Assalamu Alaikum! Mariam ta kara daga murya cikin siririyar muryar ta tana kara sallama Assalamu Alaikum! Daga can cikin gidan ta jiyo ana amsa mata kafin aka bata izinin shiga, dauke da kwaryar furar ta ta idasa shiga gidan tana murmushi tace Inna Allah Yayi na samu dawowa, Innan ta karaso tana murmushi tace sannu Maryamu sannu kinji, bari in kawo maki ruwa da dan sauran dumamen daya rage mana sai kiyi hanzari kici ki wuce Islamia kada ki makara, Mariam tace Inna bari kawai ni zan dauko abincin da kai na basai na daga ki ba, nasan kinyi aiki kin gaji, ga kuma baba da kike jinya, sai hawaye sharrrrr, Innan ma cikin sanyin jiki tace to ya muka iya da Ikon Allah Maryamu? Sai dai muyita addu'a Allah Ya bamu ikon cinye jarabawar mu kawai, taci gaba da cewa gaki da saurin kuka indai akan baban ki ne... Mariam tayi murmushin cikin kukan ta katse Innan da cewa ko kuma Innata ko? Innan ma tayi daria tace wannan gaskia ne Maryamu, Allah Ya maki albarka.
Daganan Mariam ta mike ta karasa can karshen dan akurkin gidan nasu mai kama da kango, a can ta samu mahafin ta yana bacci, tayi kusan minti biyu tana kallon shi tana hawaye kafin ta yi addu'ar da kullum take dauke a bakin ta sama da shekaru biyu da baban nata ya fara jinya wato Allah Ya tashi kafadun ka babana, Inna dake bayan ta ta amsa da cewa ameen, gami da mika mata kwanon dumamen tuwon tace yi sauri kici ki wuce makaranta. Mariam tana cin abincin take baiwa Innan labarin yau an samu cinikin fura domin ta siyar da duka furar saboda tsananin zafin da ake ne tana ga yasa mutane suka fara rububin siyan furar kasancewar lokacin ta ne, saida ta gama sana ta isa ga Inna ta mika mata cinikin furar, kafin ta shiga daki ta dauko jikkar littattafan ta tanawa Inna sallama zata tafi Islamia, Inna tayi mata addu'a gami da tunatar da ita tayi tata addu'ar idan zata fita daga gidan, cikin ladabi tace toh Inna.**
Asalin su en kauyan Dankama ne dake karkashin hukumar Kaita ta jihar Katsina, Malam Ibrahim shine mahaifin Mariam kuma su hudu ne Allah Ya baiwa iyayen su kafin rasuwar su, Hamza shine babba sai maibi mashi Dahiru sana shi mahafin Mariam wato Malam Ibrahim sai kuma autar su Uwale. Sai kuma mahaifiyar Mariam wato Inna, Asalin sunan ta Maryama ne, Malam Ibrahim takwara yayi mata ya maida sunan ta ga tilon diyar su, kuma basu boye sunan da sunan ta suke kiran ta wato Maryamu.
Talakawa ne likis da basu da cin yau bare na gobe amma akwai Ilimin addini daidai gwargwado, babu yanda Uwale autar su Malam Ibrahim batai ba akan ya auri kawar ta Asabe lokacin daya tashi aure amma fir yaki yace shi ya hango bafulatana Maryama wacce take ba uwa ba uba duk sun mutu babu kuma wani guda daya kwakwkwara da zata ce dangin ta ne, sai walagigi take cikin kauyan Babbar ruga wanda yake kafin a karasa kauyan moda da Dankama, Malam Ibrahim kuma yaje ne siyar da kajin shi wajen wani mutum da suka saba harkar cinikayya anan Allah Ya hada shi da Maryama, Uwale tabi dukkan sauran yayyin ta da matan su ta hure musu kunne akan auran da Malam Ibrahim zaiyi, sun Kuma yi iya bakin kokarin su akan su hana shi auran Maryama da basu san asalin ta ba amma yace shi yaji ya gani, wannne sanadin da duk suka janye jiki daga gare shi kuma dama su din ba wani Ilimin addini ba bare na boko, tunda Maryama ta shigo gidan suka kafa mata kahon zuqa ba kamar da suka ga ta haura shekara shida da aure amma ko batan wata bata taba yi ba wannan yasa Uwale ta kara tada maganar kawarta Asabe wacce a lokacin auren ta uku da yara biyu, Malam Ibrahim yace baisan zancan ba shi yana son matar sa a haka aiba 'ya'ya ya aure ta ta haifa masa ba, ya ganta ne yana so ya aure ta, yana fata ne Allah Ya bashi zuri'ar tare da ita kuma dan bata haihu ba baya nufin ya dena son ta harda zai mata kishiya tazo ta daga musu hankali suna zaune lafia, wannnan maganar ta kara iza wutar kiyayyar Maryama a wajen Uwale da sauran matan yayyin ta, Fatsuma matar Hamza sai Jamila matar Dahiru wa'anda duk halin su daya da Uwalen dan zama mu iya cewa sunfi Uwale nunawa Inna Maryama tsana da kiyayya, musammam suke zagayo wa ta katangarta suna yada mata habaici, so daya bata taba daga kai ta kalle su ba bare ta tanka wannan kuma ba karamin tunzurasu yake ba, ga Fatsuma dai tace ita ba abinda yafi firgitata irin kyawun da Inna Maryam take da shi kamar jinsin Jinnu, yayin da Jamila tace ita kuma yanda Inna Maryamar take magana ne ta tsana, tana wani magana can kasa kasa kamar tsohuwar munafuka kuma duk yanda zasu zage ta bata taba tanka musu ba bare ta samu ta duke ta kota huce haushin ta da take ji, yayin da Uwale kuma take ganin ai kyawun Maryama ne yasa dan uwan ta Malam Ibrahim ya nace sai ita zai aura kuma tasan kyawun nan ba'a banza ba kila tayi wani surkullen su na fulani ta mallake mata dan uwa, ita kuwa Uwale a dunia babu abinda ta tsana irin daya daga cikin yayyin ta ukku a samu wanda zaifi son matar sa akan ita tilon er uwar su da aka mutu aka bar musu suka rene ta tun kankantar ta. Yaran Fatsuma hudu a lokacin duka mata, Hadiza suna kiran ta dije, Aisha suna kiran ta da A'i, Hafsat sai kuma auta Hawwa suna ce mata kulu, daga kan su Allah Bai kara bata haihuwa ba duk kuwa da fadi tashin ta akan ta haifi namiji, dan fatsuma tana cewa idan mace bata haifi namiji a gida ba to batai wata haihuwar azo a gani ba, sana kuma tana tsoron ranar da Hamza zai yi mata kishiya akan da namiji saboda hamza ya fita son ya samu yaro namiji.
Gidan Dahiru kuwa yaran sa biyar danshi matar shi rurrutsa ta rika haihuwa, mata uku sai maza biyu, Karima ce babba sai Sa'adatu sai Amina ana karshe ne ta samu Jabir kafin Kaseem ya zama autan ta dan haka ita Jamila bata da haushin haihuwar namijin amma tana tsananin jin tsoron son mata irin na Dahiru dan yasha gaya mata ko wane lokaci zai iya karo aure shiyasa kullum duk abinda Jamila ta samu yana wajen en borin kauyan da ma makwabtan su akan a hana Dahiru kara aure.
Uwale kuma tana auren wani abokin Dahiru ne Tasi'u shima dai rufin asiri ne kawai gare shi amma baya da shi gaskia, yaran su uku Nuhu, Rabe sai Balki itace autar su. Uwale ce ta biyu a gidan Tasi'u kuma itace Allah Ya baiwa yaran da suka rayu domin dayar matar Tasi'u ta haihu har hudu amma duka basu rayu ba, ganin hakan da Uwale tayi yasa tabi da addabi kishiyar ta Hajara ta hanata sakat.
Daga baya Hamza ya auri Rakiya wacce ta haifa masa en biyu duk maza Hassan da Hussaini, ba karamin kishi ake tsakanin Fatsuma da Rakiya ba dan kowacce cikin su er bala'i ce ta bugawa a jarida, kuma kowaccen su da irin kalar kiyayyar da takewa Inna Maryama musamman ganin ita ba haihuwar kuma Malam Ibrahim baida niyyar kara auren. Gidan Dahiru ma ya kara auren mata biyu Halima da Rabi, Halima dai a bazawara ya auro ta dan har tana da yaran ta biyu a gidan marigayin mijin ta amma da zata auri Dahiru ta baro su wajen babarta, kuma tunda ta auri Dahirun bata yi ko batan wata ba, yayin da Rabi kuma take da tilon yaro wato Umar.
Gidajen su a jere suke dana juna kasancewar gado ne tunna iyayen su dan haka sai kowa yaja katanga ya kuma fitar da kofar gida, ita kuma Uwale ta siyar musu da nata kason sai tayi jari da kudin ta tana siyar da kayan cikin gida na masarufi, to cikin su dai babu wanda Allah bai rufawa asiri ba amma koda wasa babu taimako tsakanin su, baran tana su taimaki Malam Ibrahim wanda duk ya fisu mugun talauci musamman da aka bi dare aka sace mashi en kajin dayake kiwatawa, wani irin bakin talauci gidan Malam Ibrahim ake fama da shi, idan suka samu suka ci abinci so daya a rana to bama su tunanin wani karin abincin, tun yana zuwa neman taimako wajen en uwan shi harya hakura ya dena neman taimakon kowa sai Allah. A shekarar su ta takwas da aure ne Allah Ya albarkace su da samun diya mace inda Malam Ibrahim ya mayar da sunan Maryama, har bayan haihuwar Inna Maryama bata dena shan gorin dangin miji da facalolin taba, Halima matar Dahiru ta biyu kadai ce bata da hali irin na sauran, ita suna shiri sosai da Inna Maryama kuma ita tayi wankan jegon ma, Mariam ma kusan wajen ta ta tashi saboda Halima akwai son yara gashi ita nata yaran ba damar ta kawo su wannan fitinannen gidan kada a fitine su gara mata suna zaune gaban mahaifiyar ta cikin rufin asirin Allah.
Babu Ilimi ko wane iri ga rayuwar mutanen nan, har zuwa lokacin da Mariam ta kai minzalin shiga makaranta, Malam Ibrahim ya sakata makarantar Gwamnatin dake kauyan nasu, gefe kuma tana zuwa makarantar allon dake gaba kadan dasu, Mariam tun tana yarinyar ta halayen ta kaf na mahaifiyar ta ne sanyi sanyi, muryar tama ko fita bata yi sosai, bata da kawa ko daya sai Innar ta sai kuma Inna Halima da yaran ta idan sun kawo wa Inna Halima ziyara wato Atine da Larai. Harta gama primary ta samu shiga JSS One anan Government Day Dankama, kamannin ta sak na mahaifiyar ta kamar yanda halayen ta yake na mahaifiyar, sai dai ita tana da wata kalar kwayar ido blue wanda suka kara mata wani irin kyau, da alamun ta dan dauko kalar fatar Malam Ibrahim duba da yanda hasken ta baikai na Inna Maryama ba dan ita fara ce tass sabanin Mariam da farin nata ya dan banbanta da na mahaifiyar ta.
Malam Ibrahim ya fara jinya ne kusan shekara biyu kenan, ciwon nashi gashi nan dai ba za'a ce ba tunda ba asibiti suka kaishi ba babu kudin asibitin bare na motar zuwa birni, saidai a kwantar a tayar, har magana wani lokaci takan yi mashi wahala ga kuma bakin talauci dan baya fita nema saboda rashin lafiyar da yake fama da ita, Inna Maryama ita ke fadi tashin abinda zasu ci, yau intayi wannan gobe tayi wannan, cikin hakan ne aka fara zafin nan irin mai tsananin shiga jikin nan dan haka ta yanke shawarar fara dakawa Mariam fura ta kai gidaje taga ko za'a siya cikin ikon Allah kuma ana siyan saboda tsananin zafin da ake mutane sunfi bukatar abu mai dan sanyi sanyi haka.Wannan kenan daga labarin Mariam, muje ga babi na biyu domin ci gaba da labarin Mariam.
AsmauLilly ✨❤️
YOU ARE READING
Mariam
RomantikRayuwar Mariam ta fara ne a kauyan su cikin tsananin talaucin da yayi sanadin barin ta gida zuwa binni aikatau, kafin daga baya komai ya canja dalilin AIKATAU.