Mariam 06

15 3 0
                                    

Mamma ta kalli mariam tayi murmushin nan nata tace a zubo maki abinci mariam? Mariam ta kada kai tace an kawo mana abinci munci, mun gode sosai Allah Ya biya Ya saka da alkhairi, ameen. Mamma tace to Alhamdulillah, mariam jeki waccen kofar ta nuna mata kofar kitchen da mariam taje dazu, idan kin shiga kice asabe tazo ina neman ta, cikin ladabi mariam ta amsa gami da mikewa domin cika umarnin mamma, ba'a jima ba suka dawo tare da asaben, asabe ta zauna kasa tana cewa barka da fitowa mamma gani ance kina nema na, mamma tace yawwa asabe, daman ina so ne kije da mariam wajen ku kiyi mata wanka ki wanke mata gashin ta, inda keda datti a fidda shi, ina son ganin wannan kyawun nata ya fito sosai yanda ya kamata, mariam ta sunne kai cikin jin dadin kulawar mamma da kuma kunyar wai aje a mata wanka kamar ta katuwa da ita haka, mamma taci gaba da cewa zan aiko kauna ta kawo maki kayan da zata saka da kuma turaren jiki dana kaya da sabulun wanka, asabe ta amsa cikin ladabi da cewa to mamma.
Mamma ta kira sunan mariam, mariam din ta amsa amma bata iya ta dago kai ta kalle ta ba, mamma taci gaba da cewa ki tashi kibi asabe tayi maki wanka sosai inaso inga kinyi gayu kin fito a matsayin ki na kyakykyawa kinji mariam dina, mamma ta karashe maganar cikin lallashi, mariam sai ta kasa tankwabe wannan kyakykyawar kulawar ta mamma kuma dama can ita ba mai gardama bace ba, ta mike tana mai cewa asabe muje toh, a daidai lokacin kamshin turaren royal oud creed ya cika katon falon, da kuma sallamar ma'abocin kamshin cikin husky voice din shi, kallo daya zaka mashi ka tabbatarwa ranka lallai Allah Yayi halittar namiji anan wajen, kai tsaye bazan iya cewa ga abun kushewa ba a tare da shi ba, sanye yake cikin yadin filtex mai kalar navy blue, da takalman sa sawu ciki (inji hausawa) babu hula a kan shi sai sumar sa da yake dan tarawa idan ta dauko yin yawa sai yaje a saisaye ta, fuskar shi ba zaka iya cewa ga yanayin da yake ciki ba domin ba fara'a yake ba haka kuma ba daure fuska yayi ba, wata fara karr din mata mai dauke da dogon tsinin dunduniyar maroon din takalma na tafe a gefen shi,fuskar ta babu annuri sam, kamar wacce mala'ikan mutuwa ya dirar mawa, lace ne a jikin ta mara nauyi mai background din lilac sai an mashi ratsi da kalar maroon, mutum na iya ganin dinkin matar wanda aka mata fitted gown, sai dan karamin gyalen dake rataye a kafadar ta. Asabe ta dakata da tafiya sashen su kamar yarda Mamma ta umurce ta sai ta tsaya domin gaishe da masu shigowa, fuskar ta dauke da fara'a take masu lale marhabin, sai a lokacin Arham ya danyi murmushi yayi hanzarin gaishe da asabe saboda yasan idan ba yayi saurin gaishe ta ba to ita zata gaishe shi, hakan kuma kunya yake bashi ganin ratar shekarun dake tsakanin su, asabe ta amsa gami da gaishe da Nafisa amma ko Nafisan bata ji bane ba oho tadai wuce fuuu kamar kububuwa tana mai karasawa wajen Mamma, mariam ta tsuguna har kasa tana gaishe da Arham, lafia, shine kadai Arham ya iya furta mata yadai kalle ta sana ya wuce ya karasa wajen mamma, asaben ta kama hannun mariam suka nufi wata kofar ba wacce ta zama ta kitchen ba, cikin zuciyar asabe tana tambayar kanta ko lafia irin wannan zuwan da Arham da Nafisa sukayi? Ai basu ma jima da komawa kasar da suke da zama ba to meye ya dawo dasu? Allah Yasa dai lafia, shine abinda ta fada a zuciyar ta.
A can falon kuma nafisa ta karasa wajen mamma ta saki kururuwa kamar mahaukaciya, mamma tace subhanallah, nafisa lafia? Wani ne ya mutu? Daga shigowa gida sai kururuwa? Ganin nafisa kukan ta take tana sheshsheka yasa mamma ta maida dubanta ga Arham tace masa Arham lafia? Kukan me nafisa keyi? Ya dan daga kafada irin ko in kula dinnan, kafin kuma ya isa bakin kafafun mamma ya zauna bayan ya riko hannun ta yana gaishe ta, mamma na mamman mu, mamman barka da rana, mun same ku lafia? Mamma ta amsa duka lafia, ina amsar tambayata? Arham yaja numfashi yace mamma kinsan bana iya magana cikin hayaniya idan tayi shiru zan maki bayanin abinda ke faruwa idan kuma batayi shiru ba to zan tashi in barta sai ita tayi maki bayanin abinda ke faruwa, jin hakan sai nafisa ta kara sautin kukan ta, zuciyar ta na wani irin kuna da tafasa, tana fadawa Arham bai damu da damuwar ta ba, ganin abun yaki karewa sai mamma ta mike tana cewa to ni ina da abunyi idan ku baku da shi dan haka ba zaku shigo mani gida ku nemi tayar mani da hankali ba haka kawai, mamma tasa kai ta haye bene zuwa dakin barcin ta, cikin zuciyar ta tana addu'ar Allah Yasa koma menene yazo masu da sauki, tana shiga daki ta kira wayar kitchen tana neman kauna tazo ta amsa kaya takaiwa asabe domin a sakawa mariam.
Tana gama waya Arham da Nafisa na fadowa dakin, ta dena kukan sai jan ajiyar zucia da takeyi, ranta a cunkushe yake sosai, basu kaiga magana ba kauna ma ta shigo dakin bayan tayi knocking an bata izinin shiga, mamma ta mika mata kayan data riga ta fito dasu tace amsa ki kaiwa asabe, kauna ta rusuna kasa ta amsa kayan, ta gaishe da su Arham, shi kam ya amsa amma nafisa bata ma san kaunar nayi ba, babu bata lokaci kauna ta bar musu dakin gaba daya zuwa sashen su domin isar da sakon mamma.
A can daki mamma ta hade fuska tana cewa kunga na fada maku idan babu wanda zai iya mani bayanin dalilin da yasa ake neman tayar mani da hankali to ku kama kafa ku koma inda kuka fito bana neman tashin hankali haka kawai ina zaune lafia, Arham ya ruko hannun mamma yana cewa mamma dan Allah kiyi hakuri kada ranki ya baci, yanzu ma dole ne tasa zuwan nan da mukayi, Arham yayi shiru kafin yaja ajiyar zucia yace mamma na sani kome nafisa zata fada to laifi na ne na kuma amsa, amma mamma ina neman afuwar ki tun kafin kiji abinda na aikata, dan girman zatin Allah ki yafe mani mamma, ni dan adam ne mai ajizanci, kuma ina da dalili na mai karfi, cikin dinbin karamcin ki nake neman afuwar ki dan girman Allah mamma, Arham ya hada hannu biyu yayin da yayi durkuso gaban mamma, zuciyar mamma saida ta kusa tsinkewa saboda wani bala'in tsoro na abinda za'a fada mata Arham din yayi, musamman ganin tun kafin nafisa ta fadi abinda yayi din amma ya durkusa yana mai amsar laifin sa yana kuma neman yafiyar ta, tun yarintar Arham zuwa yanzu daya mallaki hankalin kanshi yake da shekaru talatin, mamma ba zata iya cewa ga wani mugun abu daya taba aikatawa ba bare a kawo karar sa, to me yayi ne yanzu da har matar sa ta aure wato nafisa ta kawo mata karar shi? Shi kuma ya amsa laifin tun kafin a fadi laifin?
Nafisa kamar tasan abinda mamma ke sakawa a ranta, cikin zubar da hawaye tace mamma Arham yayi wa wata karuwar sa ciki ta haihu, yanzu haka tafe muke da shegiyar diyar da aka kawo mashi shekaran jiya a matsayin diyar shi kuma Arham ya amsa diyar, wasu irin taurari suka giftawa mamma a idanu dan haka ta nemi ganin ta na wucin gadi ta rasa, a wannan lokacin na tabbata idan aka auna jinin ta za'ace ya hau sosai, da kyar ta iya lalubo kalmar InnaLillahi wa'inna ilaihi raji'un ta fara furtawa, zufa kuwa babu inda bata shiga tsatstsafo mata ba ba, yau wace irin bakar rana ce haka wajen ta? Arham din ta, Arham mai tsananin kyankyami, Arham mara son magana, miskilin danta Arham, Arham din da mata basu ishe shi kallo ba, Arham dake da addini, Arham din da tunda take dashi koda kuskure bata taba jin yayi subutar baki ya furta kalmar banza ba, ta yaya hakan ta faru?
Bangaren Arham kuwa harya daga hannu zai shararawa nafisa mari sai kuma ya sauke hannun shi cikin tsananin fushi, jijiyar jikin shi na tashi ya nuna ta da yatsa yace wannan shine karo na karshe da zaki sake kallo na ki furta mani maganar banza, daga haka bai kara cewa komi ba sai yasa kai ya fice daga dakin, kitchen ya nufa yana neman asabe, nan kauna take fada mashi tana can sashen su tanawa mariam wanka, dayake ran shi a bace yake saibai fahimci me take nufi ba sosai illa ya gane tana can sashen su na masu aiki dan haka kai tsaye ya wuce can, saida ya kwankwasa kofar, asabe da lokacin ta gama tajewa mariam curarran gashin kanta data wanke mata tass da shampoo, ta bata kayan da mamma ta aiko mata na wata doguwar riga 'yar kanti tace mata ta saka, ganin asabe ta tafi bude kofar dakin nasu sai ta zare zanin dake jikin ta ya zama daga ita sai dan pant din dake jikin ta, tahau kiciniyar saka rigar, a daidai lokacin kuma Arham ya danno kai cikin dakin nasu bayan asabe ta bude mashi dakin ta kuma bashi hanya alamun ya shigo, idanun shi akan mariam wacce ko kirgar dangi bata fara ba, gabanshi ya yanke ya fadi a lokacin da sukayi ido biyu da mariam ta zuba mashi idanun ta da kwayar idon ta masu kalar blue blue suna zuba shekin su, ita kanta a razane take da ganin wani namiji a dakin, zata iya cewa wannan shine karo na farko da wani namiji ya ganta tsirara tun bayan mahaifin ta dake mata wanka, shima ganin ta girma ta kusa gama primary sai ya dena sai ya zamana innarta ce komai nata, har zuwa lokacin data iya yin komai nata, Arham yayi hanzarin juyawa yana cewa yi hakuri dan Allah bansan da ke ba, sai a lokacin asabe ta lura da katobarar da tayi domin harga Allah tayi tunanin cikin 'yan matan dake aiki ne a gidan wata ta buga kofar to kuma data bude kofar taga arham ne shaf ta manta da mariam dake dakin tana kokarin saka riga, kasancewar arham din har dakin nasu yana zuwa amma wajen ta musamman idan yana da wata magana da yake so ya fada mata, yanzu ma ta tabbata wani abun ne ya kawo shi shiyasa ta bashi hanya domin ya shigo daga ciki.
Asabe tace mariam yi hakuri na manta kina cikin dakin na budewa ubangida na kofa ya shigo bari in bishi waje inji kome ke tafe da shi, bata jira cewar mariam ba sai ta fice tabi arham, cikin gidan ta same shi a falon farko na gidan, bata jira cewar shi ba shima tace ubangidana ayi hakuri shaf na manta da mariam dake saka kaya a dakin, mariam mariam sunan arham ya maimaita kafin ya dan tabe baki yace amma dai baaba asabe ya kamata a rika lura sosai, asabe tace InSha Allah za'a kiyaye, kafin kuma tace me kake da bukata ubangidana? Arham yaja ajiyar zucia yace muje daga wajen mota tukuna, babu musu asabe tabi bayan shi, har suka isa wajen wata bakar mota kirar Mercedes asabe bata tambaya ko lafia ba, ya bude bayan motar ya saka hannu ya dauko babyn dake bacci har zuwa lokacin ba tare da tasan meke faruwa ba, asabe tayi saurin karbar yarinyar ba tare data ce masa komai ba, arham yace baaba asabe ga baby nan kije da ita wajen ku kafin abubuwa suyi sauki, idan da abinda ake bukata na babies ki fada mani zansa a kawo maku, asabe cikin kasa gane halin data ke ciki ta amsa masa da toh, arham ya bude boot din motar ya fiddo katon akwati guda ya mikawa asabe yace ga kayan babyn nan kije ki duba abinda zaki bukata, harda madara da feeding bottle duk akwai a ciki sai kiyi yanda akewa babies, arham yaci gaba da cewa baaba asabe wannan alfarma ce na nema da kiyi mani wato kula da babyn nan dan Allah, asabe tace zanyi iya bakin kokari na ubangida na, daga haka ta juya zuwa cikin gida yayin da ta umurci mai bawa flowers din wurin daya dauki akwatin yakai can sashen su.
Asabe ta shigo dauke da baby a hannun ta, mariam dake zaune gefe tayi saurin tashi ta mikawa asabe hannu tana murmushi tace baby ne? Kawo babyn in rike, asabe ta mika mata babyn ba tare da tace mata komai ba, kamar babyn tasan meke faruwa tana zuwa hannun mariam ta tashi daga baccin da takeyi ta hau mutsu mutsu sai mariam ta fara mata daria tana mata wasa, asabe tayi hanzarin janyo akwatin babyn da aka kawo mata, ta bude ta dauko madara da fida ta nufi kitchen din cikin gida tana cewa mariam bari inzo yanzu, mariam din tayi nisa wajen wasa da babyn dan haka bata ma san me asabe take fada ba, asaben bata jima ba ta dawo dakin ta cewa mariam kawo ta a bata abinci, mariam ta dago tana kallon asabe tace ki kawo in bata, asaben tace kin iya ne? Mariam tace a'a amma zan koya sai in rika bata kullum, asabe tayi daria tace to kawo ta yanzu in bata sai ki ga yanda akeyi kinga saiki koya ko? Mariam ta mikawa asabe babyn sana ta matsa kusa dasu dan ganin yanda ake baiwa babyn madarar.
Nutsuwa irin na mariam zakai tunanin ta kusa lunka shekarun ta, ta nutsu sosai tana ganin yanda ake baiwa babyn madara har asabe ta gama ba babyn madara ta daga ta ta saka saman kafadar ta tana shafa bayan ta har babyn tayi gyatsa sana asabe ta sauke ta, mariam tace meyasa kika saka ta a kafada kina shafa bayan ta bayan da kika gama bata abincin? Asabe tayi murmushi tace saboda anaso tayi gyatsa ne, shiyasa ake saka su a kafada ana shafa bayan su har suyi gyatsa idan ba haka ba to madarar zata iya dawo mata, duk babies haka ake musu, mariam tace toh nagane kinga yanzu na koyi abu biyu kenan na yara, asabe tace dami dami? Mariam tace da bada madara da kuma sanya su suyi gyatsa, asabe tace lallai kam ashe da wuri zaki gane komai kenan, yanzu bari inje in hada ruwa inyi mata wanka sai a canja mata kaya.
Cikin mintunan da basu wuce talatin ba asabe ta wanke babyn tas ta bude akwatin ta ta dauko mata wasu kayan ta saka mata bayan ta saka mata diaper, asabe tace mariam ina son zuwa cikin gida zan iya bar maki babyn nan inje in dawo? Cikin sauri mariam tace eh kije ki dawo ki bar mani ita zan mata wasa. Asabe kai tsaye dakin mamma ta wuce ta yi knocking kofa, mamman ta bata izinin shiga, a can ta samu nafisa wacce har lokacin idanun ta kamar garwashi dan azabar kuka, amma asabe na shiga dakin nafisa ta mike bataiwa kowa magana ba cikin mamma da asabe tasa kai ta fice gaba daya daga gidan da niyyar zuwa nasu gidan. Asabe ta samu wuri gefe ta zauna ganin halin da mamma take ciki, da alamun wani abu ya kada ta sosai, asabe cikin sanyin murya tace kome yayi zafi maganin shi Allah, kaddara mummuna tana daga cikin shika shikan imani, kuma rayuwar ba zata taba tafiya ba ace kullum cikin samun abinda bawa ke so yake, dole wata rana sai ka samu abinda baka so kuma wannan abun shine mummunar kaddara dan haka mamma na roke ki da Allah ki sassauta zuciyar ki da koma meye, ki barwa Allah sai kiga komi yazo da sauki.
Da wannan kalaman na asabe ne mamma ta samu saukar da nannauyar ajiyar zucia sai kuma ta kalli asabe tace asabe meke shirin faruwa da mu ne? Kinji abinda nafisa ta fada mani? Mamma bata jira cewar asaben ba taci gaba da cewa asabe nafisa ce mani tayi arham yayi wa wata cikin shege harta haife cikin kuma ta kawo musu, wannan dalilin ne yasa su zuwa gida babu shiri, asabe tace ashsha Subhanallah, taci gaba da cewa to mamma kinji daga bakin arham din? Mamma cikin kunar zucia tace asabe tun kafin nafisa ta furta mani batun cikin shegen ai arham dinne ya fara karbar laifin sa yana bani hakuri, asabe cikin kwantar da murya tace to amma mamma ko arham yayi maki cikakken bayanin abinda ya faru? Mamma tace wani bayani bayan ya riga daya karbi laifin sa? Asabe ma tace duk da haka zaifi kyau mamma ki bashi dama domin kiji ta bakin shi, wata kila abinda ake zato ba haka bane ba, mamma ta sake yin ajiyar zucia taci gaba da cewa na rasa abinda ke mani dadi asabe, wannan batu baiyi mani dadi ba ko kusa ko alama, bari daddy ya dawo in fada mashi sai muji me zai ce, asabe tace to hakan babu laifi amma dan Allah mamma abi komai a hankali, sanin kanki ne ubangida na baya da mugun hali irin wannan da matar sa ta aibata shi da shi, nafi kyautata tunanin a bashi dama domin ya kare kan shi, bata jira cewar mamman ba taci gaba da cewa arham ya kira ni ya bani babyn, yanzu haka na baro ta da mariam a dakin mu, mamma sai tabi asabe da kallo kawai ba tare da tace komai ba.
Da dare bayan daddy ya gama cin abinci mamma tayi mashi bayanin abinda ya same su yau dinnan, daddy yayi salati amma baiyi fada ba sai ya dauko waya ya danna number din arham, bugu daya ana biyun arham ya amsa wayar yana sallama, daddy ya amsa sallamar gami da cewa arham kazo gida yanzu ina neman ka, arham din yace daddy yanzu haka ina cikin gidan zuwa na kenan, gani nan karaso wa, minti biyar ba'aiba arham ya bayyana gaban su, ya gaishe su cikin ladabin nan nashi, daddy kadai ya amsa, mamma kuwa sai ta maida kai gefe, daddy yayi gyaran murya yace arham mamman ku ta fada mani abinda ya faru dazu amma ina so inji daga bakin ka gaskiyar abinda ya faru, shin abinda matar ka nafisa ta fada gaskia ne?

AsmauLilly ❤️✨

MariamWhere stories live. Discover now