free pg 9-10

7 0 0
                                    

🦇🦇🦇 *JEMAGE.* 🦇🦇🦇


_MALLAKIN._
*ZAHRA ABDUL M AHLAN.*

*PAID.*
BOOK.
    _3/2/2023_🪄

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

_da sunan Allah mai rahma mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga shugaba ja gaba Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa sallam da iyalan gidansa da Sahabbansa da shehunnai da ma magoya baya bakidaya har izuwa ranar sakamako, Ya Allah ka bamu ikon gama wa lafiya yadda muka fara lafiya alfarman Ahalil baitin Nabiy Rasulillahi S,A,W_💚

_~AMINTATTU GUDA UKU DAGA AMINAN JUNA UKU~_
*AISHA A YABO FULANI*
*RASHIDAT USMAN OUM NASMAH*
*ZAHRA'U ABDUL M AHLAN*
_PAID BOOKS CIKIN FARASHI MAI SAUKI_
_GUDA ƊAYA #200 GUDA BIYU #300 GUDA UKUN #500, AMMA PAYMENT TA KATI YA SHA BAMBAN DA TA ACCT, GUDA DAYA #300 BIYU #500 UKUN #600, BIYA KUDIN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKI 0006064512 Rashida Usman JAIZ BANK ko kuma katin waya ta daya daga cikin waɗannan lambobin_
08147537180
08162576936
08165550116
*Masu turo da evidence of payment wadanda suka yi transfer to acct ku turawa ɗaya daga cikin mu, don girman Allah banda vtu inde kika yiwa ɗayan mu vtu to kinyi sadaka Anty☺️ muna godiya gareku masoya*🪄

_SADAUKARWAR LITTAFIN *JEMAGE* GA KAWALLIYA *RASHIDAT USMAN UWAR NASMAH* INA MIKI LUV DOMIN ALLAH, BABBAN KAUNA ZUWA GAREKI AMINIYA *AISHA FULANI* RABBI YA BARMU TARE_

_LITTAFIN *JEMAGE* KYAUTA CE GA SISINA KUMA TAWAN *KHADIJA SANI JOURNALIST* INA MIKI SAHIHIN KAUNA TAWAN❣️🥹 INA ROƘON ALLAH YA SHIGA LAMARIN KI,ALLAH YA IYA MIKI ALLAH YA DAFA MIKI ALLAH YA BIYA MIKI BUKATUNKI NA ALKAIRI FIDDUNYA WAL AKHIRAH, ANA UHIBBUKI YA UKHTY_❤‍🩹

*TSOKACI*
_LITTAFIN *JEMAGE* KIRKIRARRIYAR LABARI NE, DA FATAN ZA A DUBA DARASIN DAKE CIKI_

*GARGAƊI*👂🏼
_BAN YARDA A JUYA MINI LABARI TA KO WANI SIGA BA, BAN YARDA A ƊORA MINI LITTAFI A YOUTUBE CHANNEL BA TARE DA IZININA BA, SO PLS A KIYAYE._
===========
Follow me on my wattpad @Fateemah0.
==============
*MARUBUCIYAR.*
1-HALITTA DAGA ALLAH NE.
2-GUDU A JEJI.
3-SHUHADA.
4-NIDA ƘANNEN MIJINA.
5-WA'YA KASHE ZAHRA'U? #200.
6-COLONEL UBAIDULLAH.
7-ITA CE ZUCIYATA #200.
8-SAMIMA (MACIJIYA CE).
9-DA NA SANI NA.
10-GAWURTACCEN SOJA #300.
11-BADAWIYYAH.
12-AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE) #300.
13- AHLAN #200.
14-DSP ALIYU HAIDAR.
15-SARKIN RUWA #200.
16-MAMIYOTA CE #200
  
     🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆

FREE PG-9️⃣▶️🔟

ya jima a tsaye a gun yana saƙe-saƙe yana tunanin mafita har Musa ya isa gida Baba bai motsa daga inda Musa ya bar shi ba, da kyar ya iya jan kafafunsa ya nufi gida da sallama ya shiga dakin Rashida wacce ke kwance a katifarta. Kallo daya Baba ya yi mata ya dauke kai dan bazai jure kallonta a wannan halittar ba, Inna kuwa ta ƙurawa Rashida idanu ko ƙiftawa bata yi.
"Salame?" Baba ya kira sunan Inna a sanyaye,jan hanci tayi ta riƙe ha6arta tana jinjina kai har yanzu idanunta na kan Rashida ta ce
"Malam yanzu wannan Rashida ce? 'Yata Rashida ce ta koma haka? Lamari kamar a wasa ga shi nan ya koma gasken-gaske, Malam dubi Rashida ka ga Rashida fuska ya koma na dodo, har yanzu ganin abin nake kamar a mafarki, me muka aikata ne haka wani zunubi muka aikata mai girman gaske haka, ga shi an kasa sanin mene ne musabbabin wannan ciwo ance ba aljanu bane to miye mutum zai yi tunani akan ciwon Rashida?" wani kuka Inna ta saka mai ban tausayi da karya zuciya, da sauri Baba ya matso kusa da Inna ya hau bubbuga kafaɗunta cikin rarrashi dan ya kasa bata baki ba, Inna ta yi kuka har ta godewa Allah a wannan dare a karshe Baba yasa ta suka yo alwala suka fuskanci alƙibla domin kai kukan su ga Allah ya kawo musu daukin wannan tashin hankali, har aka kira asuba Baba ya fito kenan ya ga Musa har ya ma idar da alwala ga buta a gaban Abdul da ke ta faman gyangyaɗi dan shi ma kwanan firgita yayi fuskar Rashida da ya gani ta tsorota shi matuƙa, sai da suka jira Baba ya yi alwala suka fita tare kamar yadda suka saba a hanya Musa ke fadin
"Baba kayi hakuri idan a cikin abinda na faɗa jiya ya bata maka rai"
"Ko kaɗan Musa bai bata min rai ba, ka tuna min abinda na so na manta ne, in sha Allah kuma zanyi kokari naga na fayyace komai kuma In sha Allah sai Jalo da Jatau sun wulakanta sun tozarta sai sun girbi abinda suka shuka Allah zai kawo mana karshensu" da haka suka isa masallaci bayan sunyi sallah aka gaggaisa mai unguwar lanbu wato Murtala ya dubi jama'a ya koro musu bayanin da Malam Yahaya yazo ya sanar da shi daren jiya, nan take masu jaje suka hau jajinta masa wasu kuwa da ba a shiri Allah ya ƙara suka yi a ransu inda mai unguwar lanbu ya ce a yanzu za ayi zuga ne aje gidan sarkin lanbu a sanar da shi za a haɗu aje gidan sarkin ƙauyuka ya kira shuwagabannin sauran ƙauyuka ayi sanarwan zuwa da Rashida can ƙauyen sanda domin nemo mata magani za a kaita gurin malam Habu mai cirbi,nan kowa yayi na'am da batun mai Unguwa, Mai Unguwa ya ce kafin nan su fara zuwa su duba Rashidan tukunna, Malam Yahaya ne ya yi musu jagora izuwa gidansa inda wasu sunje ne kawai dan gulma domin har da Buba, Musa bai so Buba bin su ba zai kara samun bakin gulma ne kawai tunda shi munafuki ne,Baba ne ya danni Musa, shiga cikin gidan ya yi ya sanar da Inna za a shigo duba Rashida sam Inna bata so ba amma ba yadda ta iya ta sanya mayafi Baba ya fita ya shigo dasu mai unguwa wanda shi da kansa mai unguwar ne a gaba, har izuwa dakin da Rashida ke kwance wanda abin kamar ƙara yawa yake yi domin kuwa safiyar yau hannuwanta ma sun sauya daga hannun bil'adam lamarin da ya rikita mai unguwa da mutanensa ya sa musu sanyin jiki, duk yadda Buba yaso hange ya hango Rashida abin ya gagara da gayya Musa ya sake tare shi, addua mai unguwa ya yi jagoranci suka yi wa Rashida kana suka fito basu yi sai6in jiki ba kuwa suka yi tattaki izuwa gidan sarkin lanbu, sun sha tattaki kam kafin su isa wasu ma kam a amalanke suka tafi dan ba zasu iya tafiyar kafan ba,Musa ya ce da Baba ya hau amalanke amma ya ce sam ya bar shi kawai ya ci gaba da tafiya dan shi kadai ne yasan halin da yake ciki.
Sun isa gurin sarkin lanbu inda wazirin lanbu da sauran hadimai da wakilan lanbu da sauri suka tarbi su mai unguwa nan aka gaggaisa cikin mutunci a fada kana aka sa karamin yaron sarkin lanbu da ya kira mahaifinsa a cikin gida, wakilin sarkin lanbu ya dubi mai unguwa yace
"Allah ya taimakeka ai sarki bai jima da shiga gida ba sabida bamu dade da tashi a gun addua ba"
"Allah sarki muma cewa muka yi gara mu yi sammako kan anjima a fara cika ba zamu ji dadin isar da abin da ya kawo mu ba" nan dai suka ɗan taba hira a tsakaninsu Yayinda Baba yayi shuru kamar bai gun Wakilan sarkin lanbu ya ce
"Malam Yahaya ya na ganka wani iri ne haka?" a dan zabure Baba ya gyara zama ya ce
"Ba komai Malam Bukar" shuru ya yi dan bai yarda ba da alama akwai gagarumin matsalar dake faruwa a lanbu in ba haka ba yasan dai Malam Yahaya manomin mutum ne mai guzari da hanzari ga himma ga jarumta, shuru dai kawai yayi ya rabu da shi aka ci gaba da tsumayen fitowar sarkin lanbu kamar da mintuna da ba zasu gaza hudu ba ya fito daga ganinsa mutum ne mai kamala ya dace da mulkin da yake kai.
Zama ya yi inda mai unguwa da sauran mutane da suka zo aka kwashi gaisuwa gun sarki lanbu wato  sarki Jabiru, ya amsa cikin mutunci da mutuntawa inda yake tambayar da fatan komai yana tafiya lafiya a lanbu da kewayenta? Gyara zama mai unguwa ya yi kana ya yi gyaran murya ce
"Alhamdulillah Allah ya taimake ka lafiya amma ayansu ba zamu ce lau ba sabida akwai wani abu dake dinfaro mu"
"SubhanAllahi! Me ke nan?" cewar sarkin lanbu.
"Wato yar gidan malam Yahaya ce Rashida ta samu matsala, da fari bamu yi zatan matsalar zata zama gagaruma ba amma a halin yanzu ta zarce tunani, kwanaki ne da basu gaza takwas ba a yadda mahaifinta ke bada labari rannan sunje kauyen bishiyar kuka wato sunje dandali tun daga ranar da ta dawo ta fara zabure-zabure da maganganu irin wadanda aljannu suka shafa, to koda aka dauketa aka kaita gun malam mai allo ya yi mata iyakar abin da Allah ya yassare masa na daga cikin hikima amma ba abinda ya sauya sai ma da abi ya dinga gaba ihu take yi tana faɗin cewa tana ganin *JEMAGE*"
Haɗa baki Sarkin Lanbu da jama'arsa dake gurin suka yi wajan faɗin
"Jemage dai? Wani irin jemage?" sake gyaran murya mai unguwa ya yi ya ce
"A yadda take fasalta shi hankali ma zai dauka ba, babban damuwar malam mai allo ya ce ba shafan aljanu bane lamarin dai da daurewar kai Allah ya taimake ka, yanzu haka malam mai allo ya yi mata rubutun wankin kwakwalwa amma Rashida halittarta ta sauya ta fita daga jinsin bil'adam"
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Allahumma ajirni fi musibatihi wa akhlafni khairan minha" Sarkin Lanbu ya faɗi ya dubi Baba ya sake maida idanunsa kan
Mai unguwa
"Yanzu fisabilillahi kunyi min adalci kenan ace tun farkon matsala baku zo kun gaya min mu hada karfi da karfi a shawo kanta ba sai a yanzu da lamari ya ta'azzara yayi tsamari zaku kwaso jiki ku zo?" ya karisa maganar cikin nuna fushi
"Allah ya taimake ka wlh sam bamu san abin zai yi tsanani haka ba" cewar Baba
"Ai ita dama matsala daga karama take farawa indai ba a tare ta an shawo kanta ba zatayi girman da shawo kanta zaiyi wa mutane wuya"
"Duk a tunaninmu aljanu ne suka shafeta sabida suna yawan zuwa kauyen bishiyar kuka kuma hanyar sai a hankali ita karan kanta dandalin fa akwai katuwar bishiyar kuka"
Cewar wakilan mai unguwa, sarkin lanbu ya ce
"Duk wannan ba hujja ba ce, aljanun da suke hanyar ƙauyen bishiyar kuka sun zauna lafiya da iyaye da kakanninmu idan ba taba su aka yi ba ba wani abun cutar wa da zasu yiwa wani daga cikin alumma sai dai taba su aka yi" hannu Baba ya saka yana goge gumi mai unguwa ya ce
"Amma fa malam mai allo yace ba aljanu a lamarinta"
"Ikon Allah ikon gaske" sarkin lanbu ya faɗi yana jinjina kai, kana yace.
"Yanzu ta ina zamu fara maganin wannan matsalar?" nan mai unguwa ya sanar mi shi ana son kai Rashida kauyen sanda ne wajan Malam Habu mai carbi kuma sai an kwana a ƙauyen 6illiri ga kuma rikicin dake tsakanin ƙauyen 6illiri da maƙotan ƙauyen su ƙauyen gona, a takaice dai suka sanar da shi suna so ne aje a samu sarkin ƙauyuka ayi masa bayani da ya kira 'yan ƙauyen 6illiri ya sanar dasu za a kwana ban da tashin hankali ko ɗaga makami, gyaɗa kai Sarkin lanbu ya yi ya ce
"Hakan ya yi bari na shiga na karisa kimtsawa na fito mu ɗunguma zuwa gun sarkin ƙauyuka ba a bori da sanyin jiki" tashi ya yi da sauri ya shiga gida bai jima ba ya fito da shirinsa ya tambayi alummansa kowa ya shirya suka shaida masa a shirye suke kawai a tafi. sunyi tafiya mai dogon zango da kafa inda a karshe wasu aka fara kwasar su a amalanke wasu kuma akan jaki.
Sun samu isa ƙauyen tsakiya inda a nan ne sarkin ƙauyuka ke zama kuma duk abinda ke faruwa a sauran kauyuka yana samun labari wasu abubuwan ma da umarninsa ke tafiya, bayan anyi musu iso zama suka yi suna jiransa inda ya shafe sama da mintuna ashirin kafin ya fito, hakika Sarkin ƙauyuka ba ya mulkin adalci idan kuma haka zai ci gaba da tafiya zasu fara addua Allah ya musu maganin shi ya sauya musu shi cikin gaggawa, zama ya yi kana ya dubi sarkin lanbu yace
"Sarkin lanbu lafiya kuwa na ganku zuwa babu wasiƙa?" ba tare da bata lokaci ba suka gaishesa cikin martaba wa suka shaida masa abinda ke tafe dasu, ganin abinda sarkin ƙauyuka ke yi yasa jikin Baba yayi sanyi ya kasa furta koda kalma ɗaya ne akan abinda ya shiga tsakaninsa da Jalo, basu sake karaya ba har sai da ya furta cewa har sai idan ƙauyen 6illiri sun yarda da a kwana a ƙauyensu idan ba haka ba sai dai su zarce kai tsaye su tafi kauyen sanda a ranar, cikin mamaki sarkin lanbu yace.
"Ranka ya dade a halin da ake ciki ance yarinyar nan fa halittarta ta sauya, taya kuma zasu miƙe tin daga kauyen lanbu har izuwa ƙauyen sanda a rana ɗaya?"
"Sarkin lanbu tuhumata kake yi?" ƙasa da kai sarkin lanbu ya yi yace.
"Ko kaɗan ranka ya dade bana tuhumarka, kawai ina duba ita yariny...."
"Ya isa haka! Ku tashi kuje ina da zuwa rafi duba abu mai mahimmanci zanyi kokari nasa a rubuta saƙo sarkin 6illiri da mai unguwan 6illiri da wakilan 6illiri su zo, dan haka sai kuzo a haɗu har da sarkin ƙauyen gona da mai unguwar ƙauyen gona" yana gama faɗi ya mike bai saurari abinda zasu faɗa ba, kasa tashi Baba ya yi har sai da sarkin lanbu ya ɗagosa haka suka koma jiki ba kwari.

Su Fatu yau ko makaranta basu je ba suna gama aikace-aikacen su a tare da iyayensu suka zo duba Rashida wanda ganinta a yau ya yi matukar gigita su amma ko kaɗan ba zasu gujeta ba, har su Umma da Iyah suka tafi aka bar Rashida da kawayenta wacce sam bata gane su wa ke kanta, sosai Inna ke danasanin rubutun wankin kwakwalwa da Rashida tasha dan gani take shine musabbabin komawarta haka dama an barta da ganin jemagen da tace tana yi.

     Jiki ba kwari bayan sun dawo lanbu a hanya Musa ke fadin shi zai kai Rashida ƙauyen sanda koda zai rasa ransa, Baba ya dube shi yace
"Musa idan aka yi magruba zamu je jejin zarga" da sauri Musa ya kalli Baba yace
"Wajan Jalo zamu je?"
Baba ya jinjina kai.....

#COMMENTS
#SHARE
#MomAhlan🪄

JEMAGE🦇Where stories live. Discover now