"Baba!..." A razane Jannah ta saki kara yayin da goshinta ke zubar da gumi. Nishi take jikinta yana rawa ta kasa koda daga kanta.
Karo na uku kenan da Jannah take mafarki mara dadi da mahaifinta. Sai dai na yau yafi na ko yaushe ban tsoro dan gawan mahaifinta ta gani rufe da farin kyalle.
"Firdausi you okay?" Talib wani dan ajinsu ya dafa kafadarta yana tambaya dan ya fahimci ba a cikin hankalinta take ba.
"Huh! I..I...I'm okay Talib'' ta kada kanta. Sai a yanzu ta fahimci a class take. Ajiyar zuciya ta sauke tana me rokan Allah ya kare mata Babanta.
"Jannah you had a dream" Talib ya fada cike da damuwa. Kallonshi tayi sannan tai saurin sauke idanunta. "I'm okay Talib''
Shiru sukayi na tsawon lokaci ba tare da sunce komai ba. A hankali Jannah ta daga idonta tana kallon yanda yan ajin suka zuba musu ido.
Bata yi mamaki ba dan Talib' shine heart-throb na class din ya kasance someone cool with easy going nature duk dacewa gidansu suna da kyau da arziki
Kula Jannah da Talib keyi yasa matan class din suke jin haushinta. Ga kyau ga ilimi ga Kuma Talib da kullum yake tare da ita.
Mazan kua kowa na son winning heart dinta sai da it's not easy dan wani Karo da wani Tahir yace yana sonta dukan bala'i ta mishi.
Suna nan a haka Mr Frank ya shigo ya fara musu Economics da a da ne da tayi tsaki dan duk sunyi a school ko a lesson.
Amma yau shiru tayi dan ko kadan bata san me yake fada ba. "I'm asking you Miss" muryar Mr Frank ne ya dawo da ita daga duniyar tunaninta.
Shiru tai dan bata san me ya gama fada ba. "You weren't listening" ya sake magana. Sunkuyar da kai tai tana wasa da yatsunta.
Hakan ba karamin batawa Mr Frank rai yayi ba "out of my class" yayi mata pointing kofa. Ko kadan bata ji haushi ba dan ta ma rasa me yake mata dadi.
Cikin sanyi da fice daga class din tana tuanani. Ba da jimawa ba aka yi ringing bell na break nan kowa ya kama harkan gabansa banda Jannah da ta dawo class ta zauna.
Share hawayenta Jannah tayi wanda bata san yaushe ta fara ba. "What is it Jannah" Talib ya sake tambaya wanda hakan yasa Jannah kuka.
Shiru yayi ya barta har sai da ta dena kuka sannan ya bata hanky ta share hawayenta. "What is it Jannah" cikin kuka tace "Talib m..m...my dad"
________________________________
________________________________"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!.." hakan ba karamin tayarwa Sumayya hankali yayi ba. Ka kuma kukan da Umma take yi. Cike da tashin hankali Uncle Abdul yace "What is it Umma" cikin rikewan numfashi tace
"Ahmad. Abdul Ahmad ya tafi ya barni Allah yayi mishi rasuwa"
Cak kafan Sumayya ya bar motsi kasa aikata komai tayi yayin da kwakwalwarta yake processing abin da taji cike da tashin hankali tace
"No...it...can't be my Al'ameen is alive he.. he can't lea-" kasa karasa magana tayi dan wani wawan jiri da ya dauketa. Luu tayi baya ta fadi. Hakan yasa ta fara rolling daga kan steps din.
Dai dai nan Rahma ta shigo da sallamar ta sai dai kara ta sako sakamakon ganin Sumayya da ke fadowa daga saman beni ga Kuma jin dake bin kafafuwanta.
"Antyyyyy!!!!..." Rahma ta tsala ihu...
•
"Relax Jennah he's okay" Talib ya fada yana kallon Jannah. Girgiza kai ta shiga yi tana cewa "No Talib he isn't fine. I've been having nightmares about him"
Shiru Talib yayi na dan lokaci hade da jan numfashi. "Come let me take you home" ya fada yana mikewa "Talib-" Jannah tayi kokarin rejecting offer dinshi
YOU ARE READING
ILLAR MARAICI
RandomTa kasance sanyin idaniyar iyyayenta. Sanadin farincikinsu, dalillin jin dadinsu kuma 'ya kwalli daya ga attajirai biyu. Yaya rayuwarta zata kasance idan ta rasa dukkansu biyu? Follow the bittersweet emotional rollercoaster life of Jannah. A little...