Q page 12

761 106 8
                                    


*QADDARAR RAYUWA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Haske writers association💡

Writing by
Zaynab bawa

Follow on wattpad@zeeyybawa

           Page 12

Jikin sawwama yayi sanyi sosai har yakaiga ta gagara aikata komai hakan yasa ta aika aka kira mata halima,

Halima ce taqarasa awaran ita kuma tashiga ciki,
Mama tayita yambayarta ko wani abunne yasameta amma sai sawwama tace mata batajin dad'ine kawai,

Tagaji da yawa,
Sannu kiyi sallah kikwanta dawuri mama tafad'i,
Toh sawwma tace tashige d'aki,

Tayi juyin duniyarnan tarasa mai yake mata dad'i menene dalilinta na damuwa danta fada masa gaskiya tafara tuhumar kanta, bacin randa kika gani shimfid'e akan fuskarsa shine dalilin damuwarki,
Zuciyarta tabada amsa,

Rass rass gabanta yahau faduwa, wani irin Tuquqin baqin ciki takeji, dukda cewa bawai wasu magana mai zafi tafad'a masaba amma ta tsinci kanta da jin zafin kalamanta agareshi,

Taso ace alaqarsu ta tsaya ahaka ayanda suke baya-baya,

Hakan yanayi mata dad'i domin har nishad'i take samun kanta aciki amma inaa,

Yazo gabaki d'aya yau yana neman tarwatsa mata wannan nishad'i data dade tanajin kanta aciki, yana neman ruguza mata dan farin cikinda take ciki,

Ruwa taji yana gangara akan kumatunda mai d'umi da dukkan alamu hawaye ne yake gangarowa daga idanuwanta,

sanya hannu tayi ta share hawayen,
Wata zuciyar tana son lallashinta da fad'in menene naki na kukan??

Wace magana mai zafi kika fad'a? Iya kacin gaskiyrki kika fada kuma hakanne dai-dai,

Sannan shima kuma babu wani mummunan abu daya fad'a kokuma alamun nuna cutarwa agareki,

Cikin wannan halin tadauki lokaci mai tsayi,

Tana kwance kunnuwanta suka fara jiyo mata sautin kiran sallar magrib,

Miqewa tayi jikinta duk babu qarfi tashiga cikin gida,

Ganin fitowarta ya sanya mama fad'in badai jikin bane har yanzu?

Yatsine fuska tayi tace wallhy,

Cikin tausayawa mama tace sannu yanzu kiyi sallah saiki kwanta dawuri harda gajiya ma a alamarin idan kinyi bacci zai wartsake in sha Allahu, idanma bai wartsakeba zuwa gobe sai anemi faracitamal amma in sha Allah zaima wartsake d'in,

Toh sawwama tace sannan ta dauki buta ta nufi bayi alwala tadauro ta gabatarda sallar magrib,

Tazauna Jiran isha'i kafin ashiga sallan isha saiga babansu yadawo,

Sannu da zuwa mama tafad'i ya amsa da yawwa bayan yakai wheelbarrow dinsa dan kangon d'akinda yake ajiyeshi ya ajiye,

Kusada mama yazauna yana fadin bismillahi, sannu mama tayi masa,
Suma duka yaran suka bishi da sannu ya amsa sannan mama tace barina kawo maka abunci,

D'aga hannu yayi yace A'a dakata bari nayi sallar isha'i tukunna,

Toh mama tace sannan takoma ta zauna sannan ta dubeshi tace baban sawwama yau kayi dare awaje,

Wallhy nayi nisan zangone baba yabata amsa kinsan abubuwan sai ahankali hakane mama tafad'i,

Baba ya kalli sawwama yace" mamana lafiya kuwa?

ƘADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now