JINKIRIN AURE!!!

411 6 0
                                    

*_JINKIRIN AURE_*
*_(Ƙalubale ga ƴammata)_*

*By*

*Oum Hairan*

*Dedicated to*
Dr. Mass @gadas son so for ever.

*Free P 7-8*

_Normal 300 VIP 600 PC 1k acct details 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank. Shaidar payment ta wannan Link ɗin👇🏼._
https://wa.me/message/LFSVQWEXOXAHF1


Zahiri irin kalaman da suke amfani dasu wajen cusgunawa Adiyyah sunyi tasirin hanata walwala ta rinƙa rama babu dalili wannan ya ɗaga hankalin Alƙasim musamman lokacin da Adiyyah ta samu ciki me laulayin gaske ya kasance komai sai yayi mata kafin ya fita daga gidan hatta da girki.
Wannan ya ƙara rura wutar ƙiyayya tsakanin Adiyyah da matan yayan mijin nata wato faccalolinta ya kasance ko maganarta babu me amsawa Adiyyah zuciyarta me tsarki ce shiyasa wannan yanayi ya dami rayuwarta a haka a daddafe tayi haihuwarta ta fari ta haifi  Yaya Shamsu koda akazo batun zaman biƙi Inna me koko ita ke daukan duk surukanta amma cewa tayi bazata iya wahala mara amfani ba.
Baffana yaji ciwon wannan magana haka ya tafi Yola dangin mahaifiyarsa ya dauko wata dattijuwar ta kula masa da matarsa lokacin da sukayi arba'in tsohuwar ta tafi ya hadɗanta sha tara ta arziki, rayuwa taci gaba da tafiya babu wani daɗi indai kaga Adiyyah na walwala tsakaninta da mijinta ne ko kuma ɗanta, na manta ban faɗa miki ba a wannan lokacin Sunusi da Nuhu basu haihu ba Sunusi nada shekara bakwai da aure Nuhu yanada huɗu ga Alƙasim shekara ɗaya da rabi an sankato masa ɗansa namiji.


Aifa sai aka ƙara ɗaukar tsana aka ɗorawa Adiyyah da ɗan ta kinsan abin yaro kuma lafiyayye lokacin daya fara rarrafe Adiyyah na can na aiki saidai ta jiyoshi ya canyare da kuka tana fitowa sai taga ko Jamila ko Suwaiba wata ta make mata ɗa haka zata ɗauki abinta tayi ciki dashi ta rarrasheshi, yaron nan har wuta yasa hannunsa Jamila na girki a Madafi amma bata iya hanashi ba, wannan ta wucce wata rana Adiyyah ta shiga wanka tabar Shamsu na bacci a ɗaki ashe tana fita ya tashi ta yayo waje lokaci an siyowa Suwaiba kalanzir zatayi girki a robar swan kawai yaron ya ɗauka ya kyankyaɗa Suwaiba da Jamila suna ɗaki suna kallonshi yanata kakari da fitar da dafara babu wacce ta fito Saida Allah ya jeho Baffanmu ya ga ɗansa a wannan hali ya isa gareshi da gudu shida Baffa Kabir suka ɗaukeshi Baffanmu yana kwalawa Adiyyah kira ta fito a gigice taga halin da ɗanta ke ciki aikuwa ta fasa ihu sukayi waje a guje kafin suje asibiti rai yayi halinsa.


Sosai wannan abu ya girgiza Baffanmu take ya yanke shawarar barin wannan gida aikuwa bayan bakwai ya samu wani gidan haya shi kadai da matarsa suka shiga ciki babu daɗewa kuwa Allah ya ƙara basu rabo ta kuma haihuwar  namiji shine Yaya Mus'ab ɗina da zakiji ina yawan ambato gatana masharin kukana Yayana kuma abokina me share damuwata.
Zakiji yanda akayi ya samu wannan matsayin da darajar a gurina a hankali,
           Haka rayuwa taci gaba da tafiya shekarar Mus'ab biyu aka haifi Yaya Salees shima shekararsa biyu aka haifi Yaya Khamis sai yaya Aminu, Ni kuwa Saida yaya Aminu ya shekara tara sannan aka haifeni, Zahira haihuwata tazo da wani irin yanayi me gigita tunani domin tun kafin a haifeni komai ya janyewa mahaifinmu Mal Buba ya karɓe duk wani abu da yake nasa a hannun Baffanmu sakamakon sharrin da Sunusi da Nuhu sukayi masa dalilin siyan wani gida da yayi akusa da wanda muke ciki ya haɗe da namu dake dama ya daɗe da siyen wanda ya kama hayar ya gyareshi, bansan wanne tudu wanne gangare akabi aka sauko ba duk wannan yardar da nasamu labari dake tsakanin kakana da Baffana ta gushe ba ya zamana ko gaisheshi Baffanmu yayi baya amsawa rayuwa tayiwa Baffanmu kunci gashi bai iya komai ba sai fatauci ga babu jarin juyawa sannan ga yan' uwansa duk babu wanda zai raɓa yaji daɗi sai Baffa Kabir shikuma shima ba wata power ce dashi ba domin shima yan uwan nasa da suke ciki ɗaya sun barranta kansu dashi saboda yana tare da Baffanmu.


Tun cikina yana wata biyar Baffanmu ya kama wani ciwo ne kama da hauka sakamakon wani hatsari da sukayi shida Baffa Kabir a hanyarsu ta dawowa daga Gwangola, a wancan lokacin babu wadatar na'urorin bincike  sannan su kansu likitocin kwakwalwar sunyi ƙarancin da ba kowa ne yake da halin zuwa ya gansu ba saboda Ammi na ta sanar  dani a wancan lokacin saidai aje Lagos ko Port-Harcourt sannan za'a sami damar duba mutum indai matsala ce data shafi ƙwaƙwalwa don ko likitocinmu na arewa sunce zasuyi ƙarshe sai sun turaka can.
Tun ciwo yana ƙarami haka Ammi da Baffa Kabir sukayita fafutuka suga abin bai girma ba amma abu yaci tura karshe kan Baffanmu ya rinƙa kumbura yana wata irin firgita ko bacci baya iyawa saidai damuwa kullum cikin kuka yake kamar ƙaramin yaro idan an tambayeshi mene sai yace Adiyyah yake tausayawa ranar da baya raye gashi Mus'ab da Salees da Khamis basu kawo ƙarfi ba bare su taimaketa gata ita ba kowa ba a Nigeria idan tace zata koma Ethiopia ma can ɗin ma ba gatane da itaba tunda shima babanta Hakeem a irin yanayi da Baffanmu ya taso shima ya taso gata ita kaɗai kacal ya haifa kamar rai mace yayyanta biyu maza Daga yawon almajiranci basu dawo gida ba har aka auradda ita Tsoho Hakeem ya rasu.


JINKIRIN AUREWhere stories live. Discover now