🦇🦇🦇 *JEMAGE.* 🦇🦇🦇
_MALLAKIN._
*ZAHRA ABDUL M AHLAN.**PAID.*
BOOK.
_3/2/2023_🪄*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
_da sunan Allah mai rahma mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga shugaba ja gaba Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa sallam da iyalan gidansa da Sahabbansa da shehunnai da ma magoya baya bakidaya har izuwa ranar sakamako, Ya Allah ka bamu ikon gama wa lafiya yadda muka fara lafiya alfarman Ahalil baitin Nabiy Rasulillahi S,A,W_💚
_~AMINTATTU GUDA UKU DAGA AMINAN JUNA UKU~_
*AISHA A YABO FULANI*
*RASHIDAT USMAN OUM NASMAH*
*ZAHRA'U ABDUL M AHLAN*
_PAID BOOKS CIKIN FARASHI MAI SAUKI_
_GUDA ƊAYA #200 GUDA BIYU #300 GUDA UKUN #500, AMMA PAYMENT TA KATI YA SHA BAMBAN DA TA ACCT, GUDA DAYA #300 BIYU #500 UKUN #600, BIYA KUDIN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKI 0006064512 Rashida Usman JAIZ BANK ko kuma katin waya ta daya daga cikin waɗannan lambobin_
08147537180
08162576936
08165550116
*Masu turo da evidence of payment wadanda suka yi transfer to acct ku turawa ɗaya daga cikin mu, don girman Allah banda vtu inde kika yiwa ɗayan mu vtu to kinyi sadaka Anty☺️ muna godiya gareku masoya*🪄_SADAUKARWAR LITTAFIN *JEMAGE* GA KAWALLIYA *RASHIDAT USMAN UWAR NASMAH* INA MIKI LUV DOMIN ALLAH, BABBAN KAUNA ZUWA GAREKI AMINIYA *AISHA FULANI* RABBI YA BARMU TARE_
_LITTAFIN *JEMAGE* KYAUTA CE GA SISINA KUMA TAWAN *KHADIJA SANI JOURNALIST* INA MIKI SAHIHIN KAUNA TAWAN❣️🥹 INA ROƘON ALLAH YA SHIGA LAMARIN KI,ALLAH YA IYA MIKI ALLAH YA DAFA MIKI ALLAH YA BIYA MIKI BUKATUNKI NA ALKAIRI FIDDUNYA WAL AKHIRAH, ANA UHIBBUKI YA UKHTY_❤🩹
*TSOKACI*
_LITTAFIN *JEMAGE* KIRKIRARRIYAR LABARI NE, DA FATAN ZA A DUBA DARASIN DAKE CIKI_*GARGAƊI*👂🏼
_BAN YARDA A JUYA MINI LABARI TA KO WANI SIGA BA, BAN YARDA A ƊORA MINI LITTAFI A YOUTUBE CHANNEL BA TARE DA IZININA BA, SO PLS A KIYAYE._
===========
Follow me on my wattpad @Fateemah0.
==============
*MARUBUCIYAR.*
1-HALITTA DAGA ALLAH NE.
2-GUDU A JEJI.
3-SHUHADA.
4-NIDA ƘANNEN MIJINA.
5-WA'YA KASHE ZAHRA'U? #200.
6-COLONEL UBAIDULLAH.
7-ITA CE ZUCIYATA #200.
8-SAMIMA (MACIJIYA CE).
9-DA NA SANI NA.
10-GAWURTACCEN SOJA #300.
11-BADAWIYYAH.
12-AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE) #300.
13- AHLAN #200.
14-DSP ALIYU HAIDAR.
15-SARKIN RUWA #200.
16-MAMIYOTA CE #200
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆
FREE PG-1️⃣7️⃣▶️1️⃣8️⃣
A firgice Baba da Musa suka mike tsaye akan kafunsu da kyar ga tashin hankalin ganin kaf mutanen kauyen da suka yada zango sun mutu banda karnin jini ba abinda ke tashi a gurin, cikin zafin nama suka nufi inda suke jiyo sautin muryar Inna wanda a gigice take kana ganinta kasan ba natsuwa a tare da ita ta fita hayyacinta, Baba ne ya riƙota da sauri nan take numfashin Inna ya yi sama idanunta ma suka juye sabida tsananin tashin hankali da firgici, cikin tashin hankali Baba ke jijjiga Inna
"Salame! Salame! Salame! Musa nemo ruwa" da sauri Musa ya hau waige-waige duk a ruɗe yake ya ma rasa ta ina ne zai fara yakin neman ruwan, sai zuwa can ya kwasa da gudu kamar zautacce ya hau shiga gidajen dake kusa dasu wanda ba wani bil'adam dake rayuwa,ganin gawar yarinyar da ta yi musu iso zuwa gun mai unguwa yasa Musa ya fashe da kuka lokaci guda, ruwan ya nema ya diba ya fito yana kuka yana layi, yana zuwa ya ba wa Baba ruwan yana kan kuka bai daina ba, karban ruwan Baba ya yi ya yayyafawa Inna a fuska taja numfashi ya sake shafa mata ruwan ta bude ido da sauri tana kuka tana girgiza kai dan a yadda ta fito tana arba da gawawwaki bata yi tsammanin Baban Rashida da Musa na raye ba, cikin dauriya Baba yace.
"Ina Rashida?"
Kuka Inna ta fashe da shi cikin shekakken murya tace.
"Malam Rashida an dauke Rashida!" kuka sosai Inna take yi matsinaci yayinda Baba ya saki kafadun Inna yana yin baya ya ajiye mazaunensa da kasa jikinsa na kakkarwa,
"An dauke Rashida? Wa ye?"Girgiza kai Inna ta hau yi bata san ta inda zata fara fadi wa Baba ba ta yadda aka dauke Rashida ba domin kuwa ba zata iya cewa ga hanyar da aka dauke Rashida ba.
"Tambayarki nake Salame a garin yaya aka dauke Rashida sannan waye?"
"Ban sani ba Malam, abinda zan iya tunawa naji wani sautin iska yayinda wutar dake ci a dakin ya dauke, ina rike da Rashida tamkar an wafci takarda a hannuna haka naji malam" ta karasa da sabon kuka, sake daga kai Baba yayi ya duba al'umma dake kwance agabansu basu motsi tashin hankali goma da ashirin ne a gabansu, da wanne zasu ji? da masifan dauke Rashida ko kuma a'a da tashin hankalin bala'in ƙauyen 6illiri idan suka riski cewan wani sashe na sassanin su duk sun mutu sannan suna da labarin cewan ƙauyen lanbu zasu shige zuwa ƙauyen sanda? a zabure Baba ya katse tunaninsa dan bai san me zai tunano me kyau ba, kama hannun Inna ya yi ya dagota ya kama hannun Musa dake ta faman kuka, cikin azama Baba ya hau jan su, koda suka je amalanken Jafaru kam ta kwararra6e sai dokin dake ta jijjiga kansa yana daure, ba lokacin 6atawa Baba ya haye doki ya fizgo Inna da Musa da gudu ya juya suka dauki hanyar komawa lanbu yayinda Inna ke kuka tana fadin don Allah su tsaya su duba Rashida yanzu
tafiya zasu yi basu ga Rashida ba? Don Allah su tsaya su dubata, ko kaɗan Baba bai kulata ba burinsa kawai su isa lanbu lafiya ya nufi jejin zarga duk mai kasancewa ta kasance tsakaninsa da Jalo..🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
Yau an wari gari a ƙauyen lanbu sam ba haske garin hadiri ne ɗoɗar mai cike da wani iska wanda yake fitar da kuwwa, mamaki ne ya kama yan kauyen lanbu ganin ba a lokaci na damuna ake ba amma garin ya haɗa hadiri. Amma da yake ba a mamakin da hukuncin Ubangiji yasa suka bar zancen kowa ya ci gaba da hidimar shi.
Fadar mai unguwa zaune dattawan fada suke suna magana akan yanayin da yau aka farka a garin sannan suka kara da hiran su Malam Yahaya suna ta alhini da jimamin ya suka kare a hanya shin sun fita ne ko rai yayi halinsa inda dayawa daga cikinsu jikinsu a sanyaye yake.
Abdul dake gidan Iyan Shehu ma yau tashi yayi bai da lafiya, Shatu da Iyah da Shehu sai kula da shi suke yi sunyi-sunyi yaci abinci ma ya ki ci inda Inna ta dangana hakan da tafiyar su Malam Yahaya, idanun Shatu a kumbure yake alaman kuka ta sha, tana gama yi wa Iyah hidima ta cewa Iyah zata je gidansu Fatu, a dawo lafiya Iyah ta yi mata ta kara da cewa "karki jima dai kinga Abdul ba lafiya ga Yayanki ya fita karbo masa magani, kar a barni ni kadai da shi kinji?" a sanyaye Shatu tace
"To Iyah" ta saka kai ta fice, tana fitowa ta fara tafiya kenan sai ga Fatu, tsayawa Shatu tayi Fatu ta karaso wacce
ita ma idanunta a kumbure, hannu suka sha Shatu tace.
"Dama gurinki zani"
"Nima gidanku zanje mu koma kawai" a hankali suka juya Fatu tace
"Shatu jikina ne yayi sanyi ga wani tsinkewa da zuciyata ke yi inaji a jikina kamar wani abu ya samu Rashida" ta karasa tana sakin kuka, tsayawa Shatu tayi itama hawaye ya gangaro a idanunta tace.
"Tun farkawata gabana ke faduwa wallahi na rasa meke mun dadi, da ace ƙauyen 6illiri sun amince a kwana da duk damuwar zata zo da sauki" hawaye Fatu ta goge tace.
"Allah dai yasa sun wuce lafiya" da amin Shatu ta amsa suka koma gidansu Shatu da sallama suka shiga Iyah na rike da Abdul da ke ta faman amai da sauri Fatu ta karaso ta riƙesa Shatu ta ruga da gudu ta kawo ruwa sai da ya gama Fatu ta karbi ruwan ta wanke masa fuska Iyah tace
"Shiga da shi ciki Fatu"
"To Iyah" daki Fatu ta kai Abdul ta kwantar da shi ta lullube shi jikinsa sai rawa yake yi yana rawar ɗari ga zazzabi sosai a jikinsa.
Cikin tausaya wa Fatu ke yi masa sannu ko bude idanu ba ya iya yi.
Fitowa Fatu tayi ta zauna akan tabarman kaba kusa da Iyah ta gaisheta amsawa Iyah tayi tana tambayarta ya kafan Umma ta amsa da "alhamdulillah da sauki, dama Abdul bai da lafiyya ne?"
"Wallahi tun jiya dai da su Malam Yahaya suka tafi yake ta koke-koke ko a daren jiya bai yi wani bacci ba sai da kyar daga nan ya fara amai sai zazzabi inaga tunanin tafiyar sun ce da kuma kukan da ya yi ya haddasa masa zazzabi yanzu haka Shehu yaje amso masa magani a gun malam mai allo"
"Allah ya ba shi lafiya"
"Amin" Iyah da Shatu suka amsa, tashi Shatu ta Fatu suka yi suka shiga daki, jimani suka ci gaba da yi cikin sanyin jiki, suna zaune suka ji iska mai karfi kamar za ayi ruwa da sauri suka fito domin su kwashe kayan da Shatu ta wanke amma ina ba ruwa bane garin ne dai yau a hargitse, cikin al'ajabi Iyah tace.
"Ikon Allah, yau yanayin garin nan ya dameni, ga hadiri ba lokacin damuna ba ruwan kuma bai sauko ba"
"Wallahi yau kam garin sai a hankali ni da naji karan iska na zatan ruwan ne shiyasa na fito da gudu na kwashe kaya"
"Duk da haka kwashe ki kai su daki idan Allah yasa garin ya washe a sake fitowa dasu" da to Shatu ta amsa Iyah ta shiga daki Fatu ta taya Shatu kwashe kayan suka kai daki.Har aka yi sallar azahar ƙauyen lanbu tana nan dulum-dulum, malam mai allo ne ya fito kofar gidansa ya tsaya ya daga idanunsa ya kalli sama gabansa ya buga ya hadiyi wani miyau mai zafi a kirjinsa gabansa na fadiwa, meke shirin faruwa ne haka? a hankali ya juya ya koma cikin gida ya dauki allonsa ya hau rubutu.
Baba kuwa gudu yake zuba wa a cikin jeji har yanzu Inna sambatu take yi Musa kam bai iya cewa komai....
#AFUWA NI DAI MUNA BIKI NE
YOU ARE READING
JEMAGE🦇
ActionAmintattu guda uku daga aminan juna guda uku JEMAGE MAHAUKACI NE KO ALJANI? BURI UKU. sabbin litattafai masu cike da ruɗani da sarƙakiya karku sake a baku labari, ba free books bane paid ne amma cikin farashi mai sauki #500 dika ukun if payment ta k...