🦇🦇🦇 *JEMAGE.* 🦇🦇🦇
_MALLAKIN._
*ZAHRA ABDUL M AHLAN.**PAID.*
BOOK.
_3/2/2023_🪄*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
_da sunan Allah mai rahma mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga shugaba ja gaba Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa sallam da iyalan gidansa da Sahabbansa da shehunnai da ma magoya baya bakidaya har izuwa ranar sakamako, Ya Allah ka bamu ikon gama wa lafiya yadda muka fara lafiya alfarman Ahalil baitin Nabiy Rasulillahi S,A,W_💚
_~AMINTATTU GUDA UKU DAGA AMINAN JUNA UKU~_
*AISHA A YABO FULANI*
*RASHIDAT USMAN OUM NASMAH*
*ZAHRA'U ABDUL M AHLAN*
_PAID BOOKS CIKIN FARASHI MAI SAUKI_
_GUDA ƊAYA #200 GUDA BIYU #300 GUDA UKUN #500, AMMA PAYMENT TA KATI YA SHA BAMBAN DA TA ACCT, GUDA DAYA #300 BIYU #500 UKUN #600, BIYA KUDIN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKI 0006064512 Rashida Usman JAIZ BANK ko kuma katin waya ta daya daga cikin waɗannan lambobin_
08147537180
08162576936
08165550116
*Masu turo da evidence of payment wadanda suka yi transfer to acct ku turawa ɗaya daga cikin mu, don girman Allah banda vtu inde kika yiwa ɗayan mu vtu to kinyi sadaka Anty☺️ muna godiya gareku masoya*🪄_SADAUKARWAR LITTAFIN *JEMAGE* GA KAWALLIYA *RASHIDAT USMAN UWAR NASMAH* INA MIKI LUV DOMIN ALLAH, BABBAN KAUNA ZUWA GAREKI AMINIYA *AISHA FULANI* RABBI YA BARMU TARE_
_LITTAFIN *JEMAGE* KYAUTA CE GA SISINA KUMA TAWAN *KHADIJA SANI JOURNALIST* INA MIKI SAHIHIN KAUNA TAWAN❣️🥹 INA ROƘON ALLAH YA SHIGA LAMARIN KI,ALLAH YA IYA MIKI ALLAH YA DAFA MIKI ALLAH YA BIYA MIKI BUKATUNKI NA ALKAIRI FIDDUNYA WAL AKHIRAH, ANA UHIBBUKI YA UKHTY_❤🩹
*TSOKACI*
_LITTAFIN *JEMAGE* KIRKIRARRIYAR LABARI NE, DA FATAN ZA A DUBA DARASIN DAKE CIKI_*GARGAƊI*👂🏼
_BAN YARDA A JUYA MINI LABARI TA KO WANI SIGA BA, BAN YARDA A ƊORA MINI LITTAFI A YOUTUBE CHANNEL BA TARE DA IZININA BA, SO PLS A KIYAYE._
===========
Follow me on my wattpad @Fateemah0.
==============
*MARUBUCIYAR.*
1-HALITTA DAGA ALLAH NE.
2-GUDU A JEJI.
3-SHUHADA.
4-NIDA ƘANNEN MIJINA.
5-WA'YA KASHE ZAHRA'U? #200.
6-COLONEL UBAIDULLAH.
7-ITA CE ZUCIYATA #200.
8-SAMIMA (MACIJIYA CE).
9-DA NA SANI NA.
10-GAWURTACCEN SOJA #300.
11-BADAWIYYAH.
12-AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE) #300.
13- AHLAN #200.
14-DSP ALIYU HAIDAR.
15-SARKIN RUWA #200.
16-MAMIYOTA CE #200
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆
FREE PG-1️⃣5️⃣▶️1️⃣6️⃣
Saurin kallonta Baba ya yi ya kasa magana sai zufa da ta yanko masa lokaci guda dan ya fahimci ya yi ta6argaza, Musa ma shuru ya yi dan ba huruminsa bane magana a wannan matakin,
"Malam sunan Jalo naji ka ambata fa? miye hadinku da Jalo da kake cewa ba zai barku ba da wasu ƙauyuka?" cikin son Inna ta bar zancen ya ce
"Sabida ina zargin Jalo ne a halin da Rashida ke ciki" da mamaki Inna ta ce
"Me Rashida zata aikata wa Jalo da har zai maidata haka ya sakata a gaba? ban taba zatan ma Rashida ta taba zuwa jejin zarga ba da har..."
"Don Allah Salame ki kula da Rashida ki daina wani magana indai bata shafi ta yadda zamuyi addua mu tafi lafiya mu dawo lafiya da dubbanin nasarori ba" shuru Inna tayi bata kuma cewa komai ba, Baba ya sauko Musa ma sauka yayi akan dokin zuwa anjima can sai ga wata yar budurwa da katon kwarya a saman kanta ta dibo ruwa, sallama Musa yay mata ta amsa tana kallonsa,
"Don Allah 'yan mata ki taimaka ki mana jagora zuwa gun fadar sarkin ƙauyenku" cikin harshenta da kana ji kasan bafulatana ce ta ce
"Mu nan bamu da Sarki sai dai mai unguwa" da mamaki Musa ya ce.
"Akwai ƙauyen da bata da sarki ne dama?"
"Sarkin ƙauyen 6illiri ne ke sarautar kauyenmu shiyasa nace maka ba sarki sai mai unguwa" gaban Musa da Baba ne ya buga suka fiddo idanu har ma da Inna dake zaune,lallai an gudu ba a tsira ba kenan, cikin karfin hali Musa yace.
"To dan taimaka ki mana jagora zuwan gun mai unguwa din"
"To ku jira ni na kai wa Babata ruwan da ta aikeni"
"Ba matsala" Musa ya faɗa yana gyara tsayuwa ita kuwa tayi gaba, bata jima ba ta dawo ta samesu tace musu su je. har fadar mai unguwa ta raka Musa da Baba yayinda ita Inna tana zaune a amalamke rungume da Rashida bata bi su Baba fadar mai unguwa ba, har kasa Baba da Musa suka duka suka kwashi gaisuwa da alama mai unguwar mutum ne mai saukin kai a yadda ya amsa musu gaisuwar da suka yi masa,ya amsa yana tambayarsu ko lafiya a wannan lokacin? Kuma daga ina suke me ke tafe dasu?nan Baba ya shaida masa daga ƙauyen lanbu suke suna son zuwa ƙauyen sanda ne wannan ɗan shi ne babba matar sa tana can da 'yarsa marar lafiya wacce suna da yaƙinin aljanu ne suka kama ta shine zasu kaita gun malam Habu mai carbi, shuru mai unguwa ya yi yana nazari sai zuwa can ya ce
"Ai ƙauyen 6illiri ya kamata ku yada zango ba anan ba" sake yin ƙasa da kai Baba yayi yace
"Allah ya taimake ka ƙauyen 6illiri sunki amincewa da mu kwana a ƙauyensu ka ji dalilin da yasa muke so mu fake anan, nayi maka alkwari asuban farko zamu kama hanya" jim kaɗan mai unguwa ya yi kafin ya ce ba matsala, shi da kansa ya yiwa su Baba masauki ya ce yaje ya taho da iyalin na shi,sosai Baba ya yiwa mai unguwa godiya yana adduar kar wani munafuki yaje ya sanar da ƙauyen 6illiri wanda wannan tunanin ne ya haifar musu da sanyin jiki. Koda suka dawo a sanyaye Inna ta ce
"Sun ki amincewa ko?"
"A'a sun amince amma gudun kar mu jawo musu matsala ana asuban farko zamu tafi kan mu karasa fita daga jejin mai rabon ganin baɗi yamma bata yi ba amma tabbas rana zata yi da ace akan doki ne zamu iya gudu amma kuma wannan amalanken bazai iya gudun da doki ke yi ba, sabida haka idan Allah ya kaimu gobe duk abinda zamu gani a jejin mai rabon ganin baɗi mu rufe idonmu kar mu ji tsoro gudun abinda zai dawo akanmu" jinjina kai Inna da Musa suka yi,Musa ne ya saba Rashida a kafaɗa suka nufi masaukin da aka basu asirrance dan gaskiya shima mai unguwa a tsorace yake da ya ji Baba yace masa daga kauyen lanbu yake uwa uba kauyen lanbu da 6illiri ba shiri Suke yi ba gaba ce tsatstsaura a tsakani abinda yasa ya ba wa su Baba masauki ya san kauyen lanbu suna da mutunci dan yaronsa ya taba kwana a kauyen lanbu da yake ya fita birni yana kasuwanci ya ba shi labarin karamcin 'yan lanbu idan bai manta ba ma ya gaya masa har aboki ya yi a lanbu.
Dik da su Baba suna da guzurinsu na abinci amma hakan mai unguwa yasa aka kai musu abinci cikin mutunci, sun kuwa ci sunyi godiya.
Koda aka yi sallar isha'i su Baba a daki suka yi dan ba kowa suke son yasan suna kauyen ba idan wani yayi shuru wani bazai yi ba.
Da yake daki ɗaya suke haka suka kasa bacci Baba yace da Inna ita ta kwanta tace a'a bata jin bacci.
Dare ya tsaga tsakiya mutan gari duk an kwanta dare mahutan bawa, su Baba ma a zaune suke amma kowannensu na gyangyaɗi, cikin gyangyaɗin ne suka ji yo ihu wanda firgigit suka zabura suna zare idanu, banda sautin muryoyi ba abinda ke tashi da sauri Baba da Musa zasu fita Inna ta hana ta riƙe hannunsu tana girgiza kai.
"Malam don Allah karku fita" Baba zai yi magana wata uwar tsawa da aka saki sai da suka duka nan take dakin da suke ciki ta girgiza, gaban Baba ne ya buga ya dago yana tunanin anya wannan farmakin mutane ne kuwa? Cikin kiɗima Baba ya ce
"Anya wannan tashin hankalin na mutane ne kuwa?"
"Nima haka nake ji anya Baba na mutane ne ji tsawan bai kama da na mutane ga kum....!" maganar da Musa bai idasa ba suka ji wani sautin guɗa faka-faka, da sauri Baba da Musa suka fice, suna fitowa suka fara haduwa da gawawwakin mutane a kwance, ga garin ya kuma baƙi kamar hadiri-hadiri ne a'a guguwa ne,nan sautin murya ya hau fitowa kamar haka.
"Shugabaaaa ya aiko mu muu daukoo masaa 'yar gidan malam Yahaya" jin abinda ake cewa yasa hantar cikin Baba kaɗawa, Musa kuwa motsin arziki ya kasa yi. Baba na tsaye wani baƙin hayaƙi ya gani ya dinfaro shi yayinda hayaƙin yayi zanen takwabi ganin haka yasa Musa da ke tsaye kamar an dasa shi yayi hanzarin tare wa dan abin ya shiga jikinsa da karfi Baba da Musa suka rintse ido suna kalman shahada suna jiran na Allah ta kasance dasu hakan bai kai ga faruwa ba sai suka ji sautin iskan fuka-fukai da sauri suka buɗe idanunsu abinda suka gani ne ya gigita su, su JEMAGE ne dayawa wanda a ƙiyaste sun kai dubu daya, wani layi suka buga ga wani guɗa dake tashi,banda rawa ba abinda jikin Baba da Musa ke yi sai kakkarwa nan su JEMEGEN suka buga jere suna waina fuka-fukansu, tashin hankali ake yi ba na kaɗan ba yayinda tsayuwa ta gagari su Baba suka duƙa kasa suka ƙanƙami juna suna son zuwa duba Inna da Rashida amma ba hali sabida su jemage da suka yiwa saman kansu ƙawanya, ga wani sauti da ke tashi kana ji kasan yaƙi ake yi amma abinda ya daurewa su Baba kai basu san da su wa jemage ke yaƙi ba, suna nan durƙushe har alfijir ya fara ketowa zuwa can anjima jemagen suka fara raguwa suna watsewa, su dai su Baba suna jiran mai kasancewa ta kasance dasu idanunsu a rintse duk adduar da yazo ransu yi suke yi,zuwa wani ɗan lokaci suka ji tsit ba hayaniya ba komai, buɗe idanunsu suka yi hankali a lokacin gari ya fara haske, koda suka buɗe ido ba kowa sai gawawwakin jama'a kwance a gabansu, kafin ɗaya daga cikinsu ya buɗe baki ihun Inna ne ya tashi wanda yasa gaban Baba da Musa bugawa da karfin gaske, Ihun Inna suka sake ji tana kiran sunayensu tare da ambatar sunan Rashida .....#DA BABU GARA BA DADI INA BUSY NE YASA KU KA GA PG DIN KAƊAN,ZAN KOKARTA TYPING GOBE IN SHA ALLAH.
#Comments
#share
#GarkuwarMacizai ce🪄
YOU ARE READING
JEMAGE🦇
ActionAmintattu guda uku daga aminan juna guda uku JEMAGE MAHAUKACI NE KO ALJANI? BURI UKU. sabbin litattafai masu cike da ruɗani da sarƙakiya karku sake a baku labari, ba free books bane paid ne amma cikin farashi mai sauki #500 dika ukun if payment ta k...