DANƊANO

24 0 0
                                    

Ɗamɗano

farawa da Bismillah ✍🏻

_begining_

*SATURDAY*
_6Th February 2022_

_*Afternoon*_

*6:00pm*

*MARABAN JOS KADUNA*

Ruwa ne sosai ake tsugawa mai ƙarfi kaman zai fasa Sama, hakan Ya sa jama'a sukayi Karanci, a lokacinda kowane abu mai rai yake mafakansa don Gujewa wannan Ruwan dake sauka da iya ƙarfinsa.

Cikin Hukunci na rabbi Wanda yasa aka fara Ruwan batareda shawaran mu ba ko dabara ba ya Tsaida abinshi chak, a daidai lokacin Dukkan Abu mai rai dake ɓoye a mafakansa suka fara fitowa kowa na ƙoƙarin kama gabansa domin Kuwa a lokacin gab ake da a Kira Magrib.

A daidai wannan lokacin Motar Journal Jameel ya yanko cikin Madaidaicin dajin Dake cikin Unguwar goro dake cikin Garin Mararraban Jos , Faffada ne kuma yalwataccen daji ne iya ganinka,wanda ya wadatu da korayen tsirrai da kuma shukoki nau'ka daban daban,masu tsaho da kuma gajeru,ciyawa tafasa, Furanni da sauran tsirrai da ubangiji ya ƙayata dajin Dashi musu su wanzu a wajen,wanda wasu ma dan adam bai san meye ba, Gefe guda kuma Akwai Dogayen Bishiyun da Sukayi wa dajin Ƙawanya, ta bayan Dajin Kuma Rumfuna ne dadama wadanda aka haɗa da Busasshun karan Hatsi wasu kuma da taɓo

Sararin ya yalwatu da Korayen shukoki shar ruwa sai ɗiga yake Ako wane Tsiro na Shukan, gurin waje ne mai cike da ni'ima da kuma albarka,albarkan damuna data sanya mawuyacine ka samu wajen a bushe ko kuma a ƙafe,wannan dalilin na yawaltar Ruwa da Shuka ya kawo wanzuwar fulani a wajen,suka kafa bukkokinsu suka kuma tashi gagarumar ruga a wajen Saboda waje ne daya dace da muradinsu da kuma buƙatuwar dabbobinsu.

Yammaci ne lis,wanda daqiqu kadanne ne zasu ratsa Magrib ta shiga,lokacine da kowanne makiyayi ya riga ya kada dabbobinsa zuwa gida inda suka turkesu ,amma Dukda Haka akwai yan tsirarun Shanye dake Galabito a harabar wajen, badan Babu mai su ba, Sai don hankalin mai su yafi Kwanciya ne a lokacin da Shanayansa suka Samu makwanci a wajen Gidansa.

Journal Jameel Tuƙi yake a natse bisa Shimfidaddun ciyayin wurin da suka dan kwanta wanda Babu Alamar Taɓo a jikinsu dukda cewa lokacin Damuna ne kuma ba'a jima da Gama tsiga ruwan sama Ba, Amma sam Babu taɓo ko jar ƙasa a Hanyar kasancewar Ciyayi ne malale a wurin saidai daga Chan nesa dasu Taɓone malale a wurin abin har babu kyan gani

Tuƙi yake cikin Natsuwa, fuskarsa babu Alamar Gajiya ko kuma ƙosawa da irin Taka ciyayin da takeyi cikin kwantaccen Ruwan da ke tsalle yana Wanke Jikin motar akowane juyin da tayar motar keyi.

kallon Korayen shimfidaddun Ciyayin yake ta wajen Gilasbin motarsa, Yanajin Natsuwa na ratsa zuciyarsa, kasancewar shi mutun ne mai tsananin Son damina, Yanayinda ke sashi Farinciki a kowane Lokaci,Ƙamshin Korayen furanni da shukoki na Matuƙar Sakashi cikin Nishaɗi sosai take yaji farincikinsa ya shanye baƙin cikin da yake cikin wanda har ya manta Rabonda yayi makamancin Farin cikin irin wannan nan, Tun bayan da ya gano ɗanshi nada halittu biyu(Mata Maza), Shekaru Biyu kenan Da suka gabata, Tun daga Lokacin bai sake samun Kwanciyar Hankali ba, matarsa Ta maida Ɗansu jarinta, a yayinda yake jimamin Allah ya Azurta shi da Ɗa mai halitta biyu, a lokacin ita take murnan ta Samu Business frame ɗinta.

Matarsa BENITA UJAH TIMOTHY, Ƴar addinin Christian, haifaffiyar garin Lagos ce mahaifanta duka Anna ne, Mahaifinta Cikakken inyamurin Port Harcourt ne (Igbo), Yayinda mahaifiyarta ta kasance Bayarbiyar Lagos, BENITA Itace ta farko a wajen iyayenta sannan Kannenta Steve da Rainbow duk mazane kasancewae BENITA ita kadai ce mace a cikin ƴaƴansu Hakan Yasa ta taso cikin Gata da sangarta, bata taɓa neman Abu ta rasa ba, ta taso da burin zama Model iyayenta kuma suka goya mata baya, suka bata duk wani gudunmuwan da ya dace, Kuma a Halin yanzu BENITA international Model ce Wacce tayi Fice a duniya wajen Tallace tallace na manyan Kanfanoni dama Featuring a waƙoƙin manyan Music artists, hakan yasa bata cika zama a Nigeria ba.

ZANE ('KADDARAR MU)Where stories live. Discover now