❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
💕ALAƘAR YARINTA💞
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
NA
MMN AFRAH
FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
Page 1️⃣&2️⃣
JIGAWA STATE HAƊEJIA L.G
*UNGUWAR K/AREWA*
Sanye ya ke da kayan makarantar islamiya riga da wando ash colour sai hula dark blue, riƙe ya ke da jakar leda mai ɗauke da littattafai yaro ne ɗan kimanin shekara shida, tsaye ya ke a jikin bangon wani gida na ƙasa sai share hawaye ya ke wani na bin wani, ganin ƴan islamiyarsu sun zo za su wuce hakan yasa ya juya bayansa dan baya so su ga hawayensa su rainashi.
"Kai kun ga Hizbullah prefect" Yaro ɗaya ya faɗa daga cikinsu.
"Lah wallahi shine dama nan wajen ne gidansu" Yarinya ɗaya ta ce tana washe baki.
"Aikwa ya juya bayansa kar mu masa magana dan dama shima baya yiwa mutane magana sai ya ga dama"Ɗayan yace suna ta bin Hizbullah da kallo dan ya basu baya kuma bai waiwayo ba dan duk maganganun da suke yana jinsu.Suna wucewa ya cigaba da hawayensa.
"Hizbullah dama baka tafi makarantar ba Ikon Allah yanzu akan na ce Ridallah bacci take shine ka ƙi tafiya kake kuka?" Baba Habiba da fitowarta kenan daga gida ta ce tana riƙe haɓa.
"Ai bazan tafi ba indai bata tashi na ganta ba sai dai na fasa zuwa makarantar" Yace yana share hawayensa.
"Kai jama'a na ga ikon Allah wannan wace irin shaƙuwa ce tsakaninka da Ridallah, ace saboda tana bacci ba za ka tafi makaranta ba sai ta tashi, na ga ɗazun nan ka tafi gida ka yi shirin islamiyar shine bacci ya ɗauketa amma shine kake kuka kamar dai kwana kayi baka ganta ba"
Shiru ya yi bai ce komai ba sai sheshsheka da yake ta faman yi.
"Mu je ka ganta tana baccin sai ka tafi in yaso kafin a tasoku ta tashi daga baccin" Baba Habiba ta ce tana kama hannunsa domin su koma cikin gidan.
"Au bai tafi makarantar ba?Ai dama nasan hali shi yasa na leƙo in tabbatar" Muryar Umma Sadiya ta katse musu tafiyar tasu.
"Wallahi kwa ni zatona ma ya tafi shi yasa ban biyo bayansa ba dan da na ce masa bacci take to kawai yace ya juya ya fito daga gidan"
"Hmmm ai Hizbullah da Ridallah sai Allah ki barshi ya ganta tana baccin ko ya samu ƙwarin gwiwar tafiya makarantar dan in ba haka ba ko an matsa masa ya tafi in yaje ma ba sakin jiki zai yi ba bare ya yi karatun kirki" Ummar Hizbullah ɗin tace ta juya domin komawa cikin gidan.
"Bari na yi sauri kar ya makara"Baba Habiba tace tana jansa suka yi cikin gidan, dan shi ko uffan bai ce musu ba kansa kawai ya sunkuyar yana jin duk abin da suke cewa.
Suna shiga cikin gidan ta kai shi har ɗaki, Ridallah yarinya ƴar kimanin shekara ɗaya tana baccinta hankali kwance.Baba na kai shi ɗakin ta tsaya a bakin ƙofa jakar hannunsa ya ajiye ya ƙarasa har kan katifar da aka kwantar da ita ya tsugunna a gabanta ya saki murmushi kallonta yake kamar yau ya fara ganinta sai kuma ya sanya hannu a aljihunsa na gaban riga ya fito da naira goma kuɗin makarantarsa yace.
"Wannan kuɗin shi zan siyo miki alewa da carbin malam in kawo miki in aka taso mu" Yana gama faɗar haka ya tashi yana mata bye-bye ya ɗauki jakarsa ya fito ko ta kan Baba bai bi ba ya fice daga gidan dan ya kusa makara kuma da ɗan nisa dan dai kwalta kawai zai miƙe har makarantar ba tare da ya yi kwana ba.
"Oh wannan yaro yana ƙaunar yarinyar nan ace kullum in zai je makarantar arabi ko boko sai ya shigo haka in ya taso ma, Allah raya ta, ta ga irin tarin ƙyautatawar da yake mata"Cewar Baba tana girgiza kai ta juya domin ta fita domin samun yaron da za ta aika siyan klin domin yin wanke-wanke.
Yana isa makarantar ya nufi ofis ɗin malamai ya kirawo malamin Qur'an domin shine monita kuma duk ya haddace time table ɗin ajin nasu. A kujerar gaba yake su biyu da abokinsa Bilal yana shiga ya miƙawa Bilal hannu suka yi musabiha daga haka ya zauna bai kuma cewa komai ba ya fito da Qur'aninsa, tsit ƴan ajin suka yi saɓanin kafin zuwan Hizbullah ɗin da suke ta surutu dan shi da ido kawai yake kallonsu su yi tsit kamar babu kowa a ajin dan ko sunan ƴan surutu baya rubutawa yana musu kwarjini sosai dan ba shiga harkar kowa yake ba sai dai ya yi abin da ya kawo shi gashi da mugun ƙoƙari hakan yasa ya zama mai farin jini a wurin malamai.
Malamin ne ya shigo ajin ya maimaita musu ɗorin da ya musu jiya sau uku sannan ya fara karɓar hadda daga kan Hizbullah domin shine a kujerar gaba kuma shine a farko.Tun da ya fara karatun kowa saurarensa yake yi ya iya ƙira'a gashi ko kakarewa ba ya yi har ya kai ƙarshen ayoyin da aka ɗora musu.Kabbara aka masa sannan malamin ya cigaba da karɓar hardar sauran duk cikinsu babu wanda ya bada harda irin ta Hizbullah.
Ana fitowa break ya siyi alewa da carbin malam ya sanya a aljihu ko ɗanɗanawa bai yi ba, ana tashinsu ya kamo hanya ko gidansu bai kalla ba ya shige gidansu Ridallah dan dama maƙota ne katangarsu ɗaya.Da sallama ya shiga, Baba Habiba ta amsa masa Ridallah da ke tafiya tana ta dariya ganin ta ƙware a koyon tafiya, Hizbullah kawai wurinta ya nufa yana ta murmushi itama tana hangoshi ta nufoshi tana masa dariya dan ta matuƙar saninshi dan tun da ta buɗi ido take ganinshi.
"Oyoyo ƙanwata" Yace lokacin da ya jinginar da jakarsa jikin bango ya ɗauketa sai murna take tana zillo, da yake yana da jiki dan in ka ganshi sai ka yi zaton ya yi shekaru goma ma saboda girman jikinsa.
"Ga alewarki da carbin malam"Ya bata alewar a hannunta ta riƙe tana wasanta sai ya ɓare carbin malam ɗin ya sanya mata a baki.
"Yanzu Hizbullah ace kullum ba zaka kashe kuɗin makarantarka ba in an baka sai dai ka siyo mata wani abun? Kake siyo abu marar zaƙi saboda kar rana ta kama ƙanwartaka" Cewar Baba tana kallonsu cike da sha,awa.
"Ai ba zan iya cin abu ba ban kawo mata ba, amma zan ke siyo mata biskit dan kar rana ta kamata" Hizbullah ya ce yana zaunawa akan tabarma ya ɗora Ridallah a cinyarsa yana mata wasa Baba tana tuƙa tuwo.Sai da aka fara kiran sallar magriba sannan ya yi alwala ya ɗauki jakarsa ya yiwa Ridallah bye-bye ya tafi gida ya ajiye jakar ya wuce masallaci.Ridallah kwa daƙer Baba ta lallasheta ta yi shiru dan yana ficewa daga gidan ta fara kuka.
Da daddare bayan an yi sallar isha'i ya ɗauki abincinsa ya tafi gidan Baba domin acan yake cin abincinsa tare da Ridallah, Baba ta yi ta cewa ya daina tahowa da abinci amma sai yace shi ya fi so ya kawowa Ridallah na gidansu sai shi kuma ya ci na gidan Babar.Sai wajen ƙarfe takwas da rabi idan Ridallah ta yi bacci sai shima ya tafi gida ya kwanta dan ko homework aka bashi a makaranta to a gidan su Ridallah yake yin kayansa.
Washe gari da safe wajen ƙarfe bakwai da rabi ya shigo gidan Baba da sallama dama saboda zuwansa Baba take cire sakata ta bar ƙofar a kare dan ta san ba zai iya tafiya makaranta ba sai ya biyo ta gidan.Sanye yake da kayan makarantar boko jakar makarantarsa goye a bayansa, hannunsa da flask ɗin makarantarsa mai ɗauke da abincinsa sai leda a hannunsa mai ɗauke da biredi da ƙosai sai shayi a kofi ya kawowa Ridallah bayan ya gaishe da Baba ya yiwa Ridallah wasa ya ajiye mata abincin da ya kawo mata dan ita ma shegen wayo ne da ita dan dai siririya ce bata da jiki gashi dai akwai cin abinci dan babu abin da bata ci Baba da wuri ta koya mata cin abinci. Fita ya yi yana sauri dan ya kusa makara dan dai makarantar bayan layinsu ne.MMN AFRAH
YOU ARE READING
ALAƘAR YARINTA
ActionLabari ne a kan wata mata da kishiyarta ta haukatar da ita da tsohon cikin ta tafi ta haife cikin a halin hauka