004

0 0 0
                                    

*Z* *A* *A* *N* *E*

*004*

"Yar ki?, Hahhahha aikam kina gabda rasata ,gambari a Kulle mana kofar"

Cewar Babban cikinsu yana sake turata ciki, wanda aka kirada gambari jibgege ne ya kullo ƙofar sai lokacin Sule ya Samu damar ganin fuskarBabban cikinsu a cikin hasken da bata wadaci dakin ba.

"Mahaukaciya, Sune sukayi ma MERO abin nan"

Sule ya fada a tsorace cikin Daga Murya , har a lokacin MERO na  kwance cikin jini tana juyi, da tsananin Firgice Asma'u (Mahaukaciya) ta dubesu da fargaba ta bude baki zatayi magana suka tureta da ƙarfi tayi baya, ta faɗi ƙasa , ta tashi zumbur tana faɗin

"Bayin Allah su waye ku?, Me mukayi maku haka da kuke son kassara rayuwar mu"

Tsawa ya daka mana
"Shut up...Yi Mana shuru , Mutane irin ku bakuda wata amfani an halitto Mana ku ne dan mu more rayuwar mu daku"

Ko ba haka ba? Ya faɗa yana duban sauran Abokan nasa ,gaba ɗaya suka kece da dariya, gambari yace..

"Oga, anya wannan Ba lafiyanta lau ba kuwa?, Ji irin maganganun da suke fita daga bakinta"

"Nima naga Alama , ku Maidata ruwa kawai"

Ya fada cikin bada umurni, Nan take suka buga mata Wani gingimemen Abu a ka ta faɗi kasa take jini ya fara Zuba, Sule ya saki ƙara, babban ya daka masa tsawan da ya tilasta masa kame bakinshi yana rawar jiki hawaye kam tuni suka gama jiƙashi , tashin hankali ƙarara a fuskar sa ZUCIYARSA na harbawa da sauri da sauri.

"Zonan"
Babban cikinsu ya kirashi bayan ya samu wuri ya zauna, jikin Sule na rawa yazo ya durkusa a Gabanshi fitsari na bin Ƙafarsa, hannunsa kame da bakinshi yana ƙoƙarin hana Kukansa kufcewa.

"Kaga Fuskata ko?"

Da sauri Sule ya daga kai alamar eh

"Kayiwa yan jarida bayanin yanda fuskata take ko?"

Ya sake daga kai da sauri, Ya shafa kan Sule cikeda Mugunta.

"Kayi ƙoƙari sulaiman, saidai kayi babban kuskure"

Jikin Sule ya daɗa ɗaukan rawa, Mutumin ya cije lips Ɗinsa cikeda Mugunta yace

" amma ina so Daga yau  *ZANEN*  Fuskata ya ɓace daga Ganinka Tun Daga yanzu"

"Ya ma ɓace, Wallahi Ya bace"

Sule ya fada lokaci guda ya zare hannunsa daga riƙon da yayiwa bakinsa yawu na dalalowa, duk ilahirin Jikinshi rawa yake

"Malam sulaiman kenan, Bai ɓace ba, Kuma tabbas ka Iya kwatance , ka siffantani Exactly Babu Jiɓi ko kaɗan"

"Ina so Fuskata ta ɓace maka Gabaki Ɗaya "

Sai ya bada umurnin a shigar da Mahaukaciyar wacce take kwance a sume, suka jata kaman Kayan wanki suka rufeta cikin ban ɗakin Dake cikin ɗakin, Sule na Durƙushe a gun Jikinshi sai rawa yake.

Suka taho inda MERO ke kwance akan gado tana juyi cikin azaba suka jawota daga kan gado ta faɗo kasa, Sule ya fashe da kuka yana rokonsu kada su aikata mata komai .

“zauna anan”

Ya nuna mashi wani kan gadon da Suka sauke MERO wanda duk jini ya ɓata kaman ana controlling nashi da remote haka ya Zauna Jikinshi na karkarwa, Mutumin Ya umurceshi da ya daga ido ya kalle duk abinda zasu aikatawa MERO kuma kada ya sake ya rufe su In ba haka ba sai sun tsole idon, Hakan shine Hukuncin sa na bayyanawa yan jarida kamanninsa da yayi, duk abinda yake faɗa Sule sai gyada masa kai yake jikinsa na rawa.

ZANE ('KADDARAR MU)Where stories live. Discover now