2

89 7 2
                                    

Tsaki ya saki bayan yan sakoni ya kara sakin wani tsakin. Yau ya shigo makaranta yana taraddadin zuwa yayi abinda zai yi ya fita Lafiya, amma wata ta jawo mishi bacin rai na ba gyara ba dalili. Shi besan meyasa wasu matan basuda alqibla ba duk kauce musu da zai yi sai ya samu wata ta shiga harkar shi ko a saninta ko akasin hakan.

Wajan engineering department ya hara domin nan sukayi da Khalil Zasu hadu, rabon shi da Khalil tun jiya da ya baro shi a club 360, domin ko wasu mata ne suka bashi haushi, shi fa a rayuwarshi be son shishshigi da cusa kai, suka sashin yin abinda be taba yi ba shine baro abokinshi a wajan da suke shakatawa. Duk fadan da zasuyi zaka gan su tare ko da kuwa ba sa ma juna magana.

Abokantarsu ya samo asali ne tun suna yara domin mahaifin Khalil, Alhaji Umar saleh mailafia babban abokin Alhaji Abdullah ne. Sun taso tun suna yara, domin duk a shekara daya aka haife su, sai dai shi Khalil ya girmi Uthman da watani. Tun nursery school in su tare suke zuwa kamar wasu yan uwa, don har dakosu ma tare akeyi domin ma makotan junane, har suka girma kuma komai tare sukeyi kawai dai abinda suka sha bambam shine, Uthman miskili ne gashi da saurin fishi, shikuma Khalil ruwan sanyi ne domin ba dai hakuri ba.

Baiyi wani tafiya me nisa ba tunda a mota yake, ya isa department in nasu. A ta wani shade ya hango Khalil zaune tareda wasu guys da yake yakinin mates in su ne, domin shi fa bawai yana wani hulda da yan ajin su bane, shi kawai dai in ya zo makaranta yayi abinda zeyi sai ya tafi sabida kamar dai yanda na fada a baya be son shishigi.

Kashe motarshi yayi yafito tareda kulle ta, mutanen da suke gurun duk suka zubo mishi idanu suna kallon shi, in da sabo toh ya saba da wannan kallon da mutane suke binshi da, a duk inda yaje sai ka ga an bishi da kallo, his presence alone commands respect, yana da charisma da yake sa mutane son shi farad daya, be da mutunci amma ba shi zai hana mutane son hulda dashi ba. Takun nan nashi me jan hankalin mata da kuma kara mishi kwarjini a idon mutane shi yake yi yana me dosar inda abokin nashi yake.

Fuskar nan ya sha mur daman ya kulle idonshi da black ray ban domin shi kwata kwata be son rana ya taba mishi idon. Isar shi wurin Khalil yasa maza biyun da suke tare da Khalil suka tashi suka bar wurin dan ma kar ya disgasu, don yanzu nan in suka ce zasuyi mishi magana ya iya musu rashin mutunci. Domin ba za su manta wata rana ba, wata yar under graduate ta cire kunya da ajinta ta ajiye su a gefe, ta tunkare shi amma sakamakon da ta samu shine mari daga wajan shi.

Toh su sun ma taba jin ance ya sa body guards in shi, domin jefi jefi yana yawo da bodyguards, ya sa su yi ma wani dukan tsiya, amma de ba Susan dalilin nashi na yin dukan ba. Duk da ba kullum yake yawo da body guards nashi ba amma shi kanshi tilo, tsoranshi suke ji.

Musabaha sukayi da Khalil kafin su dan gaigaisa Sama Sama suna mai takawa zuwa theatre da za su sami lecture. Yanzu sauran musu wata uku su gama karantun su ma, domin dama ba tare da undergraduates ake hada calendar su ba.

Suna shiga cikin theatre suka sami waje ata gaba gaba suka zauna. Ko wa yazo wucewa sai ya kalle su amma bawanda Uthman yake daga kai ya kalla ma balle ya sa ran zai ce masa sannu. Gwanda gwanda Khalil yana dan bawa mazan hannu suyi musabaha da su. Shi dai Uthman da harara ta kasan ido yake bin Khalil da shi yana me jin haushin yake hakoran shi da yake a gaban mutane, sai kuma in sun mishi wani abun raini yace sun raina shi, bayan shi ya jawo.

Dan siririn tsaki ya ja yana me jiran zuwan lecturer domin shi ya fara jin gajiyan zaman da yake a cikin ajin domin duk an cika kunen shi da surutu, abunda kuma ba wai yana so ba ne.

Ba su wani kara mintuna ba lecturer ya shigo, don haka sai duk suka mai da hankalinsu kan abinda yake kowa musu, duk ajin akayi tsit kamar ba dalibai ne a ciki ba.

****
Tafiya suke da dan sassarfa suna neman cafe in da babu mutane domin su samu ayi musu photo copy na wani handout da aka basu kuma lecturer handout in yace ba'a shiga mishi lecture ba handout. Toh yanzu gashi sauran musu yan mintuna kafin su shiga amma haka suke zagaye wajen duk inda suka ga cafe za suga mutane cike a wajan ba matsaka tsinke.

Abinda rai ke so. Where stories live. Discover now