...11...

558 15 0
                                    

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[11]

[Sumaimah a mahangar gani]

Kwanci tashi hausawa kecewa a sarar mai rai,yau satina a guda kenan a gidan aurennawa.
Abubuwa da dama sun faru,wanda duk yawancinsu na rashin daɗi ne. Mutanen gidan kaman dama jira suke nazo,kowa ya daina komai a gidan na aikace aikace,inka ɗauke awara kawai da gaji takeyin kayarta. Itama wani lokacin nice ke haɗa wutar,ko dolene ma in mutum yaga abinda nake ya tausayamin kuma yaji haushina,nima haushin kannawa nakeji,to amma ya zanyi. Yanda gaji ta faɗa hakane ita ke ciyar da gidan kusan,nima ta wani wajen inaganin ƙoƙarinta akan hakan.
Dan haka dolene nayimata aikace aikace,duk da kuwa sunyimin yawa,ranar dana gwada cewa bazanyi ba zage zage tafara da gori,wanda duk akan inna mairo ya ƙare. Nikuma tausayin dattijuwar nake sosai,shiyasa nakeyin komai da jikina zai ɗauka indai gaji zata ƙyalemu.
A bangaren goje kuwa bazance lafiya ba,har yanzu babu abinda dai ya haɗani dashi,tunda ba zaman gidan ma yake sosai ba,in ya shigo ma iya karnukansa ne a gabansa. Abinda nake masifar tsoro kenan,hakanne yasaka inna tace ya fita dasu waje.

Yanzu nagane da wuri nake gama ayyukana na samu waje na zauna,muyi ta hira da inna,kwana biyun farko dana ta'ba soda hannuna ya tsage danayiwa gaji magana cewa tayi ita taga damar siyah. Inna data kulada hakanne ta bani kuɗi na siyi sabulu.
Ɗakin inna  nufah ina ta tuna tunane wanda suka zama aikina na kodayaushe,tun ina saka ran mafarkin samun rayuwa mai sauƙi yanzu na cire wannnan a raina,haka ƙaddara take kuma a haka zan ƙare inaga.
Turuss nayi a bakin ƙofar,inna nasamu tana shishshirya kayanta a wani bakko,wani razana nayi kaman ɗan da uwarsa zata tafi ta barshi.
"Inna ina zakije?"
Nafaɗa a sanyaye.
Itama diriricewa tayi,kaman da alama batasan zan shigo ɗakin ba.
"Uhm ɗiyar nan wlh garinmu zanje,ɗan ƙanina ne yayi aure sannan kuma anyi mana rasuwa wancan satin,da tun wancan satin naso tafiya,to kinga bazan tafi na barki ke kaɗai daga zuwa ba,shiyasa nace barina dakata saikinyi ko satine tukunna"
Haɗiye hawayena nayi,banason tafiyar tata,amma kuma wacece ni dazanyi sanadiyyar hanata zuwa taga danginta. Cikin dauriyah na gyara muryata na tambayeta.
"Inna inkin tafi yaushe zaki dawo?"
"Uhm zanyi kaman sati biyu tunda ina tunanin na barki,amma da wata biyu nake ko ɗaya"
Datace sati biyu har zan roƙeta ta rage,saikuma naji ashe dannice ma shiyasa zatayi sati biyun.
"To shikenan inna Allah ya dawo dake lafiyah,amma kunyi sallama da gojene,nasan yau ba lallai yadawo ba sai dare"
"Ehh nasani ai shiyasa mukayi maganar dashi jiyah"
Gyalenta tasaka na biyota zuwa waje,ƙofar gaji tashiga wadda kaman kullum take fama da yaranta,Atika bata nan tafita talle.
"To gaji nizan je gida,sati biyu zanyi na dawo,don Allah gaji ki kulada itah,ki daina yimata wannan abin dan Allah yabaki dama,kar watarana goje ya tareki bazakuyi da daɗi ba......."
"Haba mairo yakamata ki kama girmanki fah,fisabillillahi mai nayiwa yarinyar nan,dan kawai nace ta tayani aikace aikace,in batayimin ba akwai yanda zan amfaneta ne,kawai saidai in ta ciyar da itah. Dazakice goje yagani shima nasan babu abinda zaice,tunda kowa yasani dama dan haka ya yarda tazo gidan,saboda da dunga aiki ta fanshi kuɗin da ubanta yakasa biya a caca"
Jan ƙafafuna nayi na bar ƙofar,kunnuwana bazasu iya jure jin waɗannan kalamai ba masu matuƙar ɗumi,duk da cewar nasan gaskiya take faɗa ba ƙarya ba.
A bakin fita ƙofar gida na tsaya ina jiran inna harta fito,murmushi na ƙaƙalo nayi mata lokacin da muka haɗa ido,don banason tafara bani wannan haƙurin,itama tasan hakan shiyasa bata ɗagomin zancen ba.
"To Sumaimah ni zan tafi saikuma Allah yasa na dawo,ki duba ban kaɗen katifata akwai ɗari biyar ki dunga siyan koko da safe"
Kukane ya kufcemin lokacin data fice daga cikin gidan ta tafi.
Shikenan saini kaɗai a gidan,in kasheni ne ma zasuyi daga goje har gajin babu mai ƙwata ta a wajensu.
Da gudu na nufi ɗakinnamu nida itah na faɗa akan katifa,kuka nake ta rubza har saida nayi na ƙoshi kaina yayi ciwo kafin nai shuru.
A haka bacci ya ɗaukeni bansani ba.
Ƙiran sallahr azahar ne da wani masallaci gefe damu suka ƙwallah ya tasheni,hamma nayi ta yunwa kafin na saƙƙo daga kan gadon innan.
Har na idar da sallah cikina yana ƙara na neman abincin,ganin abin baxai kainiba yasa na zari takalmina na nufi ƙofar gaji.
Rabon abinci take a kwanuka ƙanana,kowa sai an zuba masa nasa.
Muna haɗa ido da itah ta watsamin harara tareda cewa.
"Mayyah kawai,ni banga amfanin zuwanki gidannan ba sam,shi wanda ya ajiyeki ko oho"
Naji haushin abin amma ya zanyi,mutumin daya ke nema ina zayyi iyayi.
Cakuɗaɗɗiyar jallof ɗin ta yafata a kwano a turomin gabana.
"Gashinan wlh kaɗan zan baki,tunda ko ɗora girki bakiyi ba yau,wannan na wanke wanke da sharar da kikayi ne"
Ɗauka nayi bance komai ba na fita daga ƙofar,a raina ji nayi gwanda ma gidanmu,ko ba komai ranar girkin ammi mutum zaici abinci ya ƙoshi,amma kuma gwanda ban babu jarabar su inna rammah saina gaji,sannan kuma babu zuwa talle kullum.
Ɗakin innan na koma na zauna,kallon abincin nake kaman za'a bawa ɗan yaye.
Nasaka hannu kenan a ciki na jiyo muryar Shareefah a kofar gidan,sallama take tayi amma bata shigoba,da alama tsoro take kar goje yana gidan.
Fitowa nayi da sauri na tareda ina murna,bayan sati guda wani ya tuna dani ya nemi inda nake.
Ɗakin innan muka shiga da ita,sai ɗari ɗari take idonta akan ƙofar goje,nasan shi take dubawa ko zata gani,amma saina sake tambayarta.
"Wakike nema ne Shareefah kike ta juyawa?"
"Kutt harma tambayata zakiyi,wannan mijinnaki mana,ke kina gida bakiji abinda yayi limamin gari ba koh"
Zaro ido nayi tareda jijjiga kai,bansan mai yafaru ba dagaske,taya zan sani ina zaune a cikin gida.
"Bansani ba mai yafaru,mai yayiwa liman ɗin"
"Bawai liman ɗin yayi wa ba,ɗan gidan liman fah ya ɗauke,har yanzu bai dawo dashi ba wai sai yayi sati a wajensa,anyi magiyar amma shuru,kinsan in suka kai mutum wannan madakatar tasu kuwa saita Allah"
"Mai.....mai ɗan liman ɗin yayi masa"?
"Bai faɗi mai yayi masa ba,kawai cewa ake wai dan liman ya zagesu ne a mubarin huɗuba"
Hannayena karkarwa suka farayi,dan kawai anyi maganar ka a mumbari saika saci ɗan liman?.
A tabarmar ɗakinna zauna dana tuna ashe a tsaye muke shigowarmu ɗakin. Itama zama tayi tana cigaba da bani labarin wane hali garin yake ciki.
Dungurar kwanon abincin nayi da ƙafata,sai sannan na tuna ashe fah abinci nake. Kwanon na kawo tsakiyar mu,cikeda kunya nayiwa Shareefah tayin abincinnawa.
Itama ta kulada hakan,dan kallon tausayi tafara yimin,kafin ta jijjiga kai alamar bazata ciba.
"Uhm Sumaimah abin ya ɗauremin kai,ya naga kayanki kuma a nan ɗakin?"
"Anan nake kwana ai,mai kike gani"?
"Abubuwa dayawa,Sumaimah nasan mijinki abin tsoro ne kowa yasan haka,amma anan kam naga rashin wayonki da rashin dabararki wacce da nasanki da itah. Shin idan baki tunkareshi ba kin gyarashi taya zakiyi rayuwa mai kyau,wlh Sumaimah mutane irin goje idan suka gyaru matansu suna morewa,kuma ko wannan abin dayake a gari zai bari,kowa fah ke yake tsammani kiyi tasiri a rayuwar goje,saboda gani ake silar shiryuwarsa ce a aurenki,amma kuma ki gudu ki dawo ɗakin innarsa da zama? Ko.........."
"Kiyi haƙuri kiyi shuru haka Shareefah,nikuwa nasan cewar akwai haƙƙinsa akaina,amma karki manta bafah nice na gujeshi dan raɗin kaina ba,yacemin idan ban fitaba zai hukuntani,idan kuma nasake dawowa saidai wata bani ba. To kece zakijene iyee faɗamin"
Sakin ajiyar zuciyah Shareefah tayi kafin tace.
"Ehh to kuma hakane,amma mai zai hana ki fara wasu dabaru dazasu janyo hankalinsa gareki a sannu"
"Kaman me kike gani zanyi,ni tsoronsa nakeji Shareefah,saidao tunda nazo gidannan bai tabayimin komai ba na mugunta,sai gaji ce dai......"
"Uhmm na gaji mai sauƙi ne idan har kika fahimtar dashi yagane muhimmancinki,shizai yimiki maganin gaji,koda da wahala amma ki gwadah kinji,komai zaizama labari Sumaimah"
Naji daɗin hirar da mukayi da Shareefah sosai,duk da bata daɗe da gidan ba ta tafi..
Bayan ta tafi har na tashi zanyi wanka naji sallamar yaro.
Jikina yana rawa nafito daga ɗakin,ƙanin Shareefah ne nasanshi a islamiyyah.
Kwano ne a hannunsa ya miƙomin yana cewa..
"Addah Sumaimah waigashi inji addah Shareefah"
Karba nayi cikeda sanyin jiki kafin nace yayi mata godiya.
Bayan koma ɗaki buɗe kwanon nayi,shinkafah da miyah ce a ciki. Babu bata lokaci kuwa nafara hannu baka hannu ƙwaryah,idona har zubar da hawaye yake,ban taba zaton zan samu abinci mai ɗumi a lokacin naciba..
"Nagode Allah yasaka da alkhairi Shareefah"
Nafaɗa akan la'b'baina.
Bayan na tashi abincin fitowa nayi da kwanon zan wanke,haɗa ido mukayi da wasu maza kaman guda biyar,kowa da kalar tafiyar dayakeyi.
Hankali kwance suka shigo gidan kaman ɗakunan iyayensu. Ina kallonsu har suka shige ƙofar gojen. Can bayan shigarsu shikuma ya shigo gidan,shida wannan mutuminnasa da indo tacemin sunansa Tunga.
Magana mai muhimmanci sukeyi da alama,ganin yanda suka tattara nutsuwarsu waje ɗaya.
Bayan sun gama maganar wucewa goje yayi,ko inda nake tsaye da kwano a hannu bai kalla ba. Ɗauke idona nayi daga kallon dana bishi dashi,charaf muka haɗa ido da Tunga,lokaci ɗaya tsoro yakamani,kar naje yaga hararar danayi masa ya faɗamasa ya babbakani. Saidai maimakon irin fuskar sauran shi murmushi yayimin saina kwantar da hankalina kaɗan.
Ƙarisowa inda nake yayi tareda cewa.
"Sumaimah koh?".
Ɗaga masa kai nayi a tsorace.
"Kidaina wannan tsoron haka,yaƙin dayake gabanki baya buƙatar tsoro,kuma ma kallon dutse kukeyiwa pillow dan dun ganshi baƙiƙƙirin a launi,macijin da kike tsoro bashida dafi a bakinsa,koda yanada shima baya saran wanda suke nasane,kicire tsoro ki tunkareshi,ta hakanne maimakon ya sareki saidai yakareki daga masu kawo miki hari. Nizan tafi munada meeting ne,ki riƙe zancena kana kiyi nazari akai"
Kallo nabishi dashi har ya shige wajenda sauran suka shiga,jijjuya maganar tungan nake a cikin kaina ,haƙiƙa sunada nasaba da abinda Shareefah ta faɗa min.
Nariga na shigo gidan,hanyar fita daga shikuwa ban ganshi ba,in hakane kuwa yazama dole na dage matuƙa wajen kawo mafita.
Harkar gabana nacigaba dayi,ina jiyo hayaniyarsu a ƙofar,dan ba ni kaɗai bama har gidan ma ana jinsu ta ko ina.
"Allah yasadai ba tattaunawar kashe wani suke ba"





Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

SANADIN CACAWhere stories live. Discover now