prologue

435 14 0
                                    

Sanyin dare ne ya mamaye garin, ga wani iska mai dadi dake busowa tana shiga ta cikin lungu da sakon da iskar zata iya bi. Wani gida ne babba amma daga gani gidan hayane domin ko kofofine wajan guda goma, wani da gulop a gaba wani kuma babu. Gidan tsit kamar ba kowa sai de qarar gen da ke tashi a ta wani bangaran, Wanda ke nuni da akwai masu dan hali a cikin su, tsakar gidan nada girma, Wanda har bishiyar mangoro ce shuke a wajan daga gani tayi shekara da shekaru domin ta girma sosai, gidan fes fes da shi kamar ba na haya ba daga gani dai kasan masu hayan gidan na da tsabata. Wani daki na uku da ke a hannun dama, Wanda windown shi a bude yake, hakan kuma ya bawa iskar daman shiga ciki tana sanyaya ma na ciki, kana iya ganin hasken wutan candle dake a cikin dakin.

Daki ne mai ciki da parlor, wanda aka fentashi da blue paint. Sai kuma wata yar tv dake a kan wani dan teberi tareda dvd akan saman ta, sai kuma kujeru biyu, daya doguwa daya kuma karama wacce daga gani ta ci duniya. Leda ce malale a cikin parlor ta kai har cikin dakin ma mai dauke da gado dan madaidaici, sai kuma sif na kayan su.

Wata yar dattijowace wace bazata wuce shekara arba'in da uku ba, matar fara ce irin tas in nan domin duk wahalarda take ciki farinta bai gushe ba, sanye take cikin wata kodaddiyar green atampha wace akayi ma dinkin bou bou da shi. Kanta kule yake da dankwali amma still kani iya ganin edges inta Wanda yake da burbushin grey hair kwance akan goshin ta. Zaune take akan gadon da ya sha rufi da dan shara sharan yadin da, daga gani an yankoshi ne a wajan sai da gwanjo.

Yar ta kuma zaune take a kasa, ita kuma da ga gani ba zata wuce shekaru goma sha takwas ba, ita ba fara bace amma kuma baza a kirata da baqa ba domin wankan tarwadace. MashaaAllah yarinyar ba dai kyau ba, yar siririyar fuska ne da ita, me dauke da manyan dara daran idanu, sai kuma siririn hanchi mai tip ata karshe, bakinta dan madaidai ci ne, ga kuma alamun dimple a both kumatun nata domin dan motsa bakin nata da tayi ma sai da ya loma.

Yarinyar kana ganinta ka ga Uwarta kawai farin fata ne ya rabasu, amma har yanda gashin kansu ya kwanta iri daya, kawai dai ita batada furfura ne.

" Zahida don Allah ki kama kanki, kinga dai Jami'a ba kamar secondary bace, don Allah banda kawayen banza, kirike maraicin ki, banda yin abokai maza kinji " babartata tafada.

Jin jina kanta Zahidan tayi kana tace.

"In Shaa Allahu Mama bazan watsa miki kasa a ido ba, kuma mama ai kinsan kuma kawayena dai Salma da Safiya ne kuma kinsan ni ba me irin tara kawaye bace. "

" ai nasani amma de ki kulla kinji Zahida, Allah yayi miki albarka ".

"Naji,  amin mama ".

"  toh yanzu tashi ki canza kaya mu kwanta kinga Kina da lecture gobe".

Tashi tayi ta je wajan sif in su bude wa tayi ta dauki wata Riga da wando masu zanen flowers a jiki, ta je wani dan lungu a cikin dakin nasu ta saka kayan, daman ta riga da ta yi wanka.

****
Taku yake da qasaita da taqama, da ka ganshi ma kaga dan hutu, sanye yake cikin bakin slacks, ya hada dawani blue button up shirt Wanda yayi tuck in a cikin wando, folding hannun rigar yayi har ta zo wajan gwiwar hannun shi, Wanda ya fito da damatse hannun shi.  Rigar ma kanta ta rike jikinshi a duk inda ya kamata, da ka ganshi ma ka ga ma'abocin zuwa gym, yana da tsaho, irin tsahon nan da in an ga mutum za a kirashi da mai tsaho. Dogowar fuska ce da shi, mai dauke da madaidaicin idanu, sai kuma dogon hanci da yayi dai dai da dan karamin bakinshi, girar shi irin curved in nan ce gata baka wuluk da kuma cika. Fuskar shi a tamke yake ba alama annuri ko dariya ma a cikinta.

Kuma daga ganinshi hakan yake, shi ba ma abocin dariya bane ko da kuwa awajan abokanan shi ne, shiyasa ma sukayi mishi lakabi da Alfa Power, amma yawanci da Alfa ake kiran shi.

Motarshi ya shiga wace take kirar audi R8 kalar baka wace tayi completing rashin annurin da ke ratsewa ta jikinshi. Farin hannunshi Wanda yake fat kamar ka taba jini ya fito sabida tsaba haskenshi, ya dora a jikin mabudin kofar ya bude motar,tareda shiga ciki. Kamshin turarenshi na Versace ne ya mamaye cikin motar, lumshe idanun shi yayi Wanda har dogaye lashes inshi suka sauka akan kasan idonshi, huro iska yayi daga bakinshi, daga gani haushi aka ba shi domin fuskar nan tashi tayi jaa. Kuna motar yayi yana mai kallon abokinshi Khalil ta rare view mirror yana sauri domin isowa inda yake, tsaki ya sake kafin yasa motar a reverse, sauran kadan ma ya bige khalil, sai da Allah yaso khalil in ya matsa, bude mishi kura Alfa yayi ya yi wuce war shi.

Tsayawa Khalil yayi yana mai kallon motar Alfa da ya ke tukawa da gudu.
" Shit " ya furta yana mai cusa hannun shi cikin tulun gashin shi. Da baya da baya ya fara tafiya kafin ya Juya ya shiga cikin club in da suka fito daga.

____________________________________________________________________________
Assalamu alaikum gani na dawo da wani sabon litafin hope you'll show some love by vote, commenting and sharing. One love

Abinda rai ke so. Where stories live. Discover now