001

16 0 0
                                    

*Daga Marubuciyar*

_Hawanjinina (Uwar Mijina)_
_Maƙaryaci (fakelife)_
_Wuƙa a Zuciya (BLEEDING HEARTS)_



*Lagos Nigeria*
1st May
9:10 na safe

Ruwane ake tsugawa mai Karfi kamar zai fasa saman kwanukan jama'a ,Gudu yakeyi da iya ƙarfin Sa , Numfashin sa har sarƙewa yakeyi , Hannunsa riƙe da Ledar Magani mai ɗauke da Tambarin Chemist din Ayman Pharmacy,gudu yake sosai a tsakiyar titin da zai kaisadashi da Kangon tsohon Ginin daya kasance tamkar Makwanci su,burinshi ya isa wurin ya Ba ƙanwarsa maganin da ya ƙwato daƙyar, yarone sosai dan Bazai wuce shekara Goma Sha Huɗu ba wahala da rashin Girman jiki yasa zaka fassara shi a jerin Masu shekaru Goma sha ɗaya ko sha biyu.

Shin Mu ɗin wane irin halittane da ake gudun Mu haka?, Kodai mu ba Mutane bane? "

Ya faɗi hakan cikin ransa Sai yayi saurin Bama kansa amsa da "munada halitta tamkar na mutane ,muna raye kaman kowa"

"Amma meyasa ake wulaƙanta mu? Saboda me? Saboda me wasu mutanen suke wulaƙanta mu?"

Ya sake tambayan kansa a karo na babu adadi Ƙwallan da suka cika masa ido suka zubo Saman dakalin Fuskar sa, a daidai lokacin kuma Ruwan da ake tsugawa ya ɗan dakata, sai yayyafin dake saukowa a hankali.

"Shin mu muka kaddarowa kanmu wannan rayuwar?, Rayuwar kwararo? Miyasa ake kyarar mu saboda Allah ya jarabe mu da irin wannan kaddarar?"

Ya fada a bayyane yana ƙara ƙarfin Gudun da yakeyi.

"Tunda Rayuwar ƙunci mukazo yi a duniyar me yasa bamu mutu ba?, Meyasa?, Meyasa Bazamu mutu mu huta ba?"

Da Iya ƙarfin Sa yayi maganar jijiyoyin jikinsa na mimmiƙewa kaman wani babba , ƙarfin Gudun sa na Dada ninkuwa akan nasa Ruwan Sama ya jiƙashi sharkaf,Gam ya rike ledar maganin hannunsa kaman Za'a Ƙwace masa dukda kasancewar ba siya yayi ba kwatowa yayi a lokacin da me Chemist yake shirin Miƙama wata mata Batareda yasan ko maganin menene ba, Burinshi Mero Tasha ta samu lafiya.

Yana isa Kangon da suke kwanciya ya faɗa da sassarfa, saidai Abinda ya gani yasashi dakatawa yaja da baya agigice Numfashin shi yayi ɗaukewar wucen Gadi,  Kafafunsa suka kama rawa gabansa na faɗuwa Tsananin tsoro da fargaba suka shige shi.

Ƙattin maza murɗaɗɗu Ƙirar karen Maguzawa ne akan ƙanwarsa suna shirin keta mata haddi su Bakwai Tumɓur Haihuwar Uwarsu , sai kokuwa Sukeyi akanta, Rashin ƙwarin Jikinta yasa basu Wahala bawajen rufe mata baki suka matseta Tamkar zasu fitarda Hanjin cikinta Ta baka.

A hankali Numfashin ta ke fita cikin azaba hawaye na cika idonta,Amma kaman babu zuciya a ƙirjinsu

"Mero"
Ya furta daker yana jin wani abu na sokar kirjinshi wanda hakan ya fargar da Mutanen ,suka taho sukayi masa Dukan Tsiya Suka wancakalar dashi gefe .

A lokacin har Mero ta Miƙe da yar ƙaramar ƙarfin Da take dashi zata gudu ,Babban cikinsu ya farga da ita, Wani irin damƙa ya kaima hannayenta biyu ya jawota da karfi tayi baya,ya buga kanta da gini, ya Riƙe hannayenta waje guda ,yasa Gwiwan ƙafarsa ya Buge ƙafarta Tayi baya Tafaɗi kanta ya bugu da wani ƙaton Dutse ta kwarma wani irin razananniyar Ƙara wanda Ya haddasa tashin Tsuntsayen dake kan bishiyan Dogon Yaro tashi Sama a tsorace Suna Fitarda Wani irin kuka mai Razananarwa.

Cikin tarin Azaba da raɗaɗi ta buɗe baki ta kwarma ihu da Ƙoƙarin kwace kanta ƙarƙarfan Riƙon da yayi mata, yasa tafin hannunsa Ya toshe bakinta bai ko damu da Dauɗa da warin dake busowa daga Jikinta ba, ya Fara ƙoƙarin aikata Burin shi akanta.

Ta Rintse idanunta Hawaye Suka silalo mata Cikin Yanayi na rashin Imani Ya Haye Kanta batareda Yayi la'akari da kankantar Shekarunta ba ,dan bazata wuce shekara goma sha biyu ba, ya barge rigar dake jikinta suka fizge Suturarta suka jefar da shi can gefe.

ZANE ('KADDARAR MU)Where stories live. Discover now