K page 85

232 55 7
                                    

*ƘADDARAR RAYUWA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡

Written by
zaynab bawa
#Follow me on
wattpad@zeeyybawa."

Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200

Page 85
     Abaya mummy tabi dady har dakinsa yasan da shigowarta amma yanuna kamar baisaniba saida yagama duk wani abunda zaiyi yayi alwala yafice masallaci hakan yasa bata samu damar yin magana dashiba,

Bai dawo gidanba sai isha'i saida tabari ya huta sannan tace "dadynsu inaga kaman bai kamata abasu yarannan sutafi dasuba tunda bamusan irin rikon da mijinnata zaiyi musuba kuma muma nana zamuyi kewarsu ba kadanba sune suke debe mana kewar rashin magaifinsu akusa damu, zamuyi matukar kewarsu kusan kowa agidannan yasaba da yaran,

Dady yayi kamar baijita sai can harta cire rab cewa zaiyi mata magana sai taji yafara fadin "shin ba yayanta bane? Ashe munada ikon da zamu hanata tafiya da yaranta? Tundaga kanki nadauka cewa uwa tafi kowa iko akan yaranda ta haifa idan nabarsu suntafi ba komai bane tunanima nakeyi har indai mijinta zai yarda zan bar mata yaranta gabaki daya har sai ranarda mahaifinsu yadawo yaji zai amshi yaransa saiya karbesu bana tunanin daga yanzu zasu kara zama agidannan saboda itama mahaifiyarsu tanada bukatar yaranta,

Yaranta ne itace takeda iko dasu kamar yanda kike gwadawa kinfi kowa iko akan yaranki toh nima nabata wannan damar akan yaranta zatafi kowa iko dasu ko mahaifinsu idanna sanar dashi hakan banaji zaija da maganata,

Kuma ni zamansu atare dake hankalina sam bai kwanta bakison mahaifiyarsu suma bai kamata ki sosu ba ko barmata kayanta a wajanta inada yakinin zata basu kulawa ba irin kulawarda ke kike bawa yaranki ba, kibar uwarda ta haifesu tataso da yaranta a yanda takeso tayi iko dasu yanda takeso na fada na nanata babu wanda zai karbo yarannan idan itama da kanta ta dawo dasu zanji cewa tanason rikesu? Idan tanaso nabata abunda tatafi dasu,

Mummy tace "dadynsu dan Allah karkayinun haka Wallhy inason yarannan jinin Sadam nefa tayaya kake tunanin zan kisu kona cutar dasu? Kuma tayaya zasu zauna a gidan mahaifinda banasu ba? Bayan nasu mahaifin yana raye idan akayi haka ba'ayiwa yaran adalci ba,

Tabe baki dady yayi yace "bana tunanin kina a stage din da zakiyi magana akan yiwa yara adalci ko akasin haka, kinsanda cewa idan uwarsu bata tare da mahaifinsu gidan wani zasu rayu kika raba auren adalci da za'ayiwa yara yanzu shine abarsu su rayu da mahaifiyarsu har lokacin da mahaifinsu zaiso karban yayansa, kuma kidaina nunawa cewa ke masoyiyar yarannan ne saboda suka girma sukaji abunda kika aikata bazasu taba sonki ba sai tsana da zai shiga tsakaninku, zasuji haushinki akan abunda yafaru da mahaifansu,

Bazasu zauna awajanki ba bare kiyi tunanin kyautata musu da wanke abunda yafaru abaya, gara su taso da sanin abunda kika aikata awannan lokacin ima tunanin zakiji kunya kisan kin aikata ba dai-dai ba,

Mummy jiki babu kwari ta mike ayanzu tafara gajiya da irin bakaken maganganun da dady yake yaba mata akowani lokaci duk abunda yafito bakinsa fada mata kawai yakeyi, shin wai baya tunanin cewa itama tanajin zafin wannan al'amarinba?

Baya tunanin cewa itama yanzu ta gyaru tanaso suyi zaman lafiya? Shekara harda watanni da faruwar wannan al'amari amma ko gobe magana tatashi sai dady ya fada mata bakake."

Sawwama yau tana cikin farin ciki suna yaran kansu walwalarsu ayau ta dabance sai zagaye sukeyi suyi nan suyi can suna wasa da kaninsu dake kokarin fara rarrafe,

Saida sukayi suka gashi Sawwama tayi musu wanka dukansu da kwantar dasu dake sun gashi basu dadeba bacci ya dauketa ta zauna tana jiran dawowar Abubakar dan yau ya faranta mata matuka itama zataso ta rama masa wannan alkahirin da faranta masa,

ƘADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now