shafi na biyu

430 12 0
                                    

*_A RUBUCE TAKE!!!_*
        (Kaddarata)
        *HUGUMA*

Free page 02

*MAAB LUXURY HOME*

*_idan kaji gangami akwai labari_*

*_SABUWAR DUNIYA CE_*
*ALFAHARIN UWAR GIDA*
*FARINCIKIN AMARYA*
*MAIDA TSOHON GIDA SABO*
*DUNIYAR QYALE QYALE*
*KAYA NA ALFAHARI DA TAQAMA*

*_Ba iya kyawun idanu suka tsaya ba,harma da ingancinsu da kuma qwarkonsu,ka dade kana mora kana kece tsara a tsakanin tsararraku da sauran mutane_*

*nasan zaku tambaya ina ne nan?*

*MAAB LUXURY HOME*

😊 *Kai daga jin sunan ma babu tambaya*

*_duniyar qawata muku gidajenku ku ganku kamar a wata nahiya ko wata duniyar_*

*Suna kawo kayan kitchen rankatakaf manya da qananu*

*Kayan gado dana parlor*

*Kai...suna kawo kowanne nau'in kayan ado na cikin gida*

*Karkiyi qasa a gwiwa kuma kada kiyi sake ma dafe,maza garzaya ki nemesu a*

_adress dinsu dake No 22 Ahmadu bello way,kano state_

*Ko kuma kuyi order din kayanku kuna daga gida ta shafinsu na instagram*

@maabluxuryhome

*Facebook*
@maabluxuryhome

*Ko ku nemesu ta lambar wayarsu kamar haka*
08034631010

*Kyau inganci da rahusa shine takenmu*😊😊🤝🤝🤝🤝
____________________________

        waiwayowa yayi yana dubanta bayan ficewarsu gaba daya,maficin da ummu ta tashi ta bari ne riqe a hannunta tana tsige adon jiki,fuskarta a dinke tsaf,yakanyi.mamakin yadda take masa,kamar wata qatuwar budurwa,ya rasa dalilin da sam bata son su zauna waje guda ko su hadu,saidai har yanzu zuciyarsa na bashi nutsuwar cewa quruciya ce kawai da rashin sanin ciwon kanta,da zarar ta sake hada hankalinta zata fuskanceshi?

"Amma sai yaushe?,lokaci qara quracewa fa yake" zuciyarsa ta gaya masa,sai ya dan gyada kai

"Soon in sha Allah" ya fada yana bawa kansa qwarin gwiwa,qwarin gwiwar da kusan kullum itace madogararsa

"Widad" ya kira sunanta

"Na'am" ta amsa a cunkushe ba tare data kalleshi ba,murmushi yayi

"To kidan kalleni mana?,ummm,ke da zaki zama matata?,so nake ki saki jiki da yayan naki" manyan fararen idanuwanta ta daga tana kallonsa,wani haushi da kuma tsanarsa suka saukar mata,lallai yaaya mahfood ta tabbata dan iska ne,ita yakewa zancen ta zama matarsa?.

          Yadda ta zuba masa fararen idanuwan nata sai yaji dadi cikin ransa,don takan jima bata tsaya ta kalleshi ba,wannan ya bashi qwarin gwiwar janyo ledar daya shigo da ita wadda ke shaqe da kayan kwalliya,kasancewar ya santa da son kayan ado da gayu ya tura gabanta

"Ga kayan kwalliya nan 'yammatan ummu,sai ayita shafawa ko?" Dauke idanunta tayi daga kansa ta mayar kan kayan,saita dalla wa kayan harara,ita zaiwa wayo?,ya dauka bata da hankali kenan,haka kawai,bayan ummu tasha gaya mata ko zama tayi kusa  namiji ciki zatayi,shine zai wami bata kayan kwalliya?,to bai isa ba,tana gama wannan tunanin ta miqe abinta ta nufi qofa da saurinta.

         "Zo mana widad.....widad"ya fara qwala mata kira,gudun kada latifa ko ummu dake daki su jiyo shi,su kuma sanyata dawowa dole saita fella da gudu ta qarasa ficewa,don ta lura shi kadai ne zaifi mata saurin barin sassan.

A RUBUCE TAKE k'addarataWhere stories live. Discover now