6

55 6 1
                                    

Da sallama a bakinta tashigo gidan, duk a gajiye take ga yunwa da ke kwakularta, yau tunda suka shiga lectures ba su wani sami interval mai yawa ba, gashi ita kuma bata son chin abincin makaranta, ba ma za ta iya cin abinci ba ne a gaba mutane da yawa although su Safiya sun dage sun bama cikin su hakinshi, itakam kasawa tayi.

Cikin gidan ma ba wani mutane domin ko duk suna ciki duba da an rigada anyi maghrib, sai Yan daidai ku ne a waje wa'inda ba su gama dafa abinci ba. Mace daya ce a cikin mataye ukun dake compound in ta amsata da fara'a a fuskarta, sauran ko sai wani daddaga hanci suke suna wani mata kallon tara saura.

" Zahida sai yanzu aka dawo ".

" eh fa maman hidaya, wallahi yau lecture har shida, kinsan kuma yanda ake wuyan samun abun hawa in shidan nan tayi". Ta fada a dan shagwabe fuskarta na nuna gajiyan da tayi.

Murmushi maman hidaya tayi tace.

" ai daman karatu sai da wahalar, ai ban inda aka taba karatu da sauki, ke dai Allah ya bada sa'a, ya sawa karatun naki albarka".

" amin Maman hidaya, barin shiga ciki na dan watsa ruwa ko na ji daidai"

Sauran matan biyu sai wani cikaro baki suke daya daga cikin su ma mai suna laure budar bikinta sai tace.

" dadai ba'a san asalin balbela ba da sai tace daga misra tafito. "

" wai ni da yar ruwa " dayar mai suna Saratu ta karasa, nan suka saki shewa har da tafawa.

Itadai zahidan ko nuna ta san da zaman su ma batayi ba, kuma in da sabo ta saba da halin Yan hanyan gidansu. Su wajan goma ne ke haya a gidan amma zata iya cewa befi mutum uku ba ita da mahaifiyar ta ke mutunci da. Daga Maman hidaya, sai Maman Sadiya wace sadiyan ma si'ar zahida ce kuma suna dasawa da ita sosai, sai kuma Maman walida. Amma duk sauran sai dai hantara da kyara yake hadusu da ita.

Ita bata san me ta taba musu a rayuwan nan ba da suka sa mata karan tsana, gwanda in Sauda ta tsaneta Wannan sabida mijin saudan ya taba ce ma zahidata yana sonta, ita kam Zahida ma ko bashi fuska batayi ba balle ma ya dauka zata amshi tayin shi. Amma still a haka sauda ta tsane ta tsana ne girma.

Shiga cikin dakinsu tayi da sallama a bakinta, mahaifiyar ta na zaune a kan doguwar kujera ta sama TV ido tana kallon arewa24. Amsamata Mama tayi tareda juyowa ta kalli yarta with mirth.

" Sannu da dawo yar Albarka ".

" wash " tace tana zama gefan mamarta.

" sannu mama ya Aiki, wallahi duk na gaji" ta fada tana mai cire hijabin jikin ta, zata yar a qasa kawai sai Mama ta cepke.

" kinga bana son kazanta ".

Bata fuska tayi . " kai mama, meye kazanta kuma a nan ".

" kazanta ne mana tayi zaki cire kaya ki yarda a qasa bayan akwai sif in da zaki iya ajiye wa a ciki. Haka zaki je gidan Aminun kina yi, aikam ze raina ki ".

" kai mama ni dai ai kinsan ba kazama bace" ta fadi a shagwabe.

" toh ai zubar da kaya a qasa shima siffar kazantace "

Tashi tai daga zaunen da take rike da hijabn a hannun ta.

" toh shikenam mama na ji, barin je in watsa ruwa. " ta fida tareda fara dosar cikin dakin.

" wai mama me a ka dafa ne yau " ta juyo tayi Wannan tambayar.

" masoyiyarki akai, shinkafa da waka, yau harda soyayyan kifi ma, da salad " Maman tafada da murmushi akan fuskarta.

Yau ta samu cinikin nika sosai shiyasa ta shiga kasuwa ta dan yo musu siyayya daman kuma jiya kawun Zahidan ya kawo mata kudin hayansu, sai ta aje wani a bankin domin makarantar zahida wani kuma tayo sarin yan atampopi da take siyar wa.

Abinda rai ke so. Where stories live. Discover now