Mariam 10

20 2 4
                                    

Ranar Monday kamar yanda mamma ta fada, suka dira saman filin tashin jiragen Nmandi Azikiwe dake garin na Abuja, tare da taimakon wani aminin daddy, shiya siya ticket din su, yasa direbanshi yaje general hospital aka kwashi malam Ibrahim da inna maryamu da inna halima, saida ya tabbatar da tashin su sana ya koma gida ya shedawa ubangidan sa ya saka su a jirgin max air kuma yaga tashin su sai fatan Allah Ya sauke su lafia, Alh Aminu yace ameen, sana ya dauki waya ya kira daddy ya masa bayanin da direban shi ya mashi. Can bangaren daddy ya sanarwa mamma abinda ake ciki dan haka mamma tace to daman nizamiye hospital sunce a sanar musu idan majinyatan sun taso daga katsina dan haka bari na sanar musu, ina kyautata tunanin sunce zasu je da motar asibiti domin daukar majinyacin, nima kuma bari in aika salisu yaje airport sai ya taho da iyayen mariam mata din, daga baya sai muje asibitin mu duka domin duba mahaifin mariam din, daddy yace toh masha Allah, hakan yayi, Allah Ya bashi lafia, Allah Yasa kaffara ne, mamma tace ameen.
Haka kuma ya faru, mintuna da basu wuce hamsin ba jirgin na max air daya kwaso su inna maryamu da inna halima da suka kusa sakin fitsari yayin tashi da saukar jirgin saboda kauyanci da rashin sabo, jirgin ya sauke su a filin jirgin na Nmandi Azikiwe domestic wing, ma'aikatan jirgin suka taimakawa su inna maryamu har suka fita daga cikin jirgin suna ta raba idanu da alamun tsoro ya cika fuskokin su, motar asibiti na kasa tana jiran su kasance war filin jirgin na amincewa motar asibiti ta isa har inda jiragen suke, saboda lalura irin ta rashin lafia, babu bata lokaci wani ma'aikacin jirgin max din wanda ke siya wa iyalan daddy ticket duk idan zasuyi tafiya ya nemi su inna maryamu da inna halima ya sada su da motar asibitin bayan an riga da an shigar da malam ibrahim ciki, ma'aikacin ya sanarwa su inna maryamu suzo zai kaisu wajen da mota zata dauke su domin ba tare zasu tafi da motar asibitin ba, ya sanar musu sakon mamma ne cewar direban gidan ta yana arrivals yana jiran su domin ya kaisu gida wajen su, daga baya su zasu je asibitin ne, inna halima kamar zatayi turjiya domin ganin abun take kamar a mafarki, ji take kamar wani ya kwashe ta da mari domin ta farka daga wannan mafarkin mai cike da al'ajabi, inna maryamu ce tayi shahadar damkar hannun inna halima taja ta suka bi ma'aikacin jirgin nan, saida ya kaisu arrivals ya sada su da salisu direban mamma sana ya juya ya koma bakin aikin shi, salisu ya gaishe su cikin mutunci da fara'a daya koya wajen ahalin daddy, ya sanar musu shine zai kaisu gida wajen su mamma, inna halima ta kasa daurewa tace to shi malam ibrahim da wata mota babba mai jiniya ta dauke shi fa? Salisu yace motar asibiti ce, sun wuce dashi ne domin su fara bashi taimakon gaggawa da yake bukata, ku kuma zamu je gida ku huta sana a kaiku wajen shi, haka kawai sukaji sun nutsu da bayanin salisu musamman da yake mutuntasu babu alamun nuna kyamatar yanayin su da ya gani, domin kallo daya zakayi musu ka tabbatar da cewa talauci ya musu katutu.
Suna tafe kan tituna na Abuja suna ganin tsaruwar garin da tsabtar shi babu wannan ledojin da ake yarwa akan tituna kuma yalwar mutane na tafiya a kasa da kafarsu, yawanci duk motoci ne saidai kaji fuuuu mota ta wuce, sanyin ac da car freshner ya musu sallama, saida suka sauke ajiyar zucia sana suka saki hanci suna shakar ni'imtaccen kamshi da basu taba jin ko mai kama da shi ba, yayin da gefe daya suka bude idanu kowa cikin su ya dafi kofar bayan mota daya suna kallon garin na Abuja, inna maryamu a ranta tana cewa yanzu a irin wannan gari diyarta mariam ke rayuwa? Ikon Allah, lallai Allah, Allah Ne, Yar zuqu man yasha'u bighairi hisab. Ita ma inna halima tunanin da takeyi kenan wato anan yaran ta laure da atine ke rayuwa? Shiyasa idan suka koma gida sai tagansu sunyi sharr sunyi kyau abun su, sai ma ta kasa daurewa saida ta jefawa salisu tambaya yanzu ita maryama a gidan da zaka kaimu take ko tana ina? Sai salisu yace wacece maryama? Inna halima tace maryama da ita hajia mamma aka kawo mata a mtsayin er aikin ta, sai salisu yace ohoo ai bangane ba da kikace maryama, anan muna kiran ta da mariam ne, yaci gaba da cewa kwarai kuwa tana nan gidan mamma, mariam uwa ga aisha noor kenan. Sukam basu gane nufin shi na mariam uwa ga aisha noor ba amma sun fahimci mariam din tana gidan da za'a kaisu din daka sai sukai hamdala kawai sukaci gaba da kalle kallen su.
Wajen karfe sha biyu saura na rana suka karasa bakin gate din gidan daddy, inna maryamu a ranta tace to ashe kallon bamuyi komai ba, ita a tunanin ta ko gidajen da ake hadawa a gina wuri daya ne akayi wa wannna katon gate din dan haka ta bari idan aka bude suka shiga taga irin gidajen da aka kewaye da kofa babba haka, kusan tunanin su daya da inna halima amma sunyi mamakin da bala mai gadi ya bude musu suka shiga sai suka hango gini waje daya sai wani wuri can dake da alamun na aje motoci ne, to sai kuma wajen pool dake can baya kadan da gidan, amma idan aka shigo daga gate kana iya gane pool side ne, ga zaton su inna maryama irin tafkin nan ne da ake samun ruwa masu kalar kasa dinnan a ciki, salisu har bakin kofa ya kaisu ya danna door bell sana ya koma gefe yana jiran a bude musu kofa, banda waige waige babu abinda sukeyi suna ta ala'ajabin gida irin wannan, dako a mafarki basu taba tunanin ganin shi bare shigar shi ba, baba asabe ta bude kofa ta wangale tana musu lale marhabin da sauka, suma suka washe baki suna gaisheta a tunanin su ko itace mamma ma, baba asabe tayi musu izinin shiga ciki sana tayi gaba tace su biyo ta ta kaisu wajen mamma dake falo tana jiran isowar su, har ciki salisu ya kwaso kullin kayan su ya kawo musu ba tare da nuna kyama ko wani abu ba.
Mamma ta mike ta yalwata kyakykyawar fuskar ta da fara'a tana musu barka da sauka, ta basu wuri su zauna bisa kujera amma sai suka durkushe kasa suka shiga gaishe ta, baba asabe ta wuce kitchen domin kawo musu abinci, mamma tace haba haba innar mariam ku mike ku zauna bisa kujeru mana, inna halima tace a'a hajiya anan ma ya isa ai mungode mungode Allah Yafi mu godewa, Allah Yasa ladar a mizani, mamma tace toh ameen, fatan ko wane musulmi mai kwadayin Rahamar Allah kenan, to ya hanya ya kuma kuka iso nan? Gaba dayan su suka amsa da lafiya lau Alhamdulillah! Mun same ku lafia? Mamma tace lafia lau muke, a nanne baba asabe da kauna suka kawo masu manyan farantai guda biyu, daya na dauke da abinci dayan kuma dauke da ruwa da lemo da filet da spoons, mamma tace to ga abinci nan kuci ku koshi sana a kaiku ku warware gajiyar hanya, suna so su tambayi ina maryama take amma sai suka kasa hakan, mamma kuma bata ce musu komai ba saima ta mike da noor dake hannun ta tana cewa to idan kun gama cin abinci asabe zatazo ta kaiku masauki saiku watsa ruwa ku huta kafin anjima kadan muje dubo mahaifin mariam, sai anan inna halima tayi kokarin cewa hajia nikam inaso in tambaya ina ita maryama take domin tunda mukazo bamu ganta ba, inna maryamu taji kamar ta tashi ta rungume inna halima da tayi wannan tambayar domin itama abinda ke ranta kenan amma kunya da fulako irin na fulani yasa ta kasa aiwatar da hakan, mamma tayi daria tace mariam ai tana makaranta bata kaiga dawowa ba amma anjima kadan zaku ganta nan, nasan yau ko islamia ba zata samu zuwa ba indai ta gan ku, domin bamu sanar mata zaku zo ba naso ne tazo kawai ta same ku, mamma ta karasa fada tana taka matakalar bene, saita barsu kamar mutun mutumi inna maryamu tace nikam halima ko kinji dakyau me hajia tace ne game da Maryama? Inna halima tace nima sai nake ganin kamar kunne na bai jiye mani daidai ba, domin da yaren da mukeji tayi maganar makaranta da kuma islamia, ikon Allah da yawa yake gaskia, mu bari idan Allah Ya hadamu da maryama ita zata warware mana komai.
Akwai charlet a gidan na daddy acan aka masu masauki, daki biyu ne da falo, kowane daki dauke da restroom a ciki, inna asabe bata barsu ba saida ta nuna musu yanda zasuyi amfani da famfo su tari ruwa cikin botiki domin suyi wanka, saida kuma ta tabbatar ta aje musu sabulun wanka da tooth paste, da sabon brushes kowa da nasa, ta kawo musu dogayen rigunan da mamma ta aiko kauna domin ta kawo masu, mamma na yawan siyan kaya ta aje saboda idan ta samu baki da zata bai mawa, wani lokacin ma bakin kwana take bai masa kamar dai yanzu da rigunan zasuyi wa su inna maryamu amfani, irin budaddun rigunan nan ne wanda basu bukatar shape saboda a sake aka yi su, hatta da shampoo saida baba asabe ta basu, kuma cikin mutuntawa da wasa da daria duk ta musu bayanin komai da yanda zasuyi amfani dashi ba tare da wani abu ya shige musu duhu ba, baba asabe tace abinda duk baku gane ba to ku barshi kawai idan na sake dawowa sai ku nuna mani, inna halima tace mun gode maku, godiyar mu bata da iyaka, Allah Yafi mu godewa, mun gode sosai, baba asabe tayi daria tace ai a gidan nan babu godia sai dai addu'a. Kuma musulmi dan uwan musulmi, babu wanda yafi wani a wajen Allah sai wanda yafi jin tsoron Allah dan haka kada ku damu wanna gida iyakar sanin mutunci da karamci sunsan shi kuma suna kwadayin ladar Allah. Inna maryamu da inna halima suka hada baki wajen furta toh Allah Ya kai musu ladar a mizani, baba asabe tace ameen, ta kuma cewa tunda kunci abinci bada jimawa ba to kuyi wanka ku canja kaya sai kuyi salla tunda zuhr tayi, sai kuma ku kwanta ku warware gajiyar hanya, bari inje kitchen in fara hada abincin rana.
Bayan sun shirya suda kansu sukaga zuwan su da baifi awanni biyu ba lallai an samu canji a tare da su, gashin inna maryamu da baya samun gyara saboda rashin kayan gyaran da kuma rashin nutsuwar da zai bada damar gyaran saifa yanzu da ta saka shampoo ta wanke gashin ta da yake tsefe domin ita daman bamaiyin kitso bace ba, gashin ta irin mai tsantsi ne da tsayi, shiyasa ko anyi mata kitso baya kwana biyu yake warwarewa da kan shi, sai kawai ta dena wahalar zaman kitson, take tattare gashin wuri daya, yau da ya samu gyara an wanke an gyar ta sake tattare gashin gefe daya sai ta fito sharr abunta ga kamshin turaren da baba asabe ta aje musu, inna halima ta kasa yin shiru tace Fatabarakhallahu ahsanil khaliqeen, maryamu dole facalolin ki suke jin haushin ki, dole su tsane ki, dole suyi kishin ki duk da ba mijin ku daya ba, Allah Ya kyautata halittar ki iyakar kyautatawa, ga halaye na kwarai da Allah Ya wadata ki da su, shiyasa malam ibrahim baya kallon kowa tunda yasan irin matar daya aje a gida, inna halima ta karashe zancan ta da tsokana tana daria, inna maryamu tace kai halima baki rabo da tsokana dai, kema ai gayanan kinyi kyau abun ki, gyara dai yana da dadi gaskia, Allah Ya karawa Annabi (S.A.W) daraja, su duka suka amsa da ameen. Baccin kam bai samu ba sai hira da sukai tayi yayinda gefe daya suke tsumayin ganin maryama.
Mariam bata shigo gidan ba sai wajen la'asar kasancewar sun samu traffic akan hanya, ta ishi salisu direba daya canja hanya ta kagara ta koma gida wajen noor dinta, tun safe na barta bata ganni ba nima banganta ba, mariam ta karashe maganar ta kamar zatayi kuka, salisu yace kiyi hakuri mariam bada jimawa ba zamu je gida In Sha Allah. Sanda suka karaso gidan da gudu ta shige ciki bayan kauna ta bude mata kofa, kai tsaye dakin mamma ta wuce inda take da tabbacin nan zata samu noor, ai kuwa acan ta same ta ana canja mata diaper, ita kanta noor din tana ganin uwar goyon nata ta hau bangala daria tana nuna alamun ta gane ta, mamma ta kama baki tace ikon Allah, yaran zamani sai a hankali wato ke nan noor kina nufin harkin gane uwar goyon taki ko? Mariam na daria bayan ta dauki noor ta manna a kirjin ta take cewa mamma barka da gida mun same ku lafia? Mamma tace daga baya kenan, ai nikam harna hakura da bambamcin da kike nuna mani, kullum babu kowa a ranki sai na diyar goyon ki, to nima ai diyata Aimana tana hanya, gobe wal haka muma muna tare In Sha Allah, Mariam ta fadada fara'ar ta tace Allah Ya kawo mana ita lafia, mamma tace ameen.
Mamma tace yawwa zo muje ki raka ni charlet din can, muna da baki inaso muje mu gaishe su, babu komai a ran mariam ta mike tana cewa to mamma muje, tana rike da noor a jikin ta suka isa char let din, kafin su shiga saida mamma ta tabbatar da ta karbe noor daga wajen mariam. Kasancewar a bude kofar take hakan ya basu damar shiga ciki, a falo suka samu inna maryamu da inna halima suna hira cikin nutsuwa da mamakin hali irin na mutanen gidan nan, mariam ta murza idon ta da hannuwan ta, ta bude ta tabbatar da innar ta take gani, sai hakan bai isheta ba, saida ta kara goge idanuwan ta amma duk abu daya dai take gani, innar ta zaune da inna halima suma suna kallon ta cikin al'ajabin canjin da mariam ta samu cikin abunda baifi wata daya ba, da gudu mariam ta kwasa ta cakumi inna Maryamu, sai kuma hawaye ya biyo baya, inna halima tace ikon Allah daga farin ciki sai kuka kuma? Inna maryamu da duk kunya da dadi suka rufe ta saita kasa cewa komai sai kokarin kwace kanta da takeyi daga jikin mariam, da kyar mariam ta cika ta sana taje wajen inna halima itama ta rungume ta tana gaishe ta, daga nan mariam ta koma wajen inna maryamu tayi zaune kusa da ita, gani take kamar mafarki takeyi har saida ta juyo tace mamma dan Allah ba mafarki nake ba kuwa? Bana so su bacewa gani na, mamma da tuni tayi ma kanta mazauni a daya daga cikin kujerun wajen tayi daria tace babu mafarki anan ciki mariam, iyayen ki ne mata gasu nan gaban ki, sai a lokacin mariam tayi hanzarin mayar da duban ta ga inna maryamu tace inna ta ina babana? Ya jikin shi? Mariam ta karashe tambayar ta da alamun sanyin jiki a tare da ita, inna maryamu tace Alhamdulillah zamu ce, yanzu ma tare muka zo dashi amma an wuce dashi asibiti, mamma dake gefe ta mike tana cewa to bari na karasa ciki in shirya sai muje asibiti mu duba jikin mahaifin mariam din, daga haka mamma ta wuce dauke da noor a hannun ta.
Hira kam sunsha ta wajen mariam, babu abinda ta rage na daga abinda ya biyo bayan zuwan ta garin Abuja, da renon noor da takeyi, da yanda suka saka ta school na boko da da arabi duka, da irin yanda suka mayar da ita kamar diyar gidan ba mai aiki ba, da yanda take da mahaifin noor din domin ga zuwa yanzu sun kara sabawa da arham sosai, kusan kullum sunayin waya a kalla sau biyu safe da dare, idan ya zama busy shine yake musu kira daya kacal a rana, kai hatta da yaya fatima yanzu tasan da zaman mariam da noor, kasancewar mamma ta kira sauran yaran nata biyu wato fatima wacce suke cewa yaya fatima kasancewar itace babba a gidan, sai kuma hawwa'u wacce suke kira da aimana, duk mamma saida ta kira su video call on whatsapp sukayi magana a tare ta musu bayanin noor da mariam duka, dan haka suma sukan kira mariam din suji ya take ita da noor? Kawai dai basu hadu a ido ba amma suna yin waya har video call suke, aimana daman tana da burin zuwa gida danta kwana biyu bata zo ba kasancewar duk ba a Nigeria suke zaman auren su ba, dan haka ta shirya batun zuwa gida cikin satin.
Inna maryamu da inna halima suka kada kai suna cewa munfa gani, mutunta dan adam anan gidan har ba'a magana, inna halima taci gaba da cewa maryama tunda muka zo ake hidima damu, kinga hatta sabon kaya saida suka bamu, babu abinda suka rage mu da shi, Allah Ya saka musu da alkhairi, amma ina jan kunnen ki daki barranta kanki da saba musu dan girman Allah, babu butulci kuma mariam, duk abinda zakiyi domin ki kyautata musu dan Allah kada ki fasa, ke ko aro kyautayi zakiyi to ki tabbata kin aro domin ki kyautata musu, inna maryamu tace gaskia ne halima, maganar ki gaskia ne, nima kuma abinda nayi niyyar fada mata kenan, tunda kin rigani shikenan sai kuma muyi fatan maryama ta rike hakan a zuciyar ta, sai kuma batun ita Aisha Noor din, ki rike ta tsakanin ki da Allah, ki sani idan kika cuce ta Allah Ba Zai barki ba, domin Allah sukayi maki domin ita Aisha Noor din sukayi maki, kuma zan nuna maki yanda ake yin kunun kamu kala kala na yara domin ki rikayi mata, hakan zai taimaka mata sosai wajen ingancin lafiyar ta da girman ta duka, mariam tace toh inna nagode.
Wajen karfe biyar na yamma suka kama hanyar zuwa nizamiye hospital, harda daddy da yace tare zasuje shima ya duba mara lafia, inna maryamu da inna halima sunyi ta godia da addu'a da aka kaisu su gaisa da daddy, bayan sun gaisa ne yace shina dashi za'aje asibitin dan haka mota biyu sukayi, mota daya daddy ne da direban shi sai mamma a gefen shi. Dayar motar kuma salisu ke jan ta, sai mariam na gaba ita da noor, inna maryamu da inna halima na gidan baya, a haka suka karasa asibitin.
Ko ba'a fada ba lallai sun ji dadin ganin kyakykyawar kulawar da ake baiwa Malam Ibrahim, ba kamar general hospital da suka baro a katsina ba, marasa lafia a zube kamar ba masu jinya ba, babu wata kulawa ta kirki, gwamnati kuma babu abinda takeyi, Allah Ya rufa mana asiri gaba daya. Basu jima ba sosai suka tafi gida sakamakon wani likita daya basu shawarar su je gida kawai nurses zasu bashi kulawa yanda ake bukata kuma baya bukatar yawan hayaniya, suna iya dawowa daga baya su gaisa, da wannan suka tafi gida cike da kwarin gwiwa hade da kuma addu'a.

AsmauLilly❤️✨

MariamWhere stories live. Discover now