Yau sati d'aya kenan da zuwansu Nigeria gashi kuma Ummul Khair zasu koma gidansu dake Abuja. Dama k'arasa sauran hutun suka yi a Kaduna.
Tun safe Jannah ta ke ta faman had'a rai ita a dole kar su Ummul Khair su tafi saboda tsananin shakuwar dake tsakanin ta dasu Asiya da Mufida. A cikin satin ma su Hamza, yayansu Zara suka zo da matansu. "Abbul khair dole ne ku tafi a yau?" Jannah ta zumb'ura baki idonta cike da hawaye.
"I-I don't want you to leave" sai kuma ta fara kuka. "It's okay Jannah you don't have to cry baby, we'll soon come back" Ya Majid ya share mata hawaye. "It's not okay". Ta sake fad'a. Da haka ta mike da bar wajen tana kuka ba tare da ta kula da inda take jefa kafanta ba.
Ji tayi an rike mata hannu wanda hakan yasata saurin juyawa. Baki ta wangale tana k' allon ikon Allah. Ashir ne ko Abbas nema baza ta iya fad'a ba tunda ba wani saninsu tayi ba. "Me haka Ashir? Let go" ta fad'a tana kokarin kwace hannunta.
"Come on baby Abbas ne fa ba Ashir ba. Let's have fun mana" kasa magana tayi tsabagen mamaki. "Dalla ka sakar min hanu" "in naki fa?" sai kuma ya sake tamke hannun. Ba tare da tayi magana ba ta kafa mishi naushi wanda yayi sanadin fasa mishi baki.
Ai ko da sauri ya sake mata hannu yana cewa "ni kika nausa?" "this is just the beginning" ta furta tana hararanshi. Ita ko a school ba'a raina ta ta bari dan da maza take gabzawa. Hakan tasa ma ko a sport ita ce football and basket ball star dinsu. Dan kap football team dinsu ma mata uku ne.
Ita da badan taka mata birki da Sumayya tayi ba da ta yi nisa cikin boxing saboda tayi joining na yara tun tana ten. Watanta biyu aka hanata a gida. Murmushin bakin ciki tayi wai wannan yaronne zai gwada mata fin karfi?.
A hanyar dawowarsu daga Airport Hafsat ta tambayi Abbas abin da ya sameshi. Kallon Jannah yayi tare da cewa fad'iwa yayi.
"Ke Jannah me haka?" Hafsa ta doka salati tana kallon Jannah dake cin kwai. "Fried egg" ta amsa a takaice. "wannan ne fried?" Hafsa ta nuna kwan da bai gama soyuwa ba.
"wai what's your problem ne Aunt Hafsat? Ni fa nake cin abuna not you. Ni haka nake ci a gidanmu" tayi karamar tsaki. Had'e da kora milkshake dake gefenta. "A hakan?" Hafsat ta sake tambaya kamar wata wawiya "toh so kike inyi roasting?" Jannah ta dage gira tana jiran amsa.
Dai dai nan Rahma ta shigo fuskarta dauke da murmushi. "thanks" ta fada yayin da Jannah ta sa mata kwai a baki. A hankali dining din ya cika da mutane. Cike da murmushi Jannah ta dauko Frittata da Sumayya tayi tana murmushi
"Shikennan mutum ta ringa cin kwai kennan?" Umma ta tambaya. Shareta Jannah tayi ta dauko waffles dake gaban Uncle Abdul.
Shiru Hafsat tayi dan ta ma rasa me zataci hankalinta ya kwanta a ganinta duk kayan tashin hankali ne. Can da taga babu sarki sai Allah ta rufawa kanta asiri ta dauki omelette da daya daga cikin crepes da Umma ke ci.
Dan tasan ko zata mutu Abdul baze bata French toast da yake ci ba. Sumayya zaune a daki Rahma suka shigo tare da sallama. Da fara'arta ta amsa hade da basu wajen zama. "Mummy?" "Na'am habibti kaifa haluk?" "bikhairin wal hamdulillah" Jannah ta amsa "wa inti habibti?" "ana bikhair shukran".
Shiru sukayi tsawon lokaci kafin Sumayya ta sake magana. "What is it babies?" "Mother i don't know how to start. But what you did that day at Toronto International Airport was so scary" shiru Sumayya tayi hade da jan numfashi.
"It's a tale for another day". Tana fadan haka ta kau da kai. Canza hira sukayi har sai da akayi azahar.
Nan kuma Umma ta fara masifar wai sai su Rahma da Jannah sunyi tuwo. Da taimakon Sumayya da masu girkin sukayi komai sai dai in banda Umma da Hafsat da mijinta da 'ya' yanta babu wanda ya iyaci.
Garama Baba da ya lallaba dan rabonshi da cin abincin Nigeria har ya mata. Sai yaji daga wanda yayi gishri, sai wanda yayi mai ko yaji. Ita dai Hafsat sai gyada kai take alamar abinci yayi dadi. A hankali Sumayya ta ke tura abincin. Jannah kuwa sai faman tsaki take yi.
A haka suka karasa hutun sai kuma suka fara shirin tafiya. Duk da cewa kullum cikin fada suke, Umma sai da taji ba dadi da su Jannah zasu tafi. Itako Jannah Allah Allah take su tafi san tun tafiyarsu Ummaul khair garin Kaduna ya isheta. Hakama Rahma.
A kwana a tashi har shekara ta zagayo. Rayuwa na tafiya dai dai kamar babu wata matsala. Jannah kam farin ciki kamar ya kasheta dan watanni bakwai da suka wuce Sumayya tayi ta rashin lafiya wanda cikin ikon Allah a ka gano cikine da ita.
Ba su kadai ba hatta Umma sai da tayi murna duk da cewa da tsani Sumayya. Jannah na zaune a gaban Tv Rahma ta daure mata ido hade da futar da ita daga dakin. A palour ta zaunar da ita hade ba bude mata ido.
Zaro idanu Jannah rayi tana karewa katon red and white cake dake gabanta. Congratulation on your monthly circle. Ta karanta cike da mamaki. Ita idan ba yanzu bama bata san ta kai shekara daya da fara al'ada ba. 'Big sis-" sai kuma ta fara kuka." shhh angel don't cry. You'll always be my baby sis.". Sumayya dake bakin kofa tayi murmushi tana me sa musu albarka.
Da kwana biyu kenan Rahma tayi graduating secondary school. Sake siya mata gida da mota akayi hade da hutun wata daya a countries biyar. Anan kuma Umma ta fara kira tana tuna musu alkawarin da sukayi na dawowa Nigeria gaba daya tunda Jannah ta gama SS1 Rahma kuma ta gama Secondary school.
Babu yanda suka iya haka suka fara shirin dawowa tare da processing komai na zamansu a can. Ba tare da sanin tashin hankalin da zasu tarar ba. Tashin hankalin da zai canza musu rayuwa gaba daya.
Dawowansu Naija suka sauka a Abuja. Yini sukayi tare da su Ya Majid kafin suka koma sabon gidansu. Kwanansu biyu Umma ta matsa musu da su dawo Kaduna. Ba yanda be yi da ita ba amma taki. Ganin babu sarki sai Allah yasa suka koma Kaduna.
Ko da Ahmad ya ma Umma maganar siyan gida, cewa tayi sai dai su zauna da ita tare da su Hafsat tunda dama apartment hudu ne a gidan wanda an gina ne saboda su. A nan aka ma Jannah registration na SS2 aka kuma yi wa Rahma applying University.
Zaune suke cikin make'ken palour kowa na abin gabanshi. As usual, Jannah tayi staining fuskarta da red velvet ice cream da take sha. "Me Jannah yanxu haka ake shan ice cream?" Sulaimi ta tambaya.
Murkud'a baki Jannah tayi had'e da cewa "ai blueberry nace ki bani ko pistachio not red velvet" "Ki gyara fuskarki kinji bumblebee?" Uncle Abdul ya shafa kanta. "Sure Uncle". Juyawa tayi ta kalli Sumayya dake ta faman zabga mata harara. Yi tayi kamar bata gane ba tace " min fadlik a yumkin an tanawil-" ta fara magana kenan Mufida tayi saurin katseta.
"Kiyi da Hausa mana". Tsaki taja kafin tace " ki dena takura min I wasn't talking to you. Idan baki San me nake fada ba sai kiyi shiru. You don't have to intrude". Harara Mufida ta gallara mata tana me cewa "larabcin Iraq larabci ne?" Amsawa Jannah tayi tana me cewa "As much as I know na iya general Arabic and Iraq's. Kefa?" "Jannah stop being rude" Ahmad ya fada. "I'm sorry Father".
Da dare Sumayya tasa Jannah da Rahma a gaba sai faman nasiha take musu. Can bayan ta gama Jannah ta fara magana " Mommy what's inside that silver chest? And why don't you let us open it? " shiru Sumayya tayi kafin tace "you'll get to know what's inside when you turn eighteen or maybe idan kika yi aure or maybe when I'm dead." "Mommy wannan wani irin magana ne?". Jannah ta fara rai bace
Murmushi Sumayya tayi hade ta tura ta wajen Babanta. Maida kallonta tayi kan Rahma sannan tace " Daughter promise me bazaki gayawa Jannah komai a kai na ko a kanki ba har sai bayan rai na ko kuma sai ta kai eighteen" "Aunty-" "No Rahma just promise me. Please baby" "I promise" Rahma ta fara a hankali. "Shukran habibty. Bahibbik kathiran" Sumayya ta rungumeta. "Bahibbik aidan Ya Omri".
YOU ARE READING
ILLAR MARAICI
RandomTa kasance sanyin idaniyar iyyayenta. Sanadin farincikinsu, dalillin jin dadinsu kuma 'ya kwalli daya ga attajirai biyu. Yaya rayuwarta zata kasance idan ta rasa dukkansu biyu? Follow the bittersweet emotional rollercoaster life of Jannah. A little...