003

1 0 0
                                    

*Z* *A* *A* *N* *E*

*003*

*Recap*
Daidai nan yaga ta Zaro Ƙwallon Mangoron daga bakinta, ta zuro harahenta waje tana Wani sambe Ƙwallon, zagin da yayi mata ko a jikinta

"Shegiya mummuna kawai marabanki da Mahaukaciya tantance kwaɗayi dan ke a rayuwarki iya abinda kike iya tantancewa cekann"

"Ɓace min da gani ƴar iska"

Ya faɗa yana ficewa ya bata dama Ta shige ciki da gudu tana cewa

"Ɗadin Abin ba Ni kadai iska ya haifa ba, harda kai a ciki ,wanka kuma baza'a yi ba saidai ka kashe Ni, dama ka saba duka na ba yau na fara sanin BAKADA IMANI BA"

*Cont...*

Haidar ya girgiza kansa yana ayyana abubuwa da dama cikin ransa , tun randa Bintou ta fara rarrafe basu Sake samun natsuwa a cikin Gidansu ba, yarinya sai kace jikar Aljanu?, Allah ko zaman Kwana biyu kayi da ita duk haƙurinka da ita sai ta kaika bango ta cusa mata tsanarta a cikin zuciyarka ta karfi da yaji, shiyasa gabaki ɗaya duniyan nan batada masoya, In ka cire antynta Anty Nussy dake karatu a chan ƙasar India wacce Bintou ta dau aniyyar zama kamarta ta karfi da yaji, shiyasa take yawan Sa Uniform dinda nussyn na bautan ƙasa tana yawo, Sai Kuma Abdul Mannan Wappah Wanda take gani Tamkar abokin Rayuwarta  wanda ya kasance mutum na biyu da baya son ganin Ɓacin ranta ko iyayensu ba kasafai Suke tausaya mata ba , so tari idan Tayi laifi Yayanta haifar shike Hukunta ta, ya kulleta a ɗaki Yayita Bugu Haka zata yita ihu babu mai Ƙarɓarta sai yaga tayi laushi yake Barinta a ciki ya kulle ƙofar yayi ficewarsa, basu Tausayinta ne ba badan Basu Sonta ba, sai dan Ita bintou baka Iya mata a duniyar nan babu wanda tafi tsana kuma take nuna ma tsana Samada mai nuna ya damu da ita, idan ka kasance mai nuna mata hanyar gaskiya Thofa batada babban Maƙiyi sama da kai Tafiso ayita bala'i da ita shiyasa ko a makaranta batada ƙawaye sai irinta Bugaggun Yan dambe.

Hauwa na zaune bakin Murhu tana Suyan Ƙosan Rogon da ta ƙwaɓa da Garin Rogo iyakar Garin kenan ya rage , yau ba'a yi cefane a gidan ba abbansu bai dawo daga Kasuwan da yaje siyo Kayan Miya ba ,Gashi yunwa takeji shiyasa ta dauko Ragowar garin da ta dawo dashi daga makaranta ta kwaɓa  .

Da waƙa Bintou ta shigo tana Sanɗe hannu har yanzu kwallon Mangoron na hannun ta Yawu na zalalowa yana jin hannun saboda waƙar da take rerawa ,kallo daya Hauwa tayi mata ta kauda kai tana jin wani irin ƙyamar ta a cikin zuciyarta , duk yanda zan iya siffanta maku kazantar Bintou a iya Rubutu bazaku taba fahimta ba ,domin kuwa dauɗar bai baro komai ba Tun daga fatar Jikinta, haƙoranta, Suturarta dama sauran sassan Jikinta Gabaki ɗaya , bata damu da ta tsaftace komai na Jikinta ba , tun kafin ta iso wuri warin Jikinta ke fara sanarda isowanta , tamkar Ita ɗin Annoba ce a cikin Al'umman da take Tareda su.

Ƙarasowa tayi gaban Murhu da hanzari tana washe baki, wanda hakan Yayi sanadiyyar Bayyanuwar Riɓabbun Haƙoranta da suka sauya Kala izuwa ruwan ɗoruwa, sunyi Wani irin Kauri, Kalar haƙoran ya saje dana Mangoron Da ta gama sha, ya bada wani irin kala na daban.

"Kulu Ƙosan Rogo Kike soyawa?, Zan tayaki"

Ta ƙarashe maganar Tana wurgi da Ƙwallon mangwaron , Hawwa tace

"In Kika ƙaraso Nan Ranki zai ɓace bintou"

Kafin ta ida maganar har bintou ta jawo Kujerar tsugunnu ta zauna ta Zaro guda cikin mai ta jefa a baki, aikau bai ida shigewa ba ta furzar zafin ya ratsata ta daka tsalle

"Wayyo bakina jidda kin kasheni"

Hawwa tace
"Allah shi ƙara"
Cikeda dariyar Mugunta

bintou ta sake kwarma ihu tana surfawa Hawwa zagi kai ka rantse yankata Akeyi, jidda na mata dariyar Mugunta , sannan ta maida hankali kan Suyan da takeyi ranta Fesss

ZANE ('KADDARAR MU)Where stories live. Discover now