free pg 13-14

9 0 0
                                    

🦇🦇🦇 *JEMAGE.* 🦇🦇🦇


_MALLAKIN._
*ZAHRA ABDUL M AHLAN.*

*PAID.*
BOOK.
    _3/2/2023_🪄

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

_da sunan Allah mai rahma mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga shugaba ja gaba Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa sallam da iyalan gidansa da Sahabbansa da shehunnai da ma magoya baya bakidaya har izuwa ranar sakamako, Ya Allah ka bamu ikon gama wa lafiya yadda muka fara lafiya alfarman Ahalil baitin Nabiy Rasulillahi S,A,W_💚

_~AMINTATTU GUDA UKU DAGA AMINAN JUNA UKU~_
*AISHA A YABO FULANI*
*RASHIDAT USMAN OUM NASMAH*
*ZAHRA'U ABDUL M AHLAN*
_PAID BOOKS CIKIN FARASHI MAI SAUKI_
_GUDA ƊAYA #200 GUDA BIYU #300 GUDA UKUN #500, AMMA PAYMENT TA KATI YA SHA BAMBAN DA TA ACCT, GUDA DAYA #300 BIYU #500 UKUN #600, BIYA KUDIN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKI 0006064512 Rashida Usman JAIZ BANK ko kuma katin waya ta daya daga cikin waɗannan lambobin_
08147537180
08162576936
08165550116
*Masu turo da evidence of payment wadanda suka yi transfer to acct ku turawa ɗaya daga cikin mu, don girman Allah banda vtu inde kika yiwa ɗayan mu vtu to kinyi sadaka Anty☺️ muna godiya gareku masoya*🪄

_SADAUKARWAR LITTAFIN *JEMAGE* GA KAWALLIYA *RASHIDAT USMAN UWAR NASMAH* INA MIKI LUV DOMIN ALLAH, BABBAN KAUNA ZUWA GAREKI AMINIYA *AISHA FULANI* RABBI YA BARMU TARE_

_LITTAFIN *JEMAGE* KYAUTA CE GA SISINA KUMA TAWAN *KHADIJA SANI JOURNALIST* INA MIKI SAHIHIN KAUNA TAWAN❣️🥹 INA ROƘON ALLAH YA SHIGA LAMARIN KI,ALLAH YA IYA MIKI ALLAH YA DAFA MIKI ALLAH YA BIYA MIKI BUKATUNKI NA ALKAIRI FIDDUNYA WAL AKHIRAH, ANA UHIBBUKI YA UKHTY_❤‍🩹

*TSOKACI*
_LITTAFIN *JEMAGE* KIRKIRARRIYAR LABARI NE, DA FATAN ZA A DUBA DARASIN DAKE CIKI_

*GARGAƊI*👂🏼
_BAN YARDA A JUYA MINI LABARI TA KO WANI SIGA BA, BAN YARDA A ƊORA MINI LITTAFI A YOUTUBE CHANNEL BA TARE DA IZININA BA, SO PLS A KIYAYE._
===========
Follow me on my wattpad @Fateemah0.
==============
*MARUBUCIYAR.*
1-HALITTA DAGA ALLAH NE.
2-GUDU A JEJI.
3-SHUHADA.
4-NIDA ƘANNEN MIJINA.
5-WA'YA KASHE ZAHRA'U? #200.
6-COLONEL UBAIDULLAH.
7-ITA CE ZUCIYATA #200.
8-SAMIMA (MACIJIYA CE).
9-DA NA SANI NA.
10-GAWURTACCEN SOJA #300.
11-BADAWIYYAH.
12-AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE) #300.
13- AHLAN #200.
14-DSP ALIYU HAIDAR.
15-SARKIN RUWA #200.
16-MAMIYOTA CE #200
  
     🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆

FREE PG-1️⃣3️⃣▶️1️⃣4️⃣

Maida duban sa kan Baba sarkin lanbu ya yi, yayinda Baba ya sunkuyar da kai ya ce
"Allah ya ƙara maka adalci zamu tafi in sha Allah koda zamu rasa rayukan mu Rashida zata samu sauki da yarda Allah" duk wanda zai ce jikinsa bai yi sanyi ba ya yi karya, nan sarkin lanbu ya ce ba damuwa tunda haka suke so Allah ya tsare ya kai su lafiya zuwa goben sai a sadda yadda za ayi, amma wani hanzari ba gudu ba waye zai kai su? ƙasa da kansa Musa ya sake cikin ladabi ya ce
"Zan karbi aron dokin gidansu abokina Umari, sai kuma zanyi magana da Jafaru ya ara mana amalanken sa"
"To shikenan, Allah yasa a dace" cewar sarkin lanbu aka amsa da amin. Daga fadar sarkin Lanbu gidansu Abokinsa Umari Musa ya wuce kai tsaye, ya ci sa'a kuwa ya samu Umari zaune a kan ƙaramar busheshshiyar itace dake kofar gidan, hannu ya ba shi suka yi musabaha yace
"Abokina ya dai na ganka haka ba dai jikin Rashidan bane?" sai da Musa ya zauna ya numfasa tukunna ya dubi Umari ya hau zayyano masa halin da ake ciki, sosai Umari ya jinjina lamarin yana mamakin sarkin ƙauyuka sam matsayin wannan mulki bai kamace shi ba, inda Musa yace.
"Don Allah aron dokin gidanku nakeso sannan inaso ka rakani naje ƙauyen Mani gun Jafaru ya bani aron amalankensa sabida Rashida tunda ba zata iya hawa doki har zuwa ƙauyen sanda ba duba da yanayin yadda ta koma"
"Ba matsala Musa zan fara shirya maka dokin da dare sai na kawo maka yanzu muje na raka ka ƙauyen mani gun Jafarun idan muna dawowa sai ka ajiye ni a hanya dan sai an yiwa dokin wanka"
"Na gode sosai Umari"
"Haba dai Musa ana tare kuma an zama ɗaya ai" a tare suka miƙe zasu fara tafiya sai ga mahaifin Umari zai shiga gida wanda dawowarsa kenan, har ƙasa Musa ya duƙa ya gaida shi, amsawa Baban Umari ya yi yana tambayarsa ya jikin Rashida ya amsa da sauki yazo ne ma yana son aron doki Baban Umari ya muna masa ba damuwa da yake mahaifin Musa aminin Baban Umari ne sosai, Umari yace
"Baba ana son kai Rashida kauyen sanda ne" gyaɗa kai Baban Umari ya yi ya ce
"Gurin malam habu mai carbi ko?"
"Eh Baba"
"Gaskiya kam hakan yayi Allahu yasa a dace" suka amsa da amin Umari yace
"Baba zamu je kauyen mani gun Jafaru ya ara mana amalanken sa"
"Yawwa to ka biya ka karbo min sakona a gun mahaifin Jafarun"
"To Baba" Umari ya faɗa yana yin gaba Musa ya sake yiwa Baba godiya kafin ya bi bayan Umari a hanya suna tafiya suna ɗan hira wanda gabaɗaya karfin hiran akan yanayin jikin Rashida ne.

JEMAGE🦇Where stories live. Discover now