...09...

621 14 0
                                    

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[09]


Runtse idona nayi,bana ma son naga mai zai kasance.
Buɗe ƙyauren ɗakin yayi ya shigo,da farko bai kulada ni ba sai daya waiwayo tukunna muka haɗa ido.
Kallon mamaki yake bina dashi,nasan bazai wuce nazari yake ba akan mai yakawoni cikin ɗakinnasa..
"Keeee"
Ya faɗa cikin shaƙyƙyƙyiyar murya,wacce take ɗauke da gajiya da kuma takaici.
Shuru nayi ban amsa ba,dan banida wannan ƙarfin halin.
"Wai ba magana nake miki ba,ko ke kurmiya ce bakya magana?"
"Uh.....uhm... Iyee na'am"
"Me ya kawoki cikin ɗakina,duk filin dayake cikin gidannan ki rasa inda zakiyi burki sai cikin ɗakina,mai kike nufi wai anan zaki zauna"
"Ahah dama inna....."
"Mtsww tashi ki fita ki bani waje,idan kuma kika sake na ƙara ganin ƙafafunki a kusada sansani na......saina karya dukkan ƙasusuwan jikinki na babbakeki na ciyar da su durwa"
Me wai ni irin wannnan kashedin haka..
Miƙewa nayi daga kan katifar ƙafafuna suna rawa,haka na jasu zuwa bakin ƙofar,ina jin idanuwansa akan ƙeyata kaman zasu bula su shige,ban waiwaya ba harna fita daga cikin ɗakin.
Tafiya nake kaman ina kan glass har na isa bakin ɗakin inna Mairo. Ƙwanƙwasa mata nake a hankali harna fara da ƙarfi ganin bata buɗe ba.
Cikin muryar bacci tabude kofar tana kallona,nima kallonnata nake har sannan hankalina bai gama kwanciya ba.
"Sumaimah lafiya kuma na ganki anan,gojen bai dawo bane koh......"
"Yadawo koroni yayi,yace idan na sake zuwa kusada ɗakinsa sai ya kasheni"
"Me kisa kuma wacce iri?"
"Dan Allah inna karki sake cewa ba koma,idan kika maidani zai kasheni nikam....."
"Kinga kwantar da hankalinki,shigo nan mu kwanta,idan gari ya waye saina ɗauko miki kayanki a ƙofarsa,sanda komai ya daidai ta in yaso saiki koma"
Jinta kawai nake lokacin dana afka cikin ɗakinnata,dan dama abinda nakeso kenan nakuwa samu,zama da ita daram ba ruwana da wani ɗakin goje,haka kawai ana miji miji ya kasheka a banza..
Gado biyu ne a ɗakinnata,mai rumfa da kuma ƙarami na ƙarfe,shima akwai katifa akai saidai ƙarama,tsayawa nayi inna kallon ɗakin na jiyo muryar innan.
"Ga nan gado saiki kwanta,da su Atika ne suka kwana a kai,to yanzu sun koma wajen uwarsu tunda suka dawo. Sai ki dunga kwanciya anan kafin komai ya daidai..
Ɗaga mata kai kawai nayi banyi magana ba,ina jin haƙarƙarina akan katifa na saki ajiyar zuciyah,koba komai iya yau kam ai na tsira.

[Goje a Mahangar Gani]

Dawowa ta kenan garin cikin darennan,kwana guda da yini bana nan ina can sansanin ƙungiya BC  sun gayyaceni na zama ɗaya daga cikin ƙungiyarsu. Tun wancan satin suka turomin takardar gayyata,sannan basu yarda naje da kowa ba idan zanje wajensu,saboda tsaro.
Fitinanniyar ƙungiya ce data addabi manyan ƙasa dama cibiyar binccike,saboda ƙungiyar tayi ƙaurin suna wajen fashin manyan bankuna da kuma gidajen ƙusosin ƙasa..
Kowa yasan labarinta da kuma irin aika aikarta,saidai babu wsnda yasan sunzo sun buya a wannan ƙungurumin daji.
Abune mai wahala su ɗauki wani yazama ɗaya daga cikinsu,saidai idan sun bincika sunga ehh ya cancanta.
Kamanni da labarin salona ya isa garesu,banida wani sha'awar shiga ƙungiyar,amma kuma ban sani Meyasa wani abu na cikin kaina yake kwaɗaita min shiga ɗin,koba komai baifi ƙara kwarewa ba,kuma dama irin wannan farmaki mai aji nakeson naga inayi..
A bakin jejin su na tsaya jiya,daidai inda suka kwatantamin,saida nayi kaman sa'a guda a wajen kafin naga wasu majaze da baƙaƙen kaya sun nufo inda nake..
Wani baƙin ƙyalle suka yafamin a kaina,kana suka riƙe hannu na muna tafiya.
Cikin duhuwa muke shiga har muka zo daidai wani bakin wani kogon ɗutsi mai masifar girma.
Wasu dakaru ne a wajen a tsaye da manyan manyan bindigogi a hannunsu..
Shigewa mukayi cikin kogon mai lunguna da saƙo kala kala.
Wani sansani muka zo mai matsakaicin fili da mutanen da zasu kai shida a wajen,dukkansu baƙaƙen kaya ne a jikinsu,saidai akwai guda ɗaya wanda shi nasa kayan ja ne.
"Barka da zuwa wannan ƙungiya Goje,mun samu labaranka da yanda ka kawar da yaronmu na garinku,da farko munso yin maganinka,sai kuma mukaga hakan dakayi ma daidai ne,dan kafishi jarumta da kuma kwarjini.
Munyi farinciki daka karbi gayyatar mu kakuma yarda cewar zaka........"
"Dakata a takardar ba'a nuna karbi aikinku ba,kawai takardar amsa gayyata ce,ko banyi daidai ba"
Nafaɗa ina kallon cikin idonsa,dan haka kawai naji banji tsoronsa ba,duk kuwa da yanda suffarsa ta zama abar tsoron..
Tsuke fuska yayi,lokaci ɗaya kuma yasake ta tareda yin shu'umin murmushi.
"Ehh kuma hakane ka faɗi gaskiya,rashin tsoronka ya burgeni. Kaman yanda kake gani nan shine sansanin BC,kuma basai nayi bayani ba kasan menene aikinmu tuntuni. Nine mai faɗa a ji na huɗu,akwai sauran mutane uku a sama na. Shugaba da kuma mataimakansa. Babu wanda yasan wanene shugaban wannan ƙungiyar,shugaba na biyu kuma ni  kaɗaine na sanshi sai Shugaba na uku zamu haɗaka dashi idan ka amince da zama ɗayan Mutane biyu da suke kulada reshe biyu na wannan ƙungiyar,Idan ka amince da wannan aiki nan gaba zamu iya baka damar riƙe sansaninka na garinku. Wanda kana da wannan damar idan ka nuna mana waye kai,saika haɗu da shugaba na uku. Abinda kuma shine muhimmi bamu yadda wani yasan da wannan maganar ba"
"Harshe zaku yankemin in wani yasani? Da kunsan inada wannan inaga bazamu zo nan daku ba. Ni zan tafi in kun gama faɗin abinda kuke ganin yakamata na sani"
"Uhm ba matsala zaka iyah tafiyah,kanada damar yin tunani har nan da kwana uku,zuwa sannan zakaga ɗan aikenmu izuwa gareka"
Daga haka nayi sallama dasu muka fito daga wajen nida wanda suka rakoni.
Ajiyeni kenan da sukayi yanzu a ƙofar gida suka tafi. Garin yayi tsitt bakajin komai sai ihun mutanennamu wato karnuka,da alama dare yayi kenan.

SANADIN CACAWhere stories live. Discover now