K page 94

233 51 9
                                    


*ƘADDARAR RAYUWA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡

Written by
              zaynab bawa
#Follow me on
              wattpad@zeeyybawa."

Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200

Page 94

    Kanta yana kasa tashiga wajan Can gefe tazauna ta gaida mutanen ciki cikin girmamawa mai martaba yace abasu waje dama tun kafin yafada wasu daga ciki sun fara barin falon,

Bayan kowa yabar Falon yadubi Sawwama yace "Hafsa Sawwama ta sake nutsarda kanta a kasa kwarjini da cika idon wannan Dattijon ya hanata dagowa ta kalleshi saida yasake kiran sunanta ta amsa cikin nutsuwa, mai martaba yace "dago ki kalleni magana zamuyi har lokacinma takasa kallon nasa hakan yasa yayi murmushi irinna manya sannan yafara magana,

Nasan ta iya yiwuwa kunyi magana da Yata ta sanar dake batunda nazo matadashi jiya amma inaso na sake jajjada zancena nazo na nemawa jikana aurenki,

Nasan zakiyi mana kallon masu son zuciya mutanennda zakafi son kansu fiyeda kowa abun bahaka yakeba,

Dalilin faruwar wannan lamari bayan zuwanki bayan tafiyarki kuma ciwo yasake dawowa muna saka rai in Allah yayarda za'a samu waraka daga gareki,

  Zakiga kamar munason aura miki wani mutum daban, Mai martaba yayi dariya Na manyan mutane sannan yace "Abun bahaka yakeba a zahirin gaskiya bantaba cin karo da wani mutum irin yareema ba A hali da komai ana cewa mutum tara yake bai cika gomaba amma fa inada tabbacin Idan Allah yabawa yareema lafiya kika zauna dashi zakice shi yacika goma,

Idan kika amince da wannan auren Allah yabawa yareema lafiya zaki kasance kullum kina min addu'a saboda hada wannan al'amari danayi,

Yareema mutum ne wanda cikin dubu samunsa ba lallai ba zaki iya tara miliyoyin mutane baki samu daya kamarsa ba, bani kadai na shaida hakanba duniya ya shaida mutanenda suke taredashi sun shaida,

Yareema mutum ne Yareema mutum ne kwarai dagaske Allah ya hadashi da jarabawa daciwo wanda bamusan menene ba,

Amma zuwanki munga canjin Al'amari harmun fara gano bakin zaren Yareema yayi magana radau yanda kowa zai fahimceshi,

    Tsawon Awa biyu suka dauka Mai martaba yana bata labarin Yareema da yanda yake tafiyarda rayuwarsa yanda yake mu'amala da mutane tanata mamaki shin dama za'a samu mutum irin haka?

Mai martaba yayi murmushi ganin yanda jikinta yayi  sanyi yace "kadan daga cikin halayansa kenan na fada miki saikin zauna dashi zaki tabbatar abunda na fada miki yafi haka, dan inaji ajikina yakusa samun lafiya,

Nisawa kawai tayi batace komaiba amma cikin ranta tana mamaki dama Sarakuna suna sakewa haka suyi magana?

Kodai dan ita yana neman wani abun wajanta ne?

Mai martaba ya daura da fadin ina neman alfarma a wajanki da ki amince da wannan auren in sha Allahu zai zame mana alkahiri gabaki dayanmu, amma yanzu zan baki lokaci kiyi tunani tunda anzo abun a kurarren lokaci kiyi shawara da mahaifanki naso nagansu amma Mahaifin Abubakar (Alhaji) yace "abari sai kin amince tukunna samau mahaifanki nima na yarda da hakan domin abi komai a ka'ida yafi kinada dama da ikon da zakice baki amincewa wannan aurenba amma ina neman alfarmarki akan ki amince in sha Allahu duniya gabaki dayanta sai tayi alfahari da wannan auren,

Sawwama ita dai batace komaiba amma jikinta yayi sanyi,

  Bayan yagama ya bukaci Alhaji da Hajiya su shigo ciki suka zauna kasa kamar yanda Sawwama take a kasa, mai martaba yace "mungama magana amma nabata lokaci tayi tunani duk abunda ta yanke saita sameki ya nuna Hajiya ta fada mikk idan yaso maji Allah yasa muji Alkahiri su duka suka amsa da amin  banda Sawwama,

ƘADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now