Makirci

17 9 2
                                    

Har aka tashi a school Zynat bata kula Talib ba, ta dai ga shigar shi aji da kuma wucewar Jannah. Amma tun da nan bata sake kallon shi ba. A lunch break ma sanin cewa Talib baya zama a canteen sai a school garden yake cin abinci yasa taje canteen cin abinci dan ko kad'an bata so su had'u da shi, dan haka kawai wani irin haushinn shi take ji.

Ana closing school tayi saurin fia ta nemi taxi ya kai ta gida, bata jira Talib ba kamar kullum kuma da yake school friend dinta ba bata zo ba yasa abin yazo mata da sauki. Dakin ta ta shiga yayin da idanun ta suka ciko da kwalla. Jakarta ta jefar tayi kuka iya son ranta, wanka tayi, ta zura evening gown dinta, hula ta sanya ta rufe gashin ta dashi.

Sallama tayi ta tura kofan dakin Ummi, zaune ta same ta bisa gado, tana ganin photo album. Ummi na jin muryar Zynat ta fara murmushi, nan Zynat ta rungume ta. "Har kin dawo?" Gyad'a kai tayi ba tare da ta d'ago kai ba. Ganin haka yasa Ummi ta hau shafa kanta tana patting bayan ta.

Kuka sosai Zynat ta saka, tana me jin wani irin radadi a ranta. Wannan  rayuwa da me tayi kama? Ummi bata ce mata komai ba illa rarrashin ta da take yi. A haka Zynat tayi bacci a jikin Ummi.

Gyara mata kwanciyar ta tayi sannan ta kara karfin AC din. Tana me nazarin abin da ya sami Zynat da har take kukan haka. Ko dai abin da take tunani ne? Girgiza kai tayi ta dauko carbi ta fara adhkaar.

*

Hankalin Talib in yayi dubu ya tashi, zuciyar shi sai bugawa take sakamakon rashin ganin Zynat. Duk da cewa tayi attending duka classes din, ko da taje school garden din a lunch break dan cin abinci bai ganta ba. Hakan yasa ya kasa cin abincin, barin ma da ya tuna kukan da tayi yau da safe.

Haka zalika da aka yi closing school ma, ko kad'an bai ganta ba, kuma abokiyar tafiyar ta ma bai gani ba. Duk wani lungu da sak'on school din sai da ya duba, amma babu alamar ta. Hatta securities na school din ya tambaya sai dai basu gane ta ba dan Zynat ba mutum me hayaniya bace. Har ya dauki hanyar police station wata zuciyar tace ya kira Ummi ya tambaye ta dan wayar Zynat baya shiga.

"Ummi, Ummita ta dawo gida ne?" A takaice Ummi ta amsa shi da "Eh". Hamdalah ya saki, nan yaji kamar an dauke mishi nauyi a kai. Yana isa gida ko parking me kyau bai yi ba ya nufi dakin Ummi. Da sallama ya shigo. Wani irin ajiyar zuciya ya sauke ganin Zynat na bacci a gefen Ummi.

"Ummi ina wuni". Sama sama ta amsa gaisuwar shi babu dakin fuska. Nan da nan jikin Talib yai san yi, dan ko kad'an baya son fushin Ummi. Matsowa yayi gabanta ya rike yatsun ta, cikin lallami da sanyin murya yace "Ummi, kuyi hakuri in na miki wani abun".

Hannun ta ta zame daga rikon shi, fuskarta babu alamar wasa tace " Abbati me kayi wa Ummita?" Kallon Ummi yayi cike da confusion yace " Ummi ni kuma?". Ganin wani irin kallon da tayi mishi yasa yayi saurin kada kai, yana kokarin tuna abin da yayi mata. Toh ko dai tambayar da yai mata dazu da safe ne?.

"Ki yi hakuri, Ummi. Ban sani ba, amma in sha Allah zan gyara idan ma ni na bata mata". Gyad'a kai Ummi tayi sai dai bata ce komai ba duk da cewa ta gano bakin zaren. Tamkar yar cikin ta ta dauki Zynat kuma bata ta so a ce Talib yana bata mata saboda Jannah ba. Haka zalika baza ta tilastawa Talib Zynat ba, in tayi hakan bata yi musu adalci ba. Gara ta bar wa Ubangiji Allah SWT komai, shi ne masanin daidai.

"Don't lose diamond in search of  gold! ka bud'e idon ka Talib! Kar ka saki rashe ka kama ganye". Cike da tsananin rashin fahimta Talib ya kalli Ummi, ko kad'an bai fahimci zancen ta ba.

" Ummi, ban fahimce ki ba". Girgiza kai Ummi tayi, sannan ta jingina da jikin gadon. Ba tare da ta bud'e ido ba tace " kaje ka huta, Abbati". Jiki a sanyaye Talib ya mike ya fice a dakin yana sake sake a cikin ransa.

*
A kwana a tashi har term ya kare an yi exams a school dinsu Jannah. Sosai aka yi mamakin ganin results, as usual, Jannah ce tazo first, Talib kuma second alhalin shine kullum yake zuwa overall first position, sai dai wannan karon ba Zynat ce tazo second ba, ita ce 5th position. Sosai abin ya daure wa kowa kai, Zynat Bashir bata taba wuce second ba.

ILLAR MARAICIWhere stories live. Discover now