Mariam 13

1 0 0
                                    

Asalin su Daddy en garin Maiduguri ne, da shi da Mamma duka sun fito daga nahiyar maidugurin, unguwar su daya wato custom ko kuma muce sabon layi, gidajen su ma babu nisa dana juna, mahaifan su ma duka ansan juna, hakanan kuma Allah Ya hada soyayyar Daddy da Mamma a lokacin quruciyar su, asalin sunan Daddy shine Badamasi amma a lokacin mutane na kiran sa da Masi, Mamma kuma asalin sunan ta Safiyya ne kuma sunan data taso da shi kenan, sunyi auren su na saurayi da budurwa dake da fahimta suka kuma amince ma junan su. Anan maiduguri suka fara zama a wancan lokacin saboda daddy yana bautar kasa ne, ba karatun bokon kadai daddy yayi ba, mahaifin sa saida ya tabbatar daya saka daddy cikin harkokin kasuwanci, shiyasa tun tasowar su daddy basu zauna haka kawai ba, shekarar su biyu da aure suka haifi fatima wacce ta maye sunan mahaifiyar daddy domin mahaifiyar shi ta rasu, bayan shekara hudu ne mamma ta kara samun cikin arham wanda yaci sunan mahaifin daddy wato Jafar shine suke kiran shi da arham, daga nan saida mamma tayi bari har uku sana Allah Ya tsayar mata da cikin aimana auta wacce taci sunan mahaifiyar mamman wato Hawwa'u sai suke kiran ta da aimana, ga zuwa bayan haihuwar aimana sai Allah Ya kara daukaka daddy zaman su ma gaba daya ya koma Abuja tun bayan haihuwar aimana bada jimawa ba, daddy ya rike muqamai daban daban na gwamnati har zuwa karshen matakim daya rike na SGF, wanda daga nanne daddy yayi retire, yaci gaba da harkokon kasuwancin har zuwa yau da muke, saida kuma daddy ya tabbatar daya saka fatima, arham da aimana akan harkar kasuwanci duk da karatun da sukeyi, idan mamma tayi magana yana yawan cewa to mamma idan ban saka yaran nan cikin kasuwanci ba me zan musu? Har kullum bana ganin aikin gwamnati a matsayin abinda mutum zai dogara da shi na har abada, sai a matsayin abinda mutum zaiyi temporary domin sha'awar hakan da kuma experience din da mutum yake samu. Da wannan dalilin ne kullum daddy yake shawo kan mamma dake ganin abun zaiwa yaran yawa.
Mai yiyuwa mamma tana ganin abun zaiwa yaran yawa ne saboda ita batayi karatun boko mai nisa ba, iyakar ya jss 3 ne, daganan ne aka cire ta aka mata aure da daddy wanda ta fitar a matsayin wanda take so, mamma bata da wasu en uwa da yawa, kuma daga ita sai kanwar ta iyayen ta suka haifa kuma kanwar tata bata jima ba Allah Ya dauki rayuwar ta, iyayen ta duk sun rasu ne bayan auren ta da daddy har ta haifi aimana ma. Daddy kuma su uku aka haifa gidan su da shi da kannen sa mata biyu, daya amma sickler ce dan haka batayi tsayin rai ba Allah Ya amsa rayuwar ta sai dayar mai sunan aimana wato hawwa'u, duk da dai ba saboda kanwar daddy aka saka sunan ba, aimana sunan maman su mamma ne ta ci, sunan ne yazo daya kawai.
Fatima da Arham da Aimana sun taso cikin nutsuwa da tarbiya da iyayen su suka jajirce wajen ganin sun samu, kasuwanci da neman ilimi duka saida daddy ya saka yaran nashi, suna yawan ziyaryar gida maiduguri saboda sauran tsirarun en uwa da abokan arziki dake can maidugurin. Lamarin Arham ya fara tun daga farkon balagar sa ne, da fari arham kasa gane meke damun sa yayi, shi kuma bamai surutun da zaije ya fada bane ba, ko zai fada to banda irin wannan lalurar da yake ji kullum yana karuwa, wani irin girma da tashi gaban shi ya rika yi, sai wata irin matsananciyar sha'awa ke damun shi, yasha ya boye kan shi a dakin shi yayi kuka ya sanar wa Allah damuwar shi, saida ya kusa shekara cikin wannan halin babu canji, sana ne a lokacin wata rana yaji hirar wasu samari akan yanda suke kallon film na batsa wato porn, a ranar saida arham yaji kamar ya musu kyauta, tun daga ranar safe, rana, dare babu abinda arham yakeyi banda kallon porn, makaranta ma sai ta gagare shi, mamma bata taba gane me arham ke ciki ba bare en uwan sa mata, daddy kuma yana yawan tafiye tafiye a lokacin saboda aiki ko kasuwancin shi, mamma ta fara gano arham nada matsala ne lokacin da su arham din sukayi wani hutu, saita lura gaba daya baya zama tare da su kamar yanda yakeyi a da, dan haka sai ta tsayar da hankalin ta akan Arham din, a hankali tayi noticing baya zama aci abinci da shi kamar yanda aka saba, result din shi na school babu kyau, rama ta fara bayyana a fuska da jikin shi, kuma sai ya shige dakin shi ya kulle harda key, tayi iya sandon da zatayi dan ta fakaice shi ta shiga dakin amma koda wasa baya barin kofar bude, dan haka da mamma ta ga duk yanda tayi dan ta fahimci damuwar Arham amma ta kasa sai kawai wata rana ta saka shi gaba a dakin ta da ya zo gaishe ta, mamma ta tsayar da shi tace ya koma ya zauna za suyi magana, Arham ya koma jiki sanyaye ya zauna.
Sai da mamma ta idar da duk abinda takeyi sana ta zo kusa da shi ta zauna cikin sakin fuska tace Arham inaso ne daman muyi magana akan abinda ke damun ka har yasa ka rame haka, bata jira cewar shi ba taci gaba da cewa, nayi tunanin idan kana da damuwa nice zan zamo mutum na farko ko na biyu bayan daddyn ku wajen sanin damuwar ka, da kai da sauran en uwan ka mata, toh amma naga gaba daya ka canja halayya ma, kullum kai ne cikin dakin ka kuma saika kulle, a makaranta baka mayar da hankali, komai naka ya canja, Arham meye ne damuwar ka?
Shiru ya biyo bayan nan har kusan minti biyar, da mamma ta tabbatar bazai fada ba saboda haka halayyar sa take indai bazai baka amsa ba to zaiyi shiru ne instead of him to lie, baya son yin karya ga kowa bare mahaifiyar shi mai fahimtar su, to taya zai fara fada mata irin matsananciyar sha'awar dake damun shi? Zai fada mata yanda gaban shi ke matukar mikewa har dick din yakan kwana tsaye a mike? Aida kunya a raka baqo ya zuba da gudu, dan haka yaci gaba dayin shiru kawai. Mamma taja ajiyar zucia tace shikenan Arham bazan matsa da sanin abinda ke damun ka ba, nasan baka shirya in sani bane ba, zan jira ka har kayi making mind dinka akan sanar da ni ko kin sanar da ni, tashi kaje, Allah Ya yaye maka duk abinda ke damun ka, cikin sanyin jiki Arham yace kiyi hakuri mamma bazan iya ba, mamman tayi murmushi da baikai zuciya ba tace na sani Arham, bakomai ai, Allah Ya yaye, Arham yace ameen.
**

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 05 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MariamWhere stories live. Discover now