƙawarta min da safe kafin in tashi yazo gdanmu shine ya tasheni da tausasan yatsunsa da naji suna yawo a fuskata yana huramin iskar bakinsa na buɗe ido ina miƙa na manta a yanayin da nake ciki, ya kuwa kafeni da idanunsa ina sauke nawa akansa ai ban gama sauke idona akansa ba na yayumo bedsheet ɗin na rufe jikina ina cewa.
“Wayyoh Oh God sorry please Hamma...." Lumshe idanunsa yayi ya kwantar da kansa jikin bango yana sauke wani wahalallen numfashi na figo hijjab ɗina nasa na miƙe zan bar gurin ya riƙoni na faɗo jikinsa ya saukemin hucin numfashinsa a saitin fuskata a wahale yace “Harda ƙwalele Deenah meye yasa kikeson tsokanata da jikinki wlh kina cutar dani shiyasa na ɗauki matakin ƙaurace Miki saboda banason ayi abin kunya"
YOU ARE READING
JINKIRIN AURE
RomanceRayuwar wata budurwa kyakkyawa kuma yar boko wacce ta samu shahadar zama Consultant a ɓangaren kwakwalwa amma kash! abu ɗaya ya zame mata tarnaƙi ga rayuwarta, ba komai bane abinnan face mijin aure daya gagareta samu.