Sulaimi

13 7 2
                                    


Dedicated to antulma thank you for being a sweetheart, Jannah loves you!


"Ban fahimce ki ba Mama, wani irin zance kike min?!" Cike da tsananin fushi da daurewar kai Ashir yayi maganar yana me neman karin bayani a wajen Hafsa.

"Cewa nayi, zaka auri Hauwa'u!". Wani banbarakwai yaji zancentan. Shi da yake ta faman tsara rayuwar shi, cikin rahamar Allah yana kokarin gyara kurakuren shi kuma mahaifiyar shi take kawo mishi wannan zance mara fasali.

"Aure kuma Mama? Toh ni shekaru na nawa ne a duniya da kike min maganar aure? Ko 23 ban cika bafa!" Wani irin kallo Hafsa tayi mishi cike da bala'i tace "ban gane shekarun ka nawa ba? Kai yanzu ba zaka rike mata hud'u ba? Da a kauye kake da kana da 'ya'ya!".

Numfashi Ashir ya fuzar yana rike da kan shi da ya fara wani irin ciwo. "Mama dan Allah ki kyale ni in yi establishing goals na. Ina da buri dayawa, kuma rayuwan kauye da birni ai ba daya bane!".

Tsaki Hafsa ta ja " dan Allah ka ji ka! Wani irin magana kake Ashir? Auren ne zai hanaka cika burin ka? Kana magana kamar wani yahudu! " Ganin ba kula shi Hafsa zata yi ba yasa ya runtse idanu, yana me neman nutsuwa, dan gaba daya ta jagula mishi lissafi.

"kayi wa kanka fad'a Ashir dan ni ba zan dai shiriritar ka ba. Kuma zan yi magana da gidan su Hauwa'u, a maka izini ka fara zuwa zance wajenta". Cikin wani irin bacin rai da dacin zuciya yace " wace Hauwa'u?".

Murmushi Hafsa tayi tace " Hauwa'u yar kawata Saude mana--!". Ashir bai saurari karshen zancenta ba yace " inna lillahi! Haba Umma ba dai wan can kazamar yarinyar ba! ".

Salati Hafsa ta saka tana tafi tace " lallai Ashir, wuyar ka ta isa yanka. Yanzu a gaba na kake zagin 'yar aminiyata? "

Tsunkuyar da kai yayi da karamar murya yace " ki yi hakuri". Sai kuma can ya kara da cewa " amma gaskiya bazan iya auran Hauwa'u ba. Ni ina da wanda nake so".

Shiru Hafsa tayi na dan lokaci sannan tace "wa ce ce ita?" Shafa wuyar shi yayi yana me jin kunya yace "Kin san ta fa Mama, ba kowa bace illa Rahama". "Wa ce Rahamar?" "Rahamar Uncle Al'amin mai rasuwa, Yayar Jannah".

Da kyar Hafsa ta iya shanye farin ciki ta, dama tayi hakan ne dan ta gano yana son Rahama. Kuma tafi so ace shi ya fito fili ya fad'a mata. Wayancewa tayi ta wani had'a fuska tace "Rahamar gidan nan?". Nan ma kai ya gyad'a yana addu'ar Allah yasa ta amince masa.

"Amma ni Hauwa'u nake so ka aura?". Kamar zai yi kuka ya d'ago yace " Mama dan Allah ki min uzuri, ni wallahi bana son ta. Ina zan kai wancan yarinyar? Ko magana fa bata iya ba. Sa'ar su Asiya ce fa, she's barely 15".

" Ka ga ni bana son shiriritar, na fahimci yanzu ba kula ni zaka yi ba, na baka nan da sati daya ka yanke shawara". Da sauri Ashir ya amsa da " toh" sannan ya mike ya nufi dakin sa, dan ko kad'an baya son sake sauraronta.

Murmushi Hafsa tayi, ganin ya nufi dakin sa. Farin ciki sosai take yi, ganin komai yana zuwa mata da sauki, saura kad'an ta aiwatar da abin da take so. Yanzu saura Abdul in nan ne zata yi maganin shi.

Tana nan zaune tana sake-saken ta har Ya Umar Ya shigo. Kallon shi tayi da gani a gajiye yake, ba dan ta so ba ta mike tayi mishi sannu dazuwa. A kasalance ya amsa ta.

Kitchen ta nufa dan ta dauko mishi abun sha, duk da cewa akwai fridge a palor din- sanin cewa baya shan abu me sanyi. Nan ta tarar da Aisha, yar aikin su tana waya. "Haba mana barrister, please ka daina fad'an haka, ai ciwo ba mutuwa bane zan zo in duba ka a asibitin in sha Allah. In kana fad'an haka zuciya ta baza ta iya dauka ba-".

Bata karasa zancen ta ba sakamakon marin da aka sauke mata a gefen fuskarta. A razane ta juya, tuni wayar ta sullube daga rikon ta. Idanunta ne suka cicciko ganin Hafsa ta sake d'aga hannu ta sake wanka mata mari a karo na biyu. Wani irin takaicin ne ya mamaye mata zuciya.

ILLAR MARAICIWhere stories live. Discover now