Washe gari kamar yanda Daddy ya fada, bayan da arham ya shigo da safe ya same su a dinning suna breakfast, bayan gaisuwa ne daddy yace yawwa arham dazu bayan sallar subh, akayi radin suna na babyn nan da muka samu an samu Aisha, Allah Ya raya ta cikin musulunci Allah Ya mata albarka, gaba daya suka amsa da ameen. Daddy bai jira cewar arham ba yaci gaba da fadin kuma cikin sa'a an samu yarinyar da zata kula da ita wato mariam, arham ya nanata sunan mariam cikin zuciyar shi, yana kokarin tuna inda yaji sunan.... Daddy ya katse mashi tunani da cewa mamma tasa a kawo mata yarinyar mace da zata rika zama da ita cikin gida tunda ita yanzu bata da masu zama kusa da ita duk ta aurar daku daddy ya fada cikin murmushin tsokana, daddy yaci gaba da cewa to a jiyan an kawo mata yarinya karama daga katsina state, sunan ta mariam, to mun yanke shawarar zata zama mai kula da baby Aisha, amma duk nauyin ta kai ne zaka dauka ina nufin dawainiyar ita mariam din, abu kadan dazan cire maka bai wuce cinta, shanta, sutura idan naga damar dinkawa kenan dan surutar tana cikin abinda dole zaka rika yi mata, sai kuma gurin kwana da zasu zauna cikin gidana amma daga ba haka ba komai nata kai ne zakayi ko kana nan ko baka nan zan kira ka kana aiko da kudi anayi mata, kuma kudin aikin ta duk kai ne zaka rika bayarwa, abu na gaba kuma ni da mamman ku mun yanke shawarar kada mu durkusar da rayuwar yarinyar dan haka zaman ta karkashin mu matsayin mai aiki bazai hana mu tallafi rayuwar ta mu inganta mata rayuwa ba dan haka ina bukatar kafin ku koma inda kuka fito kaje ka samu school mai kyau ka saka ta, ka biya duka abinda ake bukata, daga nan kuma kazo ka samu islamiya itama ka saka ta, sai kuma ka nema mata lesson teacher dake da background na arabi da boko da zai rika zuwa gida yana mata, daddy ya karashe batun shi cikin daure fuska duk don kada arham yaji an dora mashi dawainiya da yawa.
Arham din cikin ranshi baiyi mamaki da yawa da batun daddy ba domin yasan gefe daya daddy yayi hakan ne domin ya hukunta shi abisa auren amritha sultana bada sanin su ba, kuma daddy yasan arham din yana da ninkin baninkin abinda zai cire domin ya saka mariam makaranta, bugu da kari arham yasan wannan na daya daga tsarin su daddy da mamman matukar suka dauko mutum da niyyar ya temaka masu da aikace aikacen cikin gida to ba zasu zuba mashi ido ba dole sai sun bullo da hanyar da suke ganin zata taimaka ma mutumin domin ci gaban shi, wannan kadan ne daga cikin halayen daddy da mamma.... Mamma ta katse tunanin arham da cewa to kuma ya bakace komai ba ko kana ganin an dora maka dawainiya da yawa ne? Arham ya saki murmushi yace a'a mamma kawai ina tuna yawan karamcin ku ne ga mutane, hatta wa'anda kuka dauko domin suyi maku aikatau baku yarda ku barsu haka nan ba sai kun bullo da hanyar da zata temaki mutum, Allah Ya saka muku da Alkhairi, Allah Ya duba bayan ku, Allah Ya amintar daku dayin mutuwar shahada, gaba daya suka amsa da ameen. Arham yaci gaba dacewa daddy duk naji bayanan ka kuma In sha Allahu babu abinda zai gagara, gashi dama bana zaton anyi wasu satittika da komawa school, dan haka asa ita mariam din tazo ta same ni sai muje in kaita Funtaj International School. Cikin jin dadi daddy ya fadada fara'ar shi yace to madalla ka kuwa kyauta, domin makarantar nada kyau sosai, da wannan suka idasa cin abincin kafin mamma ta mike tace to bari inje in duba diyata mariam da nayi nayi tazo taci abinci amma taki fitowa ta makale ma Aisha, sai binta asabe tayi da abincin a daki, daddy da arham sukayi murmushi kawai.
Mamma ta samu mariam tana kiciniyar sakawa Aisha diaper, mamma tace mariam da Aisha na lura wannan lamarin naku sai mun dage, to kindai ci abincin ki ko? Mariam tace eh mamma na ci nagode Allah Ya saka da alkhairi, mamma tace ameen amma daga yau bama bukatar godia tsakanin mu, mun zama daya kenan In Sha Allah, mariam tace toh mamma nagod... mariam tayi saurin kama bakin ta. Mamma tayi murmushi tace a hankali zaki saba, yawwa bani Aisha sai kije dinning area arham da daddy suna can ki samu arham zai kaiki makaranta, cikin rudewa mariam ta kallo mamma sai hawaye ya fara zubo mata, she is speechless wannan wa'anne irin mutane ne? Taya suka san tana da buri akan karatu? Burikan ta kaf akan karatu ne domin ta tallafi faqiriyar rayuwar da sukeyi ita da iyayen ta, ta fitar da rai tunda batun zuwa aikatau ya shigo cikin rayuwar ta, amma kwana daya da zuwan ta gidan aikin ake mata maganar karatu? Wa'annan mutane wane irin karamci da tausayin al'umma ne da su haka? Mamma ta girgiza ta tana cewa ke mariam lafia ko karatun ne baki so? Cikin sauri da kuma zubar hawaye mariam tace a'a mamma, ina so wallahi ina so, duka burikana sun ta'allaka akan karatu ne, da na fitar da ran karatun sai kuma naji kinyi mani magana shine... mamma tace Allah Sarki, haka rayuwa take mariam shiyasa bawa ya yarda da Allah kuma yayi hakuri to komai nashi zaizo da sauki, yanzu ki tashi kije ki samu arham din.
Mariam ta fito rike da Aisha dake hannun ta tana jijjigata da alamun bacci zatayi domin bata jima da gama bata madara ba kuma asabe tayi mata wanka da safen nan, a falo ta same su ba akan dinning table ba, ta nemi gefe can nesa kadan dasu ta zauna a kasa sana ta gaishe da daddy, cikin kulawa ya bata hankalin shi yake amsawa yace kun tashi lafia ke da kanwar taki ko? Mariam tace lafia lau daddy (kamar yarda taji kowa na kiran shi). Mariam ta juya side din arham shima tana gaishe shi, arham ba yabo ba fallasa ya amsa gami da cewa matso nan kusa inji ya batun karatun ki yake domin su daddy da mamma sunce in kai ki makaranta, zamu tafi yanzu amma dole zansan ina kika tsaya a karatun ki, mariam cikin sanyin muryar nan nata tace a makarantar mu har na shiga jss one, amma banci gaba da zuwa ba saboda jinyar babana sai kuma yanzu nazo nan.
Arham yace ok bakomai kije ki fadawa mamma zamu je makarantar sai ki same ni a mota, daga haka ya mike yanawa daddy sallama, daddy ma ya mike yace nima ina da meeting a CBN Headquarters bari in wuce. Mariam ta samu mamma a dakin ta ta shiga bayan tayi sallama an bata izinin shiga anan ta tarar da asabe kuma da alamun magana sukeyi dan haka cikin hanzari tace mamma dama yace inzo in fada maki zamu je makaranta ne, mamman tace to shi wanda yace baya da suna ne? Mariam ta sunne kai tana murmushi, mamma ganin mariam zata iya bata lokaci sai tace to kawo Aishar sai kuje ku dawo sai ki amshe ta don na lura kina neman tafiya tare da ita ne, mariam ta danyi shiru kafin kuma taje ta kwance Aisha dake bacci a kafadar ta, mamman tasa hannu ta amshe ta tana cewa anya mariam zaki iya karatun nan ma? Mariam tace eh mamma zan iya, mamma tace to ai naga Aisha na neman hanaki zuwa ne, mariam din tayi daria kadan ta juya tana cewa baba asabe da mamma sai mun dawo bari in same shi kada in tsayar da shi, suka mata a dawo lafia.
A bakin harabar gidan ta same shi yana jiran ta, yana ganin ta ya dan hade fuska yana cewa meye ne sunan ki ma, bai jira cewar ta ba yaci gaba da cewa bana son jira, don haka kinyi na farko karki kuma na biyu, cikin sanyin murya mariam tace kayi hakuri, na tsaya na baiwa mamma aisha ne dake bacci, sai kuma bai kara cewa komai ba yayi gaba tabi shi a baya. Ya nuna mata motar a gidan gaba yace ta bude ta zauna, sai mariam taja gefe tace taya zan bude motar ban iya ba? Arham yayi tsaye cak kamar bazai motsa ba ko gani yayi ba amfani oho dai yazo ya bude mata yace ta shiga, sai da yaga ta zauna sana ya sunkuya zai saka mata belt, numfashin mariam ya kusa daukewa saboda shakar numfashin arham mai hade da turaren shi, wani irin dadi na daban ne ya ziyarce ta, bata kuma san ta yanda yake ba. Arham kuma ya sakala mata seat belt ya dago ya rufe ta sana ya zagaya ya bude mazaunin direba ya shiga ya saka nashi belt din sana ya tashi motar suka fice zuwa Funtaj International School dake cikin Apo, babu nisa daga Asokoro zuwa Funtaj din.
Awar su tafi biyu a school din, amma dayake abu ne na kudi sai arham bai samu tangarda ba sosai, jss one din aka sake saka mariam, amma saboda teachers din sun mata interview babu wani abun kwarai data sani sai suka so su mayar da ita koda primary 5 ne sai Arham yaki yarda, dan haka suka bashi shawara akan a maida hankali wajen yi mata extra lesson, nan suka bada uniform din ta da na sport day din ta. Tunda suka hau hanyar komawa gida Mariam ke cike da wani irin fara'a wacce take shimfide akan fuskar ta, tsarkake Allah takeyi a ranta tana kuma kara godia ga Allah da kuma wa'annan mutane masu cike da karama masu maida dan wani na su, saida mariam ta kasa hade abinda ke ranta, ta juyo a hankali ta fara godia, nagode Allah Ya saka muku da alkairi, Allah Ya biya, Allah Ya raya Aisha, Allah Ya kai mizani, nagode nida iyaye na muna godia sosai, saita fashe da kuka.
Ba shiri Arham yaci burki, ke ke wait karki kara mani kuka da aka maki me? Haka kawai ki daga mani hankali ina zaune lafia na? For what ? Mariam ta dan goge hawayen ta tana cewa kayi hakuri, na rasa ta yanda zan nuna godia ta ne kukan kuma na tausayin kai na ne da kuma na jin dadin abinda kuka mani ni da iyaye na domin ni da su iyayen nawa kuka yi mawa, abu daya da arham ya fara fahimta game da mariam shine tsananin soyayyar ta ga iyayen ta, abu na biyu shine ya lura tana da sanyi sanyi babu hayaniya cikin lamarin ta, akwai nutsuwa dan haka sai yaji ya kara nutsuwa da zaman Aisha wajen ta.
Kai tsaye gidan da basu koma ba kenan sai ya wuce da ita shopping, kaya yayi ta jido mata, babu ce kadai ke babu a kayan da Arham ya siyawa mariam yau, saida ya gama yaje biyan kudi sana mariam tace kaji ba'a siyawa Aisha nata kayan ba, Arham yayi shiru kamar bazai ce komai ba sana ya juyo ya kalle ta yace ni bansan ya kayan yara suke ba amma nan basu da kayan yara bari na kira mamma inji ina ake siyarwa sai muje itama a siya mata, babu bata lokaci ya kira mamma ya tambayeta, one stop baby shop dake garki 2 zaku je inji mamma. Nan arham yasaka a google map din shi suka dauki hanyar garki 2 daga wuse 2. Lallai kam yaci sunan shi shop din wato one stop baby shop. Baby Aisha kam tasha kaya harda su madara dasu feeding bottle, komai kam da kayan wasan yara duka mariam tayi ta jidowa, shikam yana gefe yana kallon ta ba tare daya tanka mata ba, amma a ranshi cewa yake wannan yarinyar kodai tunani take ina da kudin banza kila shiyasa take ta jidar kayan nan da yawa haka? Hatta soap da cream, body oil da su diaper babu wanda mariam ta bari, wata cikin attendants din ta samu mai jin hausa ta makale mata tana fada mata irin abunda take so, attendant din kuma daman irin su mariam suke nema wanda zasu zo suyi ta kashe kudi a wajen dan haka wani abun ma ita ke nunawa mariam shi, ita kuma ba bata lokaci sai tace a saka cikin kayan su.
Lokacin da akayi lissafin abinda total ya kama Arham shiru kawai yayi, ita kuma mariam da alama bata san lissaafi ba sosai dan babu abinda ya dame ta sai daukar kayan data shiga yi da niyyar kaiwa wajen mota, ma'aikatan sukace ta bari za'a kai musu a mota yanzu, dan haka sai taja gefe tana jiran Arham.
Sai da suka fara tafiya ne Arham ya juyo yana kallon ta rike da set din wata feeding bottle yace ita kuma wannan bottle din lafia kike rike da ita baki bayar an saka a cikin kayan ba? Cikin murmushi tace ina so da na isa gida in fara nunawa Aisha bottle din da zan rika bata madara da shi ne, Arham ya girgiza kai kawai, sai kuma yaci gaba da cewa to ya batun karatun ki na addini fa, domin nayi waya a nema maki islamia ance an samu anan apo zone e. Mariam tace ina da hadda har zuwa izif 20 kuma na iya karatun arabi babu laifi, nafiyin hadda ne dai saboda babana ke koya mani a gida ko makarantar allo shiyasa kila nayi nisa har haka. Arham yace to Alhamdulillah! Ina so inja hankalin ki akan duka karatun da zaki fara yi, kuma ina gargadin ki akan abokai, da kuma shiga abinda ba naki ba, kuma idan baki maida hankali ba akan karatun ki duka ba lallai fidda ke zanyi don bazan rika kashe kudin da nake nema da kyar ba akan banza kina ji na ko? Mariam tace eh naji zan kiyaye, da wannan suka karasa gida.
Mamma kam da taga siyayya da yawa haka batayi mamaki ba domin ta san kyauta a cikin jinin su duka take, sai ma addu'a da tayi da godia, Arham yace haba mamma ai wajen ku muke koyo,, Allah Ya kara bamu abinda zamu bayar kawai, mamma tace ameen. Mariam tuni dama tun shigowar su ta yi wa mamma barka da gida gami da tambayar ta ina Aisha take? Mamma tace tana wajen asabe, dan haka kai tsaye mariam kitchen ta nufa, anan ta samu asaben goye da Aisha, mariam tace baba asabe abani yar kanwata hakanan tunda na dawo, asabe da kauna dake girki sukayi daria suna cewa daman maganar da mukeyi kenan yanzu.
Washe gari mariam ta fara zuwa school, direban mamma wato salisu shi zai rika kaita yana dauko ta, kasancewar suna bada abinci acan yasa mariam tea kadai ta sha, mamma na cewa ba zaki ci ko da bread ba? Mariam saboda zumudi tace a'a mamma a makarantar sunce suna bada abinci dan haka idan naje zanci a can, har zata wuce ta dawo tace mamma ki kula mani da Aisha idan ta tashi ki fada mata yayarta mariam taje makaranta ta koyo karatun da zata rika koya mata idan ta isa fara koyon karatu, mamma na daria tace toh yayar Aisha bazan manta da sakon ki ba, oya maza ki wuce salisu ya sauke ki kada ki makara, da haka mariam ta fito waje domin samun salisu su tafi makarantar.
Gaba daya yinin ranar mariam bata gane karatun ba gaskia, turanci ake musu sosai ita kuma bata gane turancin duba da inda ta fito, dan haka har share hawaye take akai akai na jin daci a zuciyar ta bata gane abinda ake koyar da su, wani da ba zai girme ta da shekaru sosai ba dake kusa da seat din ta ya same ta bayan an fita break, Hi new mate, my name is Abubakar but you can call me Sadik, is it possible for you to be my friend? Mariam ta bishi da kallo tunda ya fara magana badon ta gane me yake fada ba, kome sadik din ya lura sai ya koma magana da hausa, sunana Abubakar amma zaki iya kira na da sadik, zamu iya zama abokai? Mariam ta washe baki tace zamu iya zama abokai amma idan ka amince zaka koya mani karatu kaga ni bana ganewa kuma bana jin turanci, sadik yace shiyasa kadan kadan sai in ganki dazu kina kuka ko? Mariam tayi daria tace ashe ka ganni ina kuka, sadik yace na ganki, yaci gaba da cewa kizo muje muci abinci sai mu dawo in fara nuna maki karatun tunda yau kika fara zuwa kuma an wuce ki da wasu abubuwan, kafin kace me tuni mariam da sadik suka saba, kuma yaci gaba da nuna mata karatun nasu, sadik boarding yake yi yayin da mariam takeyin day, a ranar farko ya nuna mata abubuwa da yawa kuma da yake ta mayar da hankali sai nan take ta fara fahimtar wasu abubuwan musamman da ya zama yana mata bayani da hausa ne, gefe kuma ya fara nuna mata brighter grammer book 1.
Sai yamma mariam ta dawo gida, Aisha ta fara nema ta same ta tana bacci amma saida mariam ta dauke ta ta rungume tana jin ta kamar kanwar ta da suka fito ciki daya ne, tana son yarinyar, koba komai ta zame mata silar alkhairai da dama, silar farin ciki dan haka duk inda so da kauna da kukawa suke sai mariam ta nemo su ta baiwa Aisha wacce take tunanin sunan da ya kamata tana kiran ta da shi, nan take tayi tunanin ta rika kiran ta da NOOR, wato haske. Dan kuwa Aisha ta cancanta a kira ta da hasken, cewar mariam kenan a ranta. Mamma data shigo dakin tun shigowar mariam ta lura mariam din bata da lokacin ta sai na Aisha dan haka mamma ta karasa shigowa tana cewa mariam an dawo har an makale Aisha ko? Mariam tana daria ta juyo tana gaishe da mamma gami da cewa mamma kiyi hakuri kinsan tun safe banga 'yar kanwata ba, ina ta kewar ta ko Noor dina? Mamma tana daria tace harda sabon suna? Mariam tace mamma ai yaci in bata sabon suna kuma ta cancani sunan duba da hasken data kawo mani a rayuwa ta. Mamma tace to naji maza kizo kije kici abinci ki saka uniform din islamia domin dazu an cike form din ki an mayar masu, ance zaki fara zuwa itama yau, mariam da bata gajia da karatu tace toh mamma ai ina son karatu sosai dan haka bazan gaji ba zan tafi, bana so dai ya zama bana yini tare da Noor ne, mamma tace ai zaki zauna da ita ne idan kin dawo islamia kuma tare kuke kwana da dare.
A ranar mariam ta fara islamia itama, malaman sunji dadi sun kuma yaba da haddar da take da shi da kuma iya karatun ta na larabci don haka anan kam sun saka ta a secondary section ne, aji 3. Acewar su nanne yayi daidai da nata ilimin. Arham saida yayi murmushi dayake shi ya kaita kasancewar mamma ta fita tare da salisu. Nan aka bata uniform din ta Arham yace su kara mata uniform din sai ya kara siya.Kwana uku baya Arham ya samu daddy da mamma ya fada musu shikam zai koma US washe gari, mamma tace nafisa fa? Arham yace nayi nayi amma bata ko saurare na dan haka idan taji zata iya komawa aitasan hanyar zuwa, yaci gaba da cewa dan Allah mamma kada kuce komai akan hakan, daddy dake gefe yace to ba zamu ce komai ba amma ka tabbata babu maganar saki tsakanin ku, daddy yaci gaba da cewa babu komai kana iya komawar ka bakin aikin ka goben idan Allah Ya kaimu, Arham yayi godia mai tarin yawa sana yace bari inje inyi sallama da Mariam da Aisha, mamma tace a'a zaku yi fada kuwa da mariam domin tace a rika kiran ta da Noor wai ai itace silar haska rayuwar ta, mamma ta karasa fadar hakan da murmushi akan fuskar ta, Arham da daddy sukayi daria, Arham yace to Noor din Mariam. Bari naje na musu sallama dan jirgin sassafe zanbi In Sha Allah.
AsmauLilly✨❤️
YOU ARE READING
Mariam
RomanceRayuwar Mariam ta fara ne a kauyan su cikin tsananin talaucin da yayi sanadin barin ta gida zuwa binni aikatau, kafin daga baya komai ya canja dalilin AIKATAU.