_*JINKIRIN AURE!!!*_
_(Ƙalubale ga ƴammata)_OUM HAIRAN
Last Free Page 15-16
Nan na kawo karshen free Page na wannan littafin ki biya domin karatu cikin salama Nrml 300 VIP 600 PC 1k domin jin yanda wannan littafi zai kaya sis abari ya hucce shike kawo rabon wani in baki fara ba ki fara yau JINKIRIN AURE ƙalubale ne dake ciwa al'umma tuwo a ƙwarya
Nrml 300 PC 1k acct details 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank ko 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko kati MTN ta wannan number 09013718241, Yan Niger zaku turo katin Airtel na 500cf shaidar payment direct Link👇🏼_https://wa.me/message/LFSVQWEXOXAHF1
_____________________________
Zubamin idanu Ammi da Hamma Khamis sukayi da tsananin mamaki nidai banason tuhuma wannan tasa na miƙe na shige ɗakina na kullo ƙofata na haye katifa na kwanta gabana ya sake faduwa jin Ammi tana cewa “Bawan Allah ka baƙuncemu a bazata koda yake kace gurin Munau kazo ita kuma na fahimci kamar batayi lale da zuwanka ba"
Murmushinsa na dattako yayi yace “Nasani Hajiya ba lallai Dr. Tayi farin ciki da zuwana ba Ni wakili ne daga ƙungiyar likitoci ta duniya WHO Hajiya wani albishir ne nazo Miki dashi game da Dr. Deenah duk da dai naga ita batayi murna da wannan alkhairi danaje mata dashi ba, Am dama sakamakon tacewa da zaƙulowa da wannan ƙungiya takeyi na fasihai kuma jajirtattun likitoci yasa muka zaƙulo Dr. Suka bata damar zuwa ƙasar Faransa domin ƙara samun gogewa a ɓangarenta me muhimmaci na ƙwaƙwalwa, bayan nan sunyi mata kyaututtuka na karramawa bisa ga jajircewarta wajen kawo ci gaba a wannan fanni babbar kyautar da sukayi mata itane waccen motar dake waje sai system da kuma gurbin karatu na shekara guda domin zama ƙwararriyar likitan ƙwaƙwalwa a ƙasar Nigeria, ina fatan Hajiya ke kin fahimceni Ni wakili ne daga WHO"Shiru sukayi gabaɗayansu kowa da sakon dake sauka a zuciyarsa banda Ni da bansan meye yake faruwa ba a haka Yaya Mus'ab yazo ya ishesu suna zaman kurame babu wanda ya samu damar magana saishi dake shigowa gidan ne yace “Ammi waɗanna manyan bakin mukayi ne haka a gidan naga wata kafurar mota a ƙofar gida"
Ammi ce ta ɗago ta dubeshi tace “Gara da Allah ya kawo ka Mus'ab kaina ya kulle na rasa abin tofawa nabar bawan Allah ƙurar hazo sai ƙare masa takeyi aka"
Zama Yaya Mus'ab yayi yace “to meke tafe dakai bawan Allah da farko dai Assalamu alaika don naga motar lambar WHO ke gareta" murmushi Dr. Kaltingo yayi yace “Ai motar ma nan zan tafi na bar muku ita" nan ya zayyane masa komai Yaya Mus'ab yaja dogon numfashi ya sauke yace “Danƙari maƙari wannan lamari da girma yake yanzu dai ƙwarai munawa WHO godiya ne matuƙar tarin yawa alhmdllh ko iya haka Ɓingel taci moriyar nacinta gashi har duniya ta fara sanin da ɓurɓushin tsirarta a ban ƙasa maganar zuwa Faransa ƙaro karatu kuma Dr. Kaje nidai Amatsayina na wanda nake magana da yawun Madinah na amincewa tafiyarta muna fatan tafiyarta tsanin nasararta ce......"Ammi ce ta ɗago tace “Anya Mus'ab hakan kana ganin zai yuwu kasan fa yanayin da Munau take ciki kowa bayama rayuwarta uzuri gani sukeyi kamar itace ta tsarawa kanta ƙaddararta Mus'ab inajin tsoron kada tafiyar yarinyar nan Faransa ya sake janyo mata wata masifar da bayan ta dawo zata hanata kwanciyar hankali"
Khamis ne ya magantu da cewa “Yanzu Ammi zaman nata meye ya rage nifa ina ganin tayi tafiyarta kawai shine yafi mata alkhairi...." Dr. Kaltingo ganin ya samu goyon baya yasashi saurin cewa “Kuma babban abin sha'awar inta dawo da aikinta zata dawo domin lokacin da zasu gaba karatun lokacine da WHO take daukan sabbin ma'aikata tare da gwaggwaɓan albashi Hajiya tuntuɓe daɗin gushi akwai asibitin da muke ginawa anan Kano da Gombe cikinsu ne Wannan ƙungiya zata bata jagorancin ɗaya Kinga kenan wannan dama ce da bai kamata ayi wasa da ita ba"Murmushi Ammi tayi tace “Yaro duk naji wannan amma nikam a son raina naga Ɓingel ɗina tayi aure suna zuwarmin da mijinta suna gaisheni suna tafiya....." Da sauri Dr. Kaltingo yace “Shima auren Lokacine idan lokacinsa yayi za'ayi Ammi ayi ta addu'a ba gaggawar ba samun mafi alkhairi" da haka wannan zama ya tashi nikam ina ɗakina bansan inda aka kwana ba sai magrib ina zaune a ɗaki naji sallamar Hamma Hussain gabana ya faɗi sosai inajin a raina kamar in tashi in fita wata zuciyar tana hanani amma nayi mamakin yanda aka bari ya fito yanzun da ɗanyen ciwo a kirjinsa bai warke ba.
Kasa dannar ruhina nayi na miƙe na fito mukayi karo dashi yana niyyar shigowa ɗakin nawa na matsa na bashi hanya ina buɗe bakina nace “Ya akayi wannan wanne irin kulawa likitanka yake baka da zai baka damar yawo a wannan lokac....." Ban rufe bakina ba naji nayi flat a cikin jikinsa yasa hannunsa biyu ya zagayeni ya ɗora kansa a saman kaina cikin zafin fitar iskar numfashin dake nuna wannan zuciya tana cike da ƙunci yace “Wlh babu wata mace da zan iya yima kyautar samartaka ta indai bata kasance keba Ɓingel zanyi nesa da kowa dominki a yau na gama komai nawa na barin ƙasar nan zan tafi Italian domin yin wani course ina tunanin zai ɗaukeni watanni takwas insha Allahu kafin na dawo zanyi duk me yiwuwa na daidaita komai muyi aure kafin na rasa rayuwata ta dalilinki......"
YOU ARE READING
JINKIRIN AURE
RomanceRayuwar wata budurwa kyakkyawa kuma yar boko wacce ta samu shahadar zama Consultant a ɓangaren kwakwalwa amma kash! abu ɗaya ya zame mata tarnaƙi ga rayuwarta, ba komai bane abinnan face mijin aure daya gagareta samu.