🦇🦇🦇 *JEMAGE.* 🦇🦇🦇
_MALLAKIN._
*ZAHRA ABDUL M AHLAN.**PAID.*
BOOK.
_3/2/2023_🪄*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
_da sunan Allah mai rahma mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga shugaba ja gaba Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa sallam da iyalan gidansa da Sahabbansa da shehunnai da ma magoya baya bakidaya har izuwa ranar sakamako, Ya Allah ka bamu ikon gama wa lafiya yadda muka fara lafiya alfarman Ahalil baitin Nabiy Rasulillahi S,A,W_💚
_~AMINTATTU GUDA UKU DAGA AMINAN JUNA UKU~_
*AISHA A YABO FULANI*
*RASHIDAT USMAN OUM NASMAH*
*ZAHRA'U ABDUL M AHLAN*
_PAID BOOKS CIKIN FARASHI MAI SAUKI_
_GUDA ƊAYA #200 GUDA BIYU #300 GUDA UKUN #500, AMMA PAYMENT TA KATI YA SHA BAMBAN DA TA ACCT, GUDA DAYA #300 BIYU #500 UKUN #600, BIYA KUDIN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKI 0006064512 Rashida Usman JAIZ BANK ko kuma katin waya ta daya daga cikin waɗannan lambobin_
08147537180
08162576936
08165550116
*Masu turo da evidence of payment wadanda suka yi transfer to acct ku turawa ɗaya daga cikin mu, don girman Allah banda vtu inde kika yiwa ɗayan mu vtu to kinyi sadaka Anty☺️ muna godiya gareku masoya*🪄_SADAUKARWAR LITTAFIN *JEMAGE* GA KAWALLIYA *RASHIDAT USMAN UWAR NASMAH* INA MIKI LUV DOMIN ALLAH, BABBAN KAUNA ZUWA GAREKI AMINIYA *AISHA FULANI* RABBI YA BARMU TARE_
_LITTAFIN *JEMAGE* KYAUTA CE GA SISINA KUMA TAWAN *KHADIJA SANI JOURNALIST* INA MIKI SAHIHIN KAUNA TAWAN❣️🥹 INA ROƘON ALLAH YA SHIGA LAMARIN KI,ALLAH YA IYA MIKI ALLAH YA DAFA MIKI ALLAH YA BIYA MIKI BUKATUNKI NA ALKAIRI FIDDUNYA WAL AKHIRAH, ANA UHIBBUKI YA UKHTY_❤🩹
*TSOKACI*
_LITTAFIN *JEMAGE* KIRKIRARRIYAR LABARI NE, DA FATAN ZA A DUBA DARASIN DAKE CIKI_*GARGAƊI*👂🏼
_BAN YARDA A JUYA MINI LABARI TA KO WANI SIGA BA, BAN YARDA A ƊORA MINI LITTAFI A YOUTUBE CHANNEL BA TARE DA IZININA BA, SO PLS A KIYAYE._
===========
Follow me on my wattpad @Fateemah0.
==============
*MARUBUCIYAR.*
1-HALITTA DAGA ALLAH NE.
2-GUDU A JEJI.
3-SHUHADA.
4-NIDA ƘANNEN MIJINA.
5-WA'YA KASHE ZAHRA'U? #200.
6-COLONEL UBAIDULLAH.
7-ITA CE ZUCIYATA #200.
8-SAMIMA (MACIJIYA CE).
9-DA NA SANI NA.
10-GAWURTACCEN SOJA #300.
11-BADAWIYYAH.
12-AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE) #300.
13- AHLAN #200.
14-DSP ALIYU HAIDAR.
15-SARKIN RUWA #200.
16-MAMIYOTA CE #200
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆
FREE PG-3️⃣▶️4️⃣
Yana nan tsaye sai ga abokinsa Umari yazo wuce wa ya gansa ya ce
"Ah Musa kai ne a nan?" saurin saita natsuwarsa yayi da kyar ya ba wa Umari hannu suka yi musabaha,
"Me kake yi a kofar gida kai ɗaya a wannan lokacin? ko dai matsalar jikin Rashida ne ya sanya ka a gaba? tunda yau dik inda ka gitta batun jikin Rashida ake yi" jinjina kai Musa ya yi tabbas yau gabaɗayan ƙauyen Lanbu bakinsu ya dauka da batun ciwon Rashida inda dayawa suka laƙaba mata hauka tunda sunji labarin an kai ta gidan Malam mai allo za ayi mata rubutun wankin kwakwalwa, Umari ya ce
"Mu karasa Majalisan matasa sai mu tattauna a can abokina" Musa bai yi mi shi musu ba ya bisa suka tafi majalisan matasa, zama suka yi a gefe su biyu yadda zasu ji dadin hiran tasu a ke6ance, Umari ya ce
"Na san kana kaunar Rashida Musa, kuma zaka iya mata duk kokarin ka wajan ganin ka sama mata lafiya ni a ganina me zai hana ku dauki Rashida ku kai ta ƙauye sanda wajan Malam Habu mai carbi?" shuru Musa ya yi yana auna batun abokinsa Umari kafin ya ja numfashi ya ce
"Shikenan in sha Allahu zan yi magana da Baba sai a kai ta kauyen sanda din amma ya yi nisa wallahi dole fa sai an kwana a kusa da makotan kauyen 6illiri?"
"To ya za ayi ai dole ce ta sanya, su ma 'yan kauyen 6illirin sun sani sarai yan kauyenmu na kwana a kusa da kauyensu idan zasu je kauyen sanda ka ga kuwa hakan ba matsala ba ce tunda su ma idan zasu fito zuwa ƙauyen gwarka sai sun biyo ta kauyen lanbu"
"To ai rikicin ƙauyen 6illiri da makotan kauyenmu har yanzu fa tana nan"
"Musa batun neman lafiyar Rashida ake yi ba batun rikicin manoma da makiyaya ba, yan kauyen 6illiri kowa yasan sunyi ba daidai ba amma meyasa sarkin kauyuka gabaɗaya ya goyawa ƙauyen 6illiri baya dole ƙauyen gona fa su tunzura, idan ma banda tsatstsauran gaba irinta kauye ya kamata a bar abin ya wuci haka ni dai ka bar wannan maganar aji da lafiyar Rashida tunda na san nan ba da jimawa ba za a fara batun aurenku ne" sake jan ajiyar zuciya Musa ya yi kana yace
"In sha Allahu
zan yiwa Baba da Inna maganar dik yadda muka yi zan sanar da kai"
"To shikenan ba matsala"
Sallama akayi musu, suka ɗago suka amsa Musa ya dauke kai Umari ya ce
"Ah Buba kai ne?"
"Wallahi ni ne, Musa ya aka yi kana ganina ka dauke kai? Nifa zuwa nayi na jajinta muku naji ance Rashida ta kamu da cutar hauka wanda yake sanyata gane-gane ga sambatu shine fa nazo na jajinta maka ba wani abu ba amma naga sai hura hanci kake yi kuma...."
"Haba don Allah Buba wannan wani irin Jajintawa ne haka?" Musa yace
"Bar shi ya karasa fadin abinda ke ransa kafin nima na aikata wanda yake raina dan tsaf zan fasa masa hanci da naushi daya" kafin ka an kara cacan baki ya kacame a tsakanin Buba da Musa inda duk wani baƙar magana da yazo zuciyar Buba zai ya6awa Musa kamar dama jira yake yi wani abu ya samu Musan ya caccake shi, Umari na ta hana Buba dan shi ne da jan magana bai da gaskiya har maganar da bai dace ba faɗi yake yi, fizgo Buba Musa ya yi zai kai masa duka nan yaja hankalin sauran matasan dake gun inda aka zo aka kwaci Buba da kyar daga hannun Musa inda wasu suke goyan bayan Buba wasu kuma bayan Musa, da kyar Umari yaja hannun Musa suka bar gun.
YOU ARE READING
JEMAGE🦇
ActionAmintattu guda uku daga aminan juna guda uku JEMAGE MAHAUKACI NE KO ALJANI? BURI UKU. sabbin litattafai masu cike da ruɗani da sarƙakiya karku sake a baku labari, ba free books bane paid ne amma cikin farashi mai sauki #500 dika ukun if payment ta k...