Ƙ page 71

205 44 4
                                    

*ƘADDARAR RAYUWA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡

Written by
              zaynab bawa
#Follow me on
              wattpad@zeeyybawa."

Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200

Page 71

  Wata iriyar kwala ya challa wanda yasa Sadam dake ƙoƙarin shigowa faro saurin neman ɗakin dayakejin ihun,

Da gudu Sawwama ta ƙarasa wajan ta ɗagoshi ya buga kansa jikin drawer sai jini yakeyi gashi ya shuɗe harcensa har ɓari yakeyi saboda azabarda yakeji arikice Sawwama ta ɗagoshi tariƙe ajikinta,

Its kanta Abida saida ta rikice ganin yanda jini yake zuba, dasuari ta ƙaraso wajan takai hannunta zata taɓa yaron Sawwama cikin zafin rai ta buge hannun,

  Miƙewa tayi da yaron ajikinta tana niyyar Abida abida tabita itama arikice tana shirin ƙara taɓa yaron Sawwama ta juya a zafafe ta wanke fuskar Abida da mari hakan yayi dai-dai da shigowar Sadam ɗakin, Sawwama na kuka ta raɓa gefensa zata wuce, a ɗimauce ya tsaida ita ganin jini duk ya ɓata kayanta ga Hamdan dake ta tsala ihu a hannunta,

Hannu yasa ya karɓeshi yayi wane da gudu sukaci karo da mummy wacce take shirin shiga ɗakin jin yanda ihun yaron yayi yawa,

Gabaki ɗayansu suka wuce zuwa asibiti banda Abida da aka bari a gida, jinin ya tsaya an yinasa inki kamu uku a wajan sai aka rufe da bandage ana gamawa aka sallamesu, Saida Sadam yayita rarrashin Sawwama kafin ta yarda aka koma gidan mumny da ita, Abida kuwa ido yayi tsuru-tsuru daowarsu kawai take jira,

Sun koma alokacin dady shima ya dawo, anata jajantawa dady yace har ya akabar haka tafaru, mummy wacce kamar tana wajan abun yafaru tacewa dady ai yaron dama yamada ƙiriniya kuma sands nacewa uwarsa ta kula dasu tashiga ciki tabarsu yaje yajiyawa kansa ciwo,

Dady yace subhanallahi Sai kidinga kula idan Allah yabaka yaro irin haka takatsantsan akeyi, hawayen take zuba a fuskar Sawwama, Sadam yace banajin hakane tafaru dady dan makamancin hakan baitaɓa faruwa ba Sawwama ya akayi haka?

Sawwama wacce take kuka ƙasa-ƙasa face nashiga toilet yin alwala fitowana naga Abida ta sanya ƙafa ya wullashi gefe, Sadam yace jikina yabani hakan saboda nasan Sawwama da wuya tayi zafin zuciya irin haka batareda wani kwakkwaran dalili ba,

  Mummy ta dubi Abida tace ya akayi haka tafaru? Ke kika tureshi, da sauri Abida ta girgiza kai tace bani na tureashi ba mummy zuwa wajan yayi ya buge ita kuma tana zuwa sai tahau kaina harda marina atunaninta ni nabige mata yaro, tayi maganarne cikin rashin gaskiya wanda dady da Sadam sun fahimci hakan amma mummy son kai ya rufe mata idanuwa,
A fili ta furta mari! ta mareki akan yaron dan tana hauka,
  Dady yace dakata kamar yanda bamunan Tature yaron haka bamanan itama ta mareta so acikinsu mu ɗauka cewa kowa yafaɗi son ransa ne abarsu ahaka bbu wacce zaki zauna akan maganarta kiyiwa ɗaya faɗa idan hakane dukansu haɗasu zakiyi ki musu faɗa ita ta wulla mata yaro itakuma ta mareta,

  ke kuma ya nuna Abida har indai kinsan kin wulla yaronnan kiji tsoron Allah shi yaro ba'a masa mugunta dan gaba bakisan wazai taimakeki ba, yaro baisan komai ba, har indai ya tabbata kin tureshi to tabbas baki kyautaba dan wannan abun ko ƙara takaiki mu bazamuga laifinta ba dan kinyi ba dai-dai ba,

  Mummy tace dadynsu ba'a an tabbatar ta cewa ita tatureshi ba amma kanata yimata faɗa, its wacce ta mareta ai itama yakamata kayi mata faɗa tunda gashi har shatin hannunta yafito a fuskarta ta faɗi tana juyoda fuskar abida wanda take kumbure da marinda Sawwama tayi mata"

ƘADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now