free pg 23&24

60 1 0
                                    

🧞‍♀️🧞‍♀🌊 *MAMIYOTA CE* 🌊🧞‍♀️🧞‍♀️

MALLAKIN.

*ZAHRA ABDUL*
( MOMYN AHLAN)

SAHIBAR KAINUWA👸🏻

_littafin *MAMIYOTA CE* na kuɗi ne #200, make ur payment to this acct 6035867348 fatima abdullahi galadima keystone bank or send mtn card to this numb 08165550116, pls n pls banda vtu, ko ki dauki hoton kati ko ki kwashe lambar ki turo, masu turo da evidence of payment ɗinsu duk ku turo ta lambar, ina maraba daku masoya_😉

_ga yan niger masu buƙata ku tuntubeni dan sanar daku yadda zaku biya kuɗin karatun ku._

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*
===========
Follow me on my wattpad @Fateemah0.
==============
*MARUBUCIYAR.*
1-HALITTA DAGA ALLAH NE.
2-GUDU A JEJI.
3-SHUHADA.
4-NIDA ƘANNEN MIJINA.
5-WA'YA KASHE ZAHRA'U? #200.
6-COLONEL UBAIDULLAH.
7-ITA CE ZUCIYATA #200.
8-SAMIMA (MACIJIYA CE).
9-DA NA SANI NA.
10-GAWURTACCEN SOJA #300.
11-BADAWIYYAH.
12-AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE) #300.
13- AHLAN #200.
14-DSP ALIYU HAIDAR (incomplete).
15-SARKIN RUWA #200.

∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆

*ALHAMDULILLAH! ALLAH YA NUFA NA SAKE DAWO MUKU DA SABON NOVEL DINA MAI SUNA _MAMIYOTA CE_ INA ROƘON ALLAH YADDA YA BANI IKON FARAWA LAFIYA ALLAH YASA NA GAMA LAFIYA, YA RABBI KA HANENI RUBUTA ABINDA ZAI WARGAZA TARBIYYAR BAYINKA SALIHAI, YA ALLAH KAYI RIƘO DA HANNUNA TA YADDA IDAN KA TAYAR DANI RANAR ALƘIYAMA AKAN ABINDA NA RUBUTA, ALLAH KA KIYASHEMU AIKATA AIKIN ALFASHA, ALLAH KA SHIRYAR DAMU AKAN HANYA TAFARKIN TSIRA, ALLAH KA KARA MANA SON ANNABI MUHAMMADU SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM, DA ALAYEN GIDANSA DA SAHABBANSA DA SHEHUNNAI DA MAGOYA BAYA HAR IZUWA RANAR SAKAMAKO*🙏🏻

_TSOKACI._
*Labarin mamiyota ce ƙirƙirerren labari ne, ban yisa dan cin mutuncin wani ko wata ba, sannan ban yarda a juya min labari ba, don Allah a kiyaye shiga haƙƙi.*

_GARGAƊI_❌
*BAN YARDA A ƊORA MIN LITTAFI A YOUTUBE BA TARE DA IZININA BA, DAN HAKA A KIYAYE.*

💥💥💥💥💥💥💥

*ASSALAMU ALAIKUM, MASOYA GA WATA SABUWAR DAMA TA SAMU, GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJAR SANA'ARSU A JIKIN PAGE ZAKU BIYA 1k KACAL*👌🏻

*SANNAN GAME DA MATA MASU SHA'AWAR KOYAN SANA'A BIMA'ANA DAI SKINCARE TRAINING, GAF DA SALLAH NAYI FREE DINSA YANZU SAURAN PAID DINSA INDA ZAKU KOYI ABUBUWA DAYAWA A CIKIN KUƊI ƘALILAN, DA #1500 DINKI ZAKI KOYA YADDA ZAKI HAƊA SABULAN KI DASU OILS SU CREAMS, SU MOLATO AND MORE, YAR UWA KI SANI YANZU ZAMAN BANZA BA NAKI BANE, A YANZU KUMA KASUWAN MOLATO NA CI SOSAI, DAN HAKA KI KOYI NAKI DAN KI HUTA DA SIYA, KI HAƊAWA KANKI SANNAN KI SIYAR KI SAMU KUƊINKI KI FI KARFIN WASU ABUBUWAN, RAYUWAR YANZU DUK WANDA YACE ZAI ZAUNA ZAI GA ZAMA, BANI-BANI BABU DADI, IDAN AN BAKI YAU BA LALLAI A BAKI GOBE BA KOMA DAI A GORANTA MIKI, NEMAN NA KAI YA FI ROƘO👐🏻🙌🏻, GA WATA GARABASAN, GA MUTANE GOMA DA SUKA FARA PAYMENT SUNA DA DISCOUNT ZASU BIYA 1K NE KACAL, MUTANE GOMAN NAN NA CIKA ZAKI BIYA NML PRICE NE WATO 1500, KE DAI KI NEMI NI A TA LAMBATA 08165550116 M AHLAN SKINCARE, SAI NA JIKU MASU YI DA GASKE*🙌🏻

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

FREE-🅿️AGE-2️⃣3️⃣↪2️⃣4️⃣

"Amara meya faru kin san shi ne?" Malika ta tambayeta cikin ruɗewa, gurnani Amara ta fara tana tura hannunta cikin system din tana yi tana rungumo system din, ita Malika duk ba sanin waɗannan abubuwan tayi ba da shike ba wai bibiyar labarai take yi ba ta kalli Saima tace
"Saima kin san shi ne?" girgiza kai saima tayi tace
"A'a ban san shi ba saide lokacin da aka yi sanarwan abinda ya faru dasu wannan kuma kin san duk duniya ai ta sani,nima so nake naji hiran da za ayi da shi da abinda ya samu jami'ai  yan uwansa tunda ance ba musayar wuta bane tsakaninsu da 'yan ta'adda wani abun ne dai daban wanda basu bayyana ba kin san jami'ai navy suna ayyukansu ne cikin sirri ba komai bane suke bayyanawa, wlh ban san shi ba kawai ina so na ji labaran ne" sake kallon Amara sukayi da hawaye ya 6alle a idanuwanta tana kallon fuskar Deen dake bayani cikin natsuwa da kamala da ƙwarewa, Malika tace
"Kodai to ɗan uwanta ne?"
"Allah ma sani" Saima ta faɗa tana kan kallon yadda take kuka wanda tun zaman su da ita basu taba ganin kukanta ba fuskarta har na wani jaa da yellow,
"Ya sunansa?" Malika ta tambaya tana kallon Saima, ɗan shuru Saima tayi irin na masu nazarin nan kan tace
"Lieutenant commander Izzuddeen Tajuddeen, amma dai na ga wasu na cewa Deen Taju"
A hankali Malika ta dafa Amara ta ce
"Amara kin san Deen ne? Kin san shi? Deen? Dan uwanki ne"
Tsaida kukan Amara tayi a hankali ta ce
"Deee!"
"Eh Deen kin san shi? Yayanki ne?" ga mamakinsu kawai sai ta lumshe musu ido alamun eh, Malika tace
"Saima a wani gari ne ake abin?"
"Nigerian navy headquarters area 7 garki abuja"
"That's means a abuja ne kenan?" Saima ta jinjina kai.
"Gaskiya to a tunanina cute baby bata bukatar ayi mata aikin kwakwalwa, ina ga da zamu kai ta ta haɗu da familynta ina ga hakan ba karamin taimaka wa zaiyi waja dawowar hayyacinta ba,kuma da ace bata san shi ba hankalinta bazai tashi haka tana ta kuka ba"
"Nima tunanina kenan, ina ga idan ba Yayanta ba to mijinta, amma Malika bamu san gidan su ba fa?" kallon Amara Malika tayi tace
"Kina so a kaiki wajansa?" da sauri ta hau gya ɗa kai,
"Kin san inda zamu samesa? ina nufin zaki gane gidan naku?" shuru Amara tayi tana mai ƙurawa Malika ido, Saima tace
"Wannan fa duk bata lokaci ne Malika, kawai muyi shirin zuwa abuja idan yaso ba mamaki idan ta ganmu a abujan ta tuna da wasu abubuwan watakila ma har da gidan nasu"
"Kuma haka ne fa, to yanzu kawai mu shirya tafiya abuja"
"To yaushe kenan zamu tafi?"
"Ai ina ga mu tafi gobe kawai domin da zafi-zafi ake dukan karfe, kafin nan zanyi magana da Aahil na sanar da shi sai naji abinda zai faɗi" Saima ta jinjina kai, ranar Amara kuka ta sha tana rungume da system, bayan an gama hira da Deen inda ya bada labari da cewa tsautsayi ne kawai da ajalin abokan aikinsa ya riskesu shi kuma Allah ya kaddara da kwanansa na gaba Allah ya tseratar da shi.

🧜MAMIYOTA CE🧜Where stories live. Discover now